Ban Kwana
To jama'a a nan ni Muhammad Annur Muhammad da na karbi ragamar ci gaba da kawo muku labaran kai tsaye tun da rana, nake cewa rai dangin goro, mu kwana lafiya. Sai safiyar gobe Laraba ta-bawa ranar samu, idan Allah Ya kai mu.
Wannan shafin zai kawo muku labarai kai tsaye daga Najeriya da yammacin Afirka, da ma sauran kasashen duniya.
Bello Habeeb Galadanchi
To jama'a a nan ni Muhammad Annur Muhammad da na karbi ragamar ci gaba da kawo muku labaran kai tsaye tun da rana, nake cewa rai dangin goro, mu kwana lafiya. Sai safiyar gobe Laraba ta-bawa ranar samu, idan Allah Ya kai mu.

Asalin hoton, OTHERS
Sojojin Najeriya na bataliya ta 195 sun ce sun kama mutane bakwai masu jigilar kai wa mayakan Boko Haram da masu satar mutane kayayyaki.
Hukumomin sojin sun ce sun yi nasarar kama mutanen ne da suka hada da Hadiza Ali da Kelo Abba da Mariam Aji da Kamsilum Ali da Ngubdo Modu da Abiso Lawan da wasu, a wajen babban birnin jihar Borno, Maiduguri.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne a wasu bayanan sirri da wani masanin harkokin tsaro Zagazola Makama, ya samu tare da bayyanawa jaridar.
Rahoton ya nuna cewa an kama mutanen ne da tarin kayayyaki da suka hada da man fetur da gidan sauro da taliya a yayin wani bincike, a kan hanyarsu ta kai wa 'yan Boko Haram kayayyakin.
''Sojojin sun zargi mutanen ne bayan da suka ga garin-kwaki mai yawan gaske an boye a cikin galan-galan da kuma karkashin motar da mutanen ke ciki.'' kamar yadda rahoton ya nuna.
Ya kara da cewa, '' Bayan an tsananta bincike ne sai matan suka tabbatar wa da sojojin cewa su 'yan Boko Haram ne da ke aiki a sansanin 'yan gudun hijira da ke Garejin Muna da Mafa da Dikwa, inda mayakansu ke zaune a yankin bakin ruwa na Boboshe da Gulumba a karamar hukumar Dikwa ta jihar ta Borno.
A sanadiyyar wannan kamen ne kamar yadda bayanan suka nuna sojojin suka fadada bincike abin da ya kai su ga kashe dan Boko Haram daya da kona wata babbar mota daya suka kuma kubutar da mutum biyar da aka sace a wani sansani.

Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Saudiyya ta bayar da taimakon magani da makwanci da ya kai na dala miliyan10 domin ga 'yan gudun hijirar Ukraine sama da miliyan daya.
Shugaban hukumar bayar da agaji a duniya ta kasar Saudiyya wato King Salman Humanitarian Aid and Relief Center (KSrelief), Dr. Abdullah Al Rabeeah shi ne ya sanar da haka a Poland.
Ya jaddada kudurin kasar tasa na taimaka wa 'yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine zuwa Poland da sauran kasashe makwabta da cewa hakan na daga kudurin kasar na taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a fadin duniya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ofishin jakadancin Saudiyyar da ke babban birnin Poland din Warsaw, jiya Litinin.
Hukumar bayar da agajin ta Saudiyya tana gudanar da ayyukan jin-kai da suka zarta 2,000 a kasashe 85 a fadin duniya.
Ayyukan da suka hada da samar da abinci da kula da lafiya da bayar da ilimi da samar da ruwa da tsaftar muhalli da sauransu, in ji shugaban.

