Zan sanya dokar ta-baci kan matsalar tsaro idan na ci zabe a Katsina - Imran Jino

Bayanan bidiyo, Bidiyon dan takarar gwamna na PRP a jihar Katsina
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallo wannan bidiyon

Dan takarar gwamna karkashin Jam'iyar PRP a Jihar Katsina Imran Jino ya bayyana wa BBC Hausa cewa abin da zai fara yi idan ya ci zabe shi ne sanya dokar ta-baci kan matsalar tsaro da zarar ya samu nasara.

Imran ya ce ya fito takara ne don magance matsaloli da al'ummar Katsina ke fuskanta kamar rashin tsaro da karancin ilimi da kyautata muhalli da kuma tattalin arziki.

Dan takarar gwamnan na jam'iyar PRP ya ce yana da yakinin PRP za ta kayar da dukkan sauran 'yan takara na wasu jam'iyyu kafIn karfe 12 na rana.

Da aka tambaye shi ta ya ya zai inganta harkar noma, sai yace "idan na samu nasara gwamnatina za ta samar da matakai da manoma za su bi wajen samun kudi domin yin noma cikin sauki".