Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Lewandowski, Coutinho, Phillips, Dybala

.
An wallafa

Tauraron dan wasan gaba na Manchester United da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya tattauna da wakilinsa, Jorge Mendes kan makomarsa a Old Trafford. (Sun)

Sannan kuma tauraron dan wasan gaba na Bayern Munich, dan kasar Poland, Robert Lewandowski mai shekara 33 na daukar hankalin Manchester United. (Bild - in German)

Kocin Aston Villa Steven Gerrard na son kugiyar ta yi amfani da damarta ta sayi Philippe Coutinho a kan yuro miliyan 40 (fam 33.5m). To amma kuma dole sai dan wasan na Brazil mai shekara 29, wanda ya taka rawar-gani a zaman aro da ya yi daga Barcelona, ya rage albashinsa na fam 480,000 a mako. (Telegraph - subscription required)

Haka kuma Villa za ta iya neman dan wasan tsakiya dan Ingila Kalvin Phillips idan Leeds ta fadi daga gasar Premier.

Kungiyar ta tattauna a kan dan wasan mai shekara 26 kuma masu yi wa kungiyar zawarcin 'yan wasa sun nuna sha'awarsu a kansa. (Athletic - subscription required)

Juventus na shawarar kan ko ta kara wa dan wasanta na gaba dan Argentina Paulo Dybala, kwantiragi ko kuma ta nemi dawo da Paul Pogba, wanda ta sayar wa Manchester United a 2016. (Tuttosport - in Italian)

Paulo Dybala

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya bukaci dan bayansa na Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, da ya yi watsi da maganar Barcelona, ya zauna a Stamford Bridge. (Mirror)

Luke Shaw, na sha'awar kulla sabuwar yarjejeniya ta ci gaba da zama a Manchester United. (90min)

Arsenal ta tsara sayen 'yan gaba biyu da dan tsakiya daya a bazaran nan a wani garambawul da take shirin yi. Haka kuma watakila Gunners din su nemi sayen dan wasan gaba na gefe, da kuma 'yan wasan baya na gefe, hagu da dama. (Standard)

Ita kuma kungiyar Sevilla ta kara farashin kudin na-gani-ina-so na Diego Carlos zuwa yuro miliyan 80 (fam 67m). Newcastle ta yi kokarin sayen dan wasan na Brazil mai shekara 28 a watan Janairu amma kungiyar ta Sifaniya ba ta shirya sayar da shi ba. (Goal)

Atletico Madrid na kan gaba wajen zawarcin dan wasan tsakiya na Marseille da Faransa Boubacar Kamara. Rahotanni sun ce Manchester United da Newcastle ma na son dan wasan mai shekara 22 amma Atletico ita ce dan wasan ya fi son tafiya, idan kwantiraginsa ya kare a bazara. (Footmercato - in French)

Boubacar Kamara

Watakila dan wasan Sifaniya Bryan Gil, mai shekara 21, ya ci gaba da zama a Valencia a kaka mai zuwa, bayan da ya je kungiyar ta Sifaniya a matsayin aro daga Tottenham a watan Janairu. (Star)

Dan wasan tsakiya dan Holland, Ryan Gravenberch, mai sheakara 19, yana da damar tafiya Barcelona daga Ajax a bazaran nan. (Fabrizio Romano)