Waiwaye: Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Ukraine, Najeriya ta yi sabuwar dokar zaɓe

An wallafa

Kamar kowane ƙarshen mako, wannan karon ma mun duba labaran da suka fi jan hankali a Najeriya.

Yaƙin Ukraine: Halin da 'yan Najeriya suka shiga a Ukraine da Rasha

Bayanan bidiyo, Halin da wasu ƴan Najeriya mazauna Ukraine suka shiga

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta kwashe duk wani ɗan ƙasarta da ke Ukraine kuma ke burin barin kasar sakamakon tashin hankalin da ake ciki a kasar.

Sanarwar gwamnatin na zuwa ne yayin da zaman zullumi ke karuwa kuma mutane na neman mafaka saboda hare-haren Rasha bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.

Ita ma Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta yi aiki tare da ma'aikatar harkokin wajen, wurin dawo da 'yan Najeriyar da ke wadannan kasashe biyu gida.

Jama'a da dama sun shiga a birnin Belgorod na kasar Rasha wanda ke kusa da kan iyakar kasar Rasha da Ukraine.

An shiga halin zullumi saboda karar harbe-harbe da rokoki da Rasha ke harbawa zuwa kasar Ukraine babu kakkautawa.

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe

Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kai.

Buhari ya saka hannu kan dokar ne ranar Juma'a a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon Shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilan kasar.

Shin sabuwar ƙungiyar siyasar da Kwankwaso ya ƙaddamar za ta iya barazana ga APC da PDP?

Da yake jawabi lokacin da yake sanya hannu kan dokar, shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara.

Shugaban ya ce wannan sabuwar dokar zaɓen, za ta ƙara inganta harkar zaɓe ta hanyar tabbatar da an yi abubuwa a bayyane ba tare da nuƙu-nuƙu ba a lokacin zaɓen da kuma rage abubuwan da za su ja ƴan takara su yi ta ƙorafe-ƙorafe.

Shugaba Buharin ya bayyana cewa wannan ƙoƙarin na sa hannu kan dokar zaɓen na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsu na ƙara buɗe hanya domin gudanar da sahihin zaɓe mai inganci.

Ya kuma ce babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa da zai iya zama wakilin masu zaɓe wato 'dalaget-dalaget' ko kuma a zaɓe shi a yayin babban taron jam'iyya domin ya tsaya takarar zaɓe.

Rabiu Musa Kwankwaso ya kafa sabuwar ƙungiyar siyasa

Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.

Fitattun mutane da ƴan siyasa ne suka halarci taron ranar Talata. Daga cikinsu akwai Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

An gudanar da taron ne a International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwa a ƙasar suka haɗa kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.

Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.

Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbataer da ingancinsu ba na cewa akwai yiwuwar Kwankwaso - wanda ya nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyu - da abokan siyasar tasa su kafa sabuwar jam'iyyar siyasa kafin babban zaɓe na 2023.

NDLEA ta ƙona hekta 250 na gonar wiwi a Jihar Ondo

Ondo

Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta ce ta ƙona hekta 255 na gonar tabar wiwi tare da kama mutum 13 a Jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.

Masu sharhi na cewa zuƙar tabar wiwi ya ƙaru a Najeriya a 'yan shekarun nan duk da nasarorin da hukumar ke samu a yaƙi da ita.

NDLEA ta ce ta gudanar da aikin ne a dazuka biyar manya cikin kwana bakwai bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari cewa a lalubo duk inda irin waɗan nan gonaki suke kuma a lalata su.

Hukumar ta wallafa hotuna da bidiyo na jami'anta yayin da suke aikin ƙona gonakin.

An rantsar da Sanata Hassan Nasiha mataimakin gwamnan Zamfara

Sanata Hassan Muhammad Gusau

An rantsar da Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara.

Alƙaliyar Alƙalai ta Zamfara Kulu Aliyu ce ta rantsar da sanatan ranar Laraba bayan 'yan majalisar dokokin jihar sun tsige Mahdi Aliyu Gusau daga muƙamin.

A ranar Larabar ce Kakakin Majalisar Dokoki Nasiru Muazu Magarya ya karanta wasiƙar da Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya aike musu ta neman tantancewa da naɗa Sanata Nasiha a matsayin mataimakinsa.

Lokacin da ya bayyana a gaban majalisar, 'yan majalisar sun nemi ya Sanata Nasiha ya ranƙwafa kuma ya wuce.

Kotu ta yanke wa gawurtaccen ɗan fashi Evans hukuncin ɗaurin rai-da-rai

Evans

Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta yanke wa riƙaƙƙen wanda ake zargi da garkuwa da mutane Chukwudimeme Onwuamadike - wanda aka fi sani da Evans - hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an yanke wa Evans tare da muƙarrabansa Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifi kan wasu zarge-zarge biyu waɗanda suka haɗa da haɗa baki domin aikata laifi da kuma garkuwa da mutane a ranar Juma'a.

Alƙali Hakeem Oshodi wanda ya yanke hukuncin, ya kama mutum ukun da laifin garkuwa da babban daraktan kamfanin haɗa magunguna na Maydon Pharmaceuticals Limited wato Donatus Dunu.

Ya bayyana cewa akwai cikakkun hujjoji da suka tabbatar da suna da laifi.