Asalin hoton, Getty Images
Kafar yada labarai ta gwamnatin Somalia ta ce sojojin Amurka sun kai hari ta sama kan mayakan al-Shabab a yankin Hiran d ke tsakiyar kasar.
Kafar ta ce gwamnatin kasar ce ta bukaci hakan daga sojojin na Amurka.
Sai dai rundunar sojojin Amurkar da ke Afirka ba ta ce komai ba game da labari zuwa lokacin bayar da rahoton.
Jami'an Amurka sun ce hare-haren sama biyu da aka kai a watan Yuni da Yuli sun hallaka mayaka masu da'awar jihadi bakwai
Al-Shabab ta tsananta kai hare-hare kan abubuwan da suka shafi gwamnati a watannin nan tare kuma t kai hare-hare cikin kasar Ethiopia.
A kwanan nan aka nada wani tsohon shugaban kungiyar Mukhtar Robow, a matsayin ministan harkokin addini.
Ana kallon nadin nasa a matsayin wata dabara ta yakar tsattsauran ra'ayin kungiyar ta al-Shabab.

Asalin hoton, OTHERS
Hukumar zabe ta Najeriya (INEC) ta ce ba ta karbi sunayen Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ahmed Lawan da tsohon Ministan Harkokin Niger Delta Godswill Akpabio a matsayin 'yan takarar majalisar dattawa ba.
Hukumar ta ce ta ki karbar sunayen mutanen biyu a matsayin dan takara na shiyyar Yobe ta Arewa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma ta Akwa Ibom sakamakon takaddamar da ke tattare da zaben fitar da gwanin da aka ce an zabe su a jam'yyar APC mai mulkin kasar.
Da take mayar da martani kan wani rahoto da aka sa a intanet wanda a ciki aka zargi hukumar da cewa ta sauya takardun sunayen 'yan takarar da aka gabatar mata wadanda suka yi nasara domin shigar da sunayen Lawan da Akpabio, INEC ta ce sam-sam ba ta karbi sunan kowanne daga cikinsu ba.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da kwamitin ilmantar da masu kada kuri'a na hukumar Festus Okoye, ya fitar, hukumar ta ce: “Domin fayyacewa takarda EC9 ( ta mika sunayen 'yan takara da jam'iyyu suka yi) ita ce takardar da jam'iyyu suka sanya a shafin hukumar zaben na karbar sunayen 'yan takarar da suka zaba. An nuna wannan karara a saman takardar wadda aka karba ranar 17 ga watan Yuni na 2022 a lokacin da aka rufe shafin.
“Abin da ya biyo baya shi ne wallafa bayanan takardun 'yan takarar da aka zaba, wanda aka yi bayan mako daya. Hukumar ba ta wallafa bayanan takardun mutanen biyu ba da ake magana.
Sanarwar ta kara da cewa : “Matakin hukumar ya janyo matakin shari'a wadda har yanzu ake yi. Saboda haka abu ne da ya saba hankali a je a mika wata takarda ta daban da aka yi sauye-sauye da ake cewa an yarda da mutanen biyu a matsayin 'yan takara yayin da maganar ke gaban shari'ar.''

