Sai da safenku
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Talata.
Ku tara gobe da safe domin kawo muku sababbi fil da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida, Rabiatu Kabir Runka and Umar Mikail
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Talata.
Ku tara gobe da safe domin kawo muku sababbi fil da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Asusun bayar da lamuni na duniya, International Monetary Fund (IMF), ya ce yana da yaƙinin samun bunƙasar tattallin arzikin duniya amma ya yi gargadi kan ci gaba da samun hauhawar farashi.
Cikin rahoton da ya fitar ranar Talata, asusun ya ce "harkokin tattalin arzikin duniya ya bunƙasa a zangon farko na bana, lamarin da ya sa aka yi sabon nazari kan hasashen tattalin arzikin duniya na 2023".
IMF ya ƙara da cewa "amma har yanzu bunƙasar ba ta kai yadda aka saba gani a tarihi ba, in ji IMF, kuma an yi hasashen zai kara yin kasa daga kashi 3.5 a bana zuwa 3.0 cikin 100 a 2024".
An yi hasashen raguwar tattalin arzikin ƙasashen yankin saharar Afirka da kashi 3.5 a bana, amma zai bunƙasa da kashi 4.1 a 2024.
IMF ya kuma yi hasashe kan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a yankin, Afirka ta Kudu da Najeriya, yana mai cewa tattalin arzikin Najeriya zai samu naƙasu saboda matsalolin tsaro da suka shafi ɓangaren mai.
Haka nan IMF ya ce tattalin arzikin Afirka ta Kudu zai samu koma-baya da kashi 0.3 a 2023 saboda rashin daidaiton lantarki a ƙasar.

Asalin hoton, Reuters
Kotu a Brussels ta samu mutum takwas da laifin kisan kai fiye da shekara bakwai bayan wani harin ƙunar baƙin-wake da ya kashe mutum 32 a tashoshin jirgin sama da na ƙasa na birnin.
An kai hare-haren ne a watan Maris na shekarar 2016.
Bayan daukar lokaci mai tsawo ana shari'ar da kuma kwanaki 19 da masu taimakawa alƙali suka shafe suna muhawara, kotun ta Brussels ta sanar da hukuncinta.
Tuni aka samu bakwai daga cikin waɗanda ake ƙarar da hannu a kan harin da aka kai birnin Paris wata ɗaya kafin wannan.
An kama Salah Abdeslam mai shekara 33 kwanaki kafin harin Brussels.
An same shi da hannu a harin bam da bindiga da aka kai Faransa cikin watan Nuwamban 2015, inda mutum 130 suka mutu.
Abdeslam ya tsere daga Paris zuwa Belgium a shekarar 2015, ya kuma musanta cewa yana da hannu a harin bam din.
Sai dai yanzu kotun ta Brussels ta same shi da laifin kisa da kuma yunƙurin yin kisa a birnin.

A birnin Tabarka da ke arewa maso yammacin Tunisiya, kilomita kadan daga iyakar ƙasar da Aljeriya, jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar daji.
Hayaƙi ya turnuƙe gonakin da suka ƙone yayin da yanayin iska ke ƙara gurɓacewa. Gidaje sun lalace kuma an rufe hanyoyin mota da dama.
Hukumomin Tunisiya sun kwashe mutum 300 daga ƙauyen Melloula daga kusa da wurin.
Sauran ƙasa daga birnin Tunis da sauran wurare sun fara kai masu tallafin abinci da ruwa da barguna kuma sun yi tayin ba su masauki a makarantun Tabarka.
Tsananin zafi ya ragu a yankin bayan kwanaki ana fama da shi, kuma yanzu haka yanayi ya kai maki 50 a ma'aunin selsiyas.
Hukumar tsaron farin kaya ta Aljeriya ta ce ta shawo kan kashi 80 na wutar dajin kuma mutum 34 sun mutu, ciki har da sojoji 10, yayin da wutar ta shafi yankuna 15.

Asalin hoton, @dabiodunMFR
Gwamnatin Jihar Ogun da ke kudancin Najeriya ta ce za ta fara raba wa ma'aikatanta naira 10,000 duk wata don rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Wata sanarwa ta ce tallafin wanda za a dinga ba da shi tsawon wata uku a zango na farko, ya ƙunshi har 'yan fansho.
Kazalika, za a dinga bai wa ma'aikatan lafiya da likitoci alawus ɗin rage kaifin hatsari.
Sauran matakan tallafin sun haɗa da:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, EPA
Aljeriya ta gayyaci manyan jami'an diflomasiyyar Denmark da Sweden don nuna damuwarta game da cin mutuncin Al-Ƙur'ani mai girma a kasashen biyu.
Tun a ranar Litinin rahotanni suka ce babbar kasuwar Qatar ta daina sayar da duk kayan da ake samarwa a Sweden.
Ana kuma ci gaba da nuna fushi kan abin da ya faru a ƙasashen Musulmai, inda masu zanga-zanga da gwamnatoci ke neman Sweden ta haramta ƙona littafin mai tsarki.
A ranar Litinin wasu mutum biyu da suka ce ƴan wata ƙungiya mai kishin Denmark ne suka ƙona Ƙur'ani a Copenhagen, babban birnin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ƙara yawan kuɗin ruwa da kashi 0.2 cikin 100 da masu cin bashi daga bankuna za su dinga biya a ƙasar.
Hakan na nufin yanzu duk wanda ya ci bashin banki zai biya kashi 18.75 na kuɗin da ya karɓa, maimakon 18.5 da aka saka a watan Mayu da ya gabata.
CBN ya ɗauki matakin ne da zimmar daƙile hauhawar farashi ta hanyar rage wa mutane sha'awar mallakar zunzurutun kuɗi.
Muƙaddashin Gwamnan CBN Fola Shonubi ya ce bankin ya cimma wannan matsaya ce bayan la'akari da tasirin cire tallafin mai, da na haɗe kan kasuwar canjin kuɗi, da kuma yunƙurin gwamnati na rarraba kayan tallafi.
Wannan ne ƙari na farko da Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan sauran matakan tattalin arziki da ya ɗauka tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.

