Tennis: Felix Auger-Aliassime ya lashe kofin Rotterdam Open

Asalin hoton, Getty Images
Dan kasar Canada Felix Auger-Aliassime ya lashe gasar Tennis ta Rotterdam Open, bayan da ya doke abokin karawarsa dan kasar Girka Stefanos Tsitsipas.
Felix ya doke Tsitsipas a wasan na karshe 6-4, da kuma 6-2 a cikin minti 78.
Dan Canadar shine na tara a jerin mafiya kwarewa a wasan Tennis a duniya, kuma kafin ya kai zagayen karshen ya doke sanannun fuskoki kamar Andy Murray da Cameroun Norrie dukansu 'yan kasar Burtaniya.
'' Ban taba farin ciki ba kamar na wannan rana tun da na fara wasan tennis, kuma ina fatan yanzu na sa kafar samun wasu nasarori nan gaba.'' In ji Auger-Aliassime.
Sau takwas dan wasan mai shekaru 21 na kaiwa wasan karshe amma bai taba cin ko daya ba sai a wannan karon.

Asalin hoton, Getty Images
To amma dama a bana Felix Auger-Aliassime na kan ganiyarsa, don kafin gasar ta Rotterdam Open ya taimaka wa kasarsa Canada ta lashe kofin ATP a watan Janairu, ya kuma kai zagaye na kusa da na karshe a gasar Australian Open da aka yi a birnin Melbourne.
A lokacin da ya doke shahararren dan wasan Burtaniya Andy Murray, ya ce ''irin yadda Felix ke buga wasa bai yi mamakin galabar da ya samu a kansa ba.''