Asalin hoton, Getty Images
Gobarar daji na ci gaba da addabar sassan Turai da yawa, inda ake hasashen samun yanayin tsafi mai tsanani a kwanakin da ke tafe.
Kusan 'yan kwana-kwana 90 ne ke ta fafutukar kashe gobara da ta watsu da sassan dazukanPortugal, wadda tun watan Oktoba na bara kusan rabin ruwan saman da take samu aka yi kawai.
A kudancin Faransa an kwashe mutane 3000 a wani yanki da ke kusada birnin Toulouse, inda dajin da ya kai murabba'in kilomita bakwai ya kama da wuta.
Birtaniya ta fitar da sanarwa tare da gargadin jama'a da kada su kunna wuta.
Can a gabashi kuwa, hukumomin Rasha sun ce wutar daji har 160 na ta ci a sassan dazukar kasar daban-daban.
Masana kimiyya sun ce kusan sauyin yanayi na kara ta'azzara matsalar fari da tsananin zafi.
An kama wani ɗan majalisar dokokin Kenya mai wakilar Nakaru ta gabas mai suna David Gikaria saboda kaurewa da faɗa a rumfar zaɓe.
Wani shugaban rundunar 'yan sanda a yankin Peter Mwanzo shi ne ya tabbatar da lamarin.
Gidan talabijin din NTV a Kenya ya wallafa bidiyo da ke nuna lokacin da jami'an ƴan sanda suka tafi da shi a mota.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Tamil Nadu Police
An gano wani gunki na Indiya a New York da aka sata a shekara ta 1971 daga wani wajen bautar gumaka a jihar Tamil Nadu a cewar jami'an ƴan sanda.
Gunkin da aka gina a ƙarni 12 na wata abar bauta mai suna Parvati an samo shi a gidan gwanjon Bonhams, a cewar su.
Bonhams wani gidan gwanjon kasa-da-kasa ne mallakar ƴan kasuwa da babban ofishinsa ya ke birnin London.
Wani babban jami'in ƴan sanda ya ce sashen kula da gunkuna na rundunar ya shirya takardun dawo da gunkin.
A shekarun baya, Indiya ta kara himma wajen dawo da humakant da sauran kayan tarihi da aka sace ko aka yi fataucinsu ba bisa kai'ida ba daga gidajensu.
A watan Fabrairu ne, Firayim Minista Narendra Modi ya ce an yi nasarar dawo da "humaka sama da 200" India tun shekarata 2014.
A 2020, Burtaniya ta mayar wa gwamnatin Indiya humakan tagulla guda uku da ta sace daga gidan bautar Tamil Nadu sama da shekaru 40 da suka gabata.
Shugaba Uhuru Kenyatta ya jefa ƙuri'a a mahaifarsa mai suna Kiambu da ke tsakiyar Kenya.
"Na yi imanin cewa za a yi zaɓe ingantacce, zaɓe na tafiya yadda ya kamata," ya faɗa wa ƴan jarida bayan ya ƙaɗa ta shi ƙuri'ar.
Shugaban ya yi zaben ne bayan mahaifiyarsa - Ngina Kenyatta da aka fi sani da Mama Ngina, tsohuwar matar shugaban Kenya na farko bayan mulkin mallaka Jomo Kenyatta, ta kaɗa tata ƙuri'ar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Jami'an tsaro a Najeriya sun tsare wasu mutane da ake zargi suna da hannu a harin da aka kai cocin Owo a jihar Ondo da ake kudu maso yammacin kasar.
Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan kai harin da hukumomi suka ce na ta'addanci ne.
Shugaban rundunar sojin kasar Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a yau Talata, a wata ganawa da manyan editoci da shugabannin kafafen yaɗa labaran Najeriya.
Janar Irabor ya ce sun tsare maharan ne a wani samamen hadin gwiwa da ya ƙunshi jami'an soji da hukumar leƙen asiri ta cikin gida (DSS) da ƴan sanda.
Mutane 40 ne suka rasa rayukansu a lokacin da ƴan bindigan suka kai farmaki akan cocin ranar 5 ga watan Yuni, sannan suka tayar da abun fashewa yayin da masu ibada suka nemi wajen tsira.
Irabor ya ce "tun haduwar mu na ƙarshe a baya, mun samu gagarumar nasara."

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Getty Images
Sojoji a ƙalla 17 ne da fararen hula huɗu aka kashe ranar Lahadi, sannan ba a ga wasu mutum tara ba, biyo bayan wani hari da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai.
Lamarin ya faru ne a garin Tessit da ke bakin iyakokin kasashe uku tsakanin Mali da Burkina Faso da Nijar, wajen da ake yawan samun hare-hare.
Wannan kiyasi na wadanda harin ya shafa na wucin gadi ne, kuma zai iya sauyawa, kamar yadda wata sanarwar rundunar sojin Mali a jiya Litinin ta ce..
Rundunar sojin ta kuma ce ta kashe mayaƙa bakwai da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar IS ne a yankin sahara, saboda taimakon da ta samu na amfani da jirgin mara matuƙi da kayan fashe-fashe da bama-bamai masu fasa motoci.
Sojin Malin ta kuma bayyana cewa sojoji 22 ne suka samu raunuka, sannan sun yi asarar motoci an kuma lalata shingayen tsaro.
Sannan a kalla wasu hare-hare biyu da mayakan sa kan suka kai sun yi sanadiyar rayukan fararen hula 12 ranar Asabar a tsakiyar Mali, da jami'an ƴan sanda biyar a ranar Lahadi a kudu maso yammacin kasar.
Kasar Mali na ci gaba da samun kalubalen 'yan bindiga da ke ikirarin jihadi tun 2012, lamarin da a farko ya shafi arewacin kasar ne kadai.
Amma abun ya yaɗu zuwa tsakiya da kudancin Mali, da kuma makwabciya Burkina Faso da Nijar.

