Waiwaye: Za a kashe tiriliyan huɗu a biyan tallafin mai, an cire dokar hana taron biki a Najeriya
Daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata, an cire dokar hana taruwar jama'a da fitar dare a Najeriya; 'Yan bindigar Kaduna sun yi jawabi; Kotu ta daure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan yin saɓo.
Mun duba muku muhimmai daga abubuwan da suka faru.
Kotu ta yi watsi da tuhuma takwas da gwamnatin Najeriya ke wa Nnamdi Kanu

Asalin hoton, Channels TV
Mai shari'a a Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta soke tuhuma takwas daga cikin 15 da gwamnatin Najeriya ke tuhumar madugun 'yan aware na haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Tuhume-tuhumen takwas na cikin laifukan da aka kara kan wadanda da ake yi wa shugaban 'yan awaren.
Yayin da take watsi da tuhumar, Mai Shari'a Binta Nyako ta ce zarge-zargen ba su bayyana laifin da wanda ake karar ya aikata ba.
Mai shari'ar ta ce sato shugaban IPOB din da aka yi da manufar gudanar da bincike abu ne halastacce.
Ta kuma ce da ma akwai umarnin kamu a kan Kanu bayan tserewa daga kasar a gaban kotu.
Sai dai lauyoyin da ke kare shi sun dage kan cewa gwamnatin Najeriya ta karya dokar ƙasa da ƙasa tare da take hakkin Kanu, da sato shi daga wata ƙasar a bara.
Duk da cewa har yanzu hukumomi ba su bayyana inda da kuma yadda aka kama Mista Kanu kuma aka ta so ƙeyarsa ba, dangi da kuma lauyoyinsa na cewa an kama shi ne a ƙasar Kenya cikin wani yanayi mai sarƙaƙiya.
Gwamnatin Kenya dai ta musanta wannan zargi. An ki ba da belin shugaban kungiyar ta IPOB a zaman kotun.
An cire dokar hana taruwar jama'a da fitar dare a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama'a a tarukan bikin aure da na waƙe-waƙe waɗanda aka saka da zimmar yaƙi da annobar korona.
Kwamatin yaƙi da cutar na shugaban ƙasa ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a ƙasar.
Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan ɓullar annobar cikin ƙasar a watan Fabarairun 2020.
Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar haɗarin yaɗa sabon nau'in cutar.
Sai dai kuma, ya jaddada cewa wajibi ne mutane su ci gaba da saka takunkumi idan suna cikin wani rufaffen wuri amma bai zama lallai su saka ba idan suna buɗaɗɗen wuri ko kuma fili.
An janye ƙayyadewar adadin mutanen da za su halarci wani taron addini amma kwamatin ya ce lallai ne a saka takunkumi a wurin.
Buhari ya nemi majalisa ta amince da naira tiriliyan huɗu a matsayin kuɗin tallafin mai

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi majalisar tarayyar ƙasar ta ƙara yawan kuɗin tallafin man fetur na kasafin kuɗin 2022 daga biliyan 442 zuwa tiriliyan huɗu.
Buhari ya buƙaci hakan ne cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa 'yan majalisar, inda yake neman su yi wa dokar kasafin kuɗin gyara.
Cikin wasiƙar wadda Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajamila ya karanta a zaman majalisa na ranar Alhamis, Buhari ya ambaci hauhawar farashin ɗanyen man fetur sakamakon yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.
"Kamar yadda kuka sani, an samu sauyi a tattalin arziƙin duniya da kuma na cikin gida wanda ya tilasta neman gyara kan Tafarkin Harkokin Kuɗi na 2022 wanda aka gina kasafin kuɗi na 2022 a kansa," a cewar Buhari.
A cewarsa, sauyin da za a samu a tafarkin ya haɗa da ƙari a kan hasashen farashin ɗanyen mai daga dala 62 zuwa 73 a kan kowace ganga da aka saka a kasafin kuɗin na 2022.
An saki Alwan Hassan shugaban Bankin Noma da ƴan bindiga suka sace a harin jirgin ƙasa

Asalin hoton, @FmardNg
Ƴan bindiga da suka kai harin bom a jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun saki shugaban bankin noma Alwan Ali Hassan ɗaya daga cikin fasinjojin da suka yi awon gaba da su a cikin jirgin.
An sake shi ne a ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC.
A ranar Litinin 28 ga watan Maris ƴan bindiga suka kai harin bom a jirgin ƙasa da ke kanyar zuwa Kaduna daga Abuja.
Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ce jirgin na ɗauke da fasinja 362, kuma har yanzu ba a san makomar sama da 160 bayan tabbatar da mutum 182 da suka tsira.
'Yan bindigar sun yi jawabi
A karon farko, 'yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan fasinja da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.
A ranar Laraba ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin ɗin makon jiya.
Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huɗu cikin 'yan bindigar sanye da kakin sojoji, rufe da fuskoki a tsaye suna iƙirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin ƙasa da suka sace a ƙarshen watan jiya.
Ba a dai ga fasinjojin a cikin taƙaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riƙe da su.
Sun kuma ce ba za su sake su ba har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu, amma ba su bayyana buƙatun nasu ba.
Kotu ta daure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan aikata saɓo

Asalin hoton, Facebook/Mubarak Bala
Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa Mubarak Bala hukuncin shekara 24 a gidan yari kan laifin ɓatanci ga addinin Islama.
An yanke masa hukunci ne kan laifuka 18 da aka zarge shi ciki har da amsa laifin aikata saɓo da ya yi a gaban kotu.
Sai dai ya shaida wa kotun cewa lokacin da ya yi rubutu bai san cewar saƙon zai iya haifar da tashin hankali ba, sannan kuma hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.
An kama Mubarak Bala, shugaban kungiyar waɗanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna.
Sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.
Sakon da ya wallafa ya fusata al'ummar Musulmai a Najeriya.
Ɗan majalisar Najeriya na son a fara ɗaure 'yan daudu ko tarar N500,000

Asalin hoton, @Hon_UML
Wani ƙudiri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilan Najeriya da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi a kwakwarima ya nemi a haramta daudu a ƙasar.
Da yake karanto sashe na 4 na dokar ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.
Ya nemi a saka ɗaurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin ɗan daudu.
Ɗan majalisar na so a ƙara wani ƙaramin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: "Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000."
A ranar Talata ne 'yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.



