Asalin hoton, Goodluck Ebele Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya na Goodluck Ebele Jonathan ya je kasar Kenya domin sa ido kan yadda zaben kasar ke gudana.
Mr Jonathan ya je ƙasar ne a karkashin inuwar wata kungiyar lura da zabe da manazartan dauwamammiyar dimokradiyya a Afirka (EISA), a matsayin dan kungiyar, domin gani-da-ido na yadda zabe ke tafiya a wasu mazaɓu a birnin Nairobi da ke Kenya.
Shugaban ya bayyana manufar ziyarar a shafinsa na Facebook da cewa "yayin da mutanen Kenya suka fito yau domin jefa kuri'a a duk faɗin ƙasar, muna sa ran za a fito da sakamakon zaɓe lafiya da kuma karfafa dimokradiyyar ƙasar Kenya.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƴan sandan Najeriya ta kori daya daga cikin ma'aikatanta saboda cin zalin wani farar hula.
Jami'in mai suna Liyomo Okai da ke aiki a babban ofishin ƴan sanda na Ekori a Jihar Rivers, an gan shi ne a wani bidiyo na ranar 31 ga watan Yuli yana dukan wani mutum da adda.
Rundunar ƴan sandan ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita a jiya da yamma.
Ta kuma ce korar jami'in ta fara aiki nan take daga ranar 8 ga watan Agusta.
Sifeto Janar na ƴan sanda IGP Usman Alkali Baba psc(+), NPM, fdc, ya bayyana matukar takaicinsa akan rahoton cin zali da ƙwace da ake tuhumar wasu ƴan sanda a ƙorafe-ƙorafen da jama'a suka gabatar a kafafe daban daban da aka gabatar, har da waɗanda ake yi a shafukan sada zumunta.
Babban sufeton ƴan sandan ya kuma bai wa duka kwamishinonin hukumar umarnin tabbatar da sa ido sosai da kula da ayyukan jami'anta kan faruwar irin waɗannan abubuwa.

Asalin hoton, BBC's Robert Kiptoo
A babban birnin na Kenya Rift Valley, yanayin wurin ya nuna babu wani jami'in hukumar zabe da ya je yankin Uasin Gushi.
Da yawan shaguna sun kasance a kulle da saboda hutun da aka bai wa mutane don su jefa kuri'arsu.

Asalin hoton, BBC's Robert Kiptoo
A wajen jefa kuri'a, masu kada kuri'a sun matsa wa ma'aikatan 'yan hukumar zaben da su yi sauri domin sauran mutanen da ke tsaye kan layi tun karfe 04:00 na safe su samu damar jefa kuri'arsu.
Daya daga ciki 'yan gaba-gaba a takarar shugaban kasar wato William Ruto ya je daga gundumar Uasin Gishu.
A garinsu Sugoi, 'yan acaba sun bar aikinsu na ranar suna daukar marasa lafiya da tsofaffi da ba su da karfin kai kan su waje jefa kuri'a ba kyauta domin kada kuri'arsu.

Asalin hoton, Alamy
Jami'an tsaro masu zaman kansu a jihar Ondo wadanda aka fi sani da Amotekun sun tsare wasu mutane 168 da ake zargi da kutse a cikin manyan motoci biyu.
Wannan ya zo ne bayan kwanaki uku da kama wasu mutum 151 da su ma ake zargi da kutse cikin jihar, dauke da layu a buhunhunan shinkafa a yankin Sango da ke babban titin Akure-Ado.
Kwamandan jami'an Akogun Adetunji Adeleye ya ce an tare waɗanda ake zargin ne a kusa da al'ummomin Itaogbolu da Iju da ke karamar hukumar Akure ta arewa yayin da ake binciken motoci.
Kamar yadda kwamandan ya bayyana, mutanen da aka kama sun zo ne daga jihohin Kano da Jigawa ba tare da tabbacin me ya kai su jihar Ondo ba.

An girke 'yan sandan kwantar da tarzoma a mazabar Rongai ta yankin Nakuru a arewa maso yammacin babban birnin Kenya Nairobi.
Wannan ya biyo zanga-zanga a wajen jefa kuri'ar zabe ta Mercy Ngeri, saboda an dakatar da zaben dan majalisar yankin a dalilin samun matsala da takardun zabe, kamar yadda wakilin BBC David Wafula ya ce.
Amma ba a soke sauran kuri'un ba, duk da haka mutane na zuwa jefa kuri'a, a cewar Wafula.

Kafofin yaɗa labaran yankin gabashin Afirka sun gabatar da rahotanni na musamman akan zaɓen kasar Kenya, suna jaddada muhimmancin magajin Uhuru Kenyatta a siyasar yankin.
Jaridar Mwananchi mai amfani da harshen Swahili a Tanzaniya, ta buga labari a shafinta na farko dangane da korar jami'an zaɓe guda hudu da hukumar zaɓen kasar ta yi saboda sun haɗu da ƴan takara.
Jiya Litinin ne ta wallafa zanen barƙwanci a shafinta na farko mai taken "Sa'a 24 mai zafi a Kenya" wanda ya nuna ƴan takarar shugaban kasa guda huɗu suna kokawar shiga fadar gwamnati.
Jarida mai suna The Citizen, takwarar jaridar Mwananchi ta buga labari a shafinta na farko mai taken: "Abun da ƴan Kenya za su jefa wa ƙuri'a a zaɓen yau", ɗauke da banbanci tsakanin manufofin ƴan takarar shugabannin ƙasa William Ruto da Raila Odinga.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, FYNEFACE DUMNAMENE/BBC
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta koka akan yawan adadin ɗanyen man fetur da take asararsa daga sace shi, da ke kawo koma baya wajen samar da mai kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Karamin minista na albarkatun man fetur na ƙasar Timipre Sylva, ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma a fadar gwamnatin Jihar da ke Owerri.
Mista Sylva ya kara da cewa ɓata garin da ke aikata wannan laifi sun jawo adadin man da ake samarwa a rana ya ragu da wajen ganga 400,000, saboda haka a rana a maimakon a fitar da ganga miliyan 1.8 ya koma 1.4.
Sylva, ya samu rakiyar manyan kusoshin gwamnati da suka hada da ƙaramin ministan ilimi Goodluck Opiah, da babban hafsin jami'an tsaro Janar Lucky Irabo, da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), da Alhaji Mele Kyari.
Ya bayyana zuwan nasu a matsayin babban yunkuri domin samar da dawamammar hanyar daƙile satar mai a Najeriya.
Ya kuma ƙara da cewa sun je jihar ne domin neman goyon bayan gwamnatin jihar wajen taƙalar matsalar.

Asalin hoton, EPA
Ruwa ya mamaye filayen jirgin kasa da manyan hanyoyi a birnin Seoul na Koriya ta Kudu, biyo bayan mamakon ruwan sama a birnin tun jiya Litinin.
Hukumomi sun ce ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutum bakwai kuma ana kan neman wasu bakwai.
Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ke share motoci da yadda mutane ke kokarin tsira da ransu.
Wannan ce ambaliya mafi muni da birnin Seoul ya gani a cikin shekaru takwas.

Al'ummar Kenya sun fara fita rumfunan zaɓe, don zaɓar wanda zai maye gurbin Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ya shafe wa'adi biyu yana mulkin ƙasar.
Mr Kenyatta na goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa ne Raila Odinga, a maimakon mataimakinsa William Ruto.
Matsalar durƙushewar tattalin arziƙi da dimbin bashin da ake bin Kenya, na daga cikin abubuwan da duk wanda ya lashe zaɓen zai ji da su.
Masu sharhi na ganin kawancen Kenyatta da Odinga zai haɗa kan ƙasar, la'akari da cewa sun fito ne daga ƙabilu daban-daban.
Bayan zaɓen Shugaban kasa, masu jefa kuri'ar kazalika za su zaɓi gwamnoni da ƴan majalisa.