Asalin hoton, NNPCL
Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya ce ya gano haramtattun matatun mai 69 cikin mako ɗaya da ya wuce.
Wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce sun kuma lalata haramtattun bututun man 93 a yankin Neja Delta mai arzikin mai da ke kudu maso kudancin ƙasar.
A 2022, wani rahoto ya ce Najeriya ta yi asarar gangar ɗanyen mai kusan miliyan 65, wanda ya kai fiye da naira tiriliyan biyu sakamakon fasa bututai.
Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari ta haɗa kai da jami'an tsaro masu zaman kansu don daƙile matsalar satar man.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ma'aikatar tsaron Girka ta tabbatar da cewa matuka jirgin sojin kasar sun mutu bayan hatsarin da jirgin kashe gobarar da suke ciki ya yi a tsibirin Evia.
Ma'aikatar ta ce matukan sun haɗa da kwamandansu mai shekara 34 da kuma mataimakinsa dan shekara 27.

Asalin hoton, Daily Trust
Jami'an tsaron Najeriya na farin kaya (DSS) sun sake kama dakataccen Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele bayan hatsaniyar da suka yi da jami'an gidan yari.
Lauyoyin Mista Emefiele sun faɗa wa manema labarai a Legas cewa sun bari DSS ta kama wanda suke karewa ne don gudun harbe-harbe tsakanin jami'an biyu.
Kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare gwamnan babban bankin na CBN a Gidan Yarin Ikoyi da ke Legas har sai ya cika sharuɗɗan belinsa da aka bayar kan naira miliyan 20 - dala 26,000.
DSS ta tuhumi Emefiele mai shekara 61 ne da mallakar ƙaramar bindiga ba bisa doka ba, zargin da ya musanta.
Mai Shari'a Nicholas Oweibo ya ɗage zaman kotun zuwa 14 ga watan Nuwamba.

Jami’an ‘yan sandan sirrin Najeriya, DSS da jami’an ganduroba sun yi arangama a babbar kotun tarayya da ke Legas kan tsare gwamnan babban bankin kasar da aka dakatar, Godwin Emefiele.
Kotun ta yanke hukunci da cewa dakatar Emefiele ya ci gaba da zama a gidan yari na Ikoyi da ke Legas har sai ya cika belin da aka ba shi a kan naira miliyan 20.
Jami’an DSS sun matsa kaimi wajen sake kama Mista Emefiele bayan shari’ar kotun da ta kai ga yin kace-nace tsakanin jami’an tsaron biyu.
An tuhumi Emefiele da laifin mallakar bindiga da harsasai daga hukumar DSS ba bisa ka'ida ba. Zargin da ya musanta.
Mai Shari’a Nicholas Oweibo ne ya bayar da belin Emefiele, mai shekaru 61, wanda ya yi watsi da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa zai iya tserewa zuwa wani ƙasa idan ya sami sarari.
An dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.

Asalin hoton, TIKTOK
Kamfanin TikTok mai dandalin wallafa labaran bidiyo mallakar ƙasar China ya ce zai ba da damar wallafa rubutu kawai ga masu amfani da shafin yayin da gasa tsakanin manyan kafofin sada zumunta ke daɗa zafi.
Dandalin ya ce sabon tsarin zai bai wa masu amfani da manhajar "wata hanya da za su iya bayyana kansu".
A farkon wannan watan, TikTok ya buɗe sabon ɓangaren kaɗe-ƙaɗe a dandamalin don yin gogayya da manhajojin kaɗe-kaɗe irinsu Spotify da Apple Music a Brazil da Indonesia.
Kuma a ranar Litinin, shafin Twitter na Elon Musk ya watsar da sanannen tambarin tsuntsu mai launin shuɗi inda ya canza shi da harafin X.
Yanzu za a bai wa masu amfani da TikTok zaɓi uku a manhajar - ko dai su wallafa hotuna ko bidiyo ko kuma kawai su yi rubutu.
Haka kuma za su iya yi wa saƙonninsu kwalliya ta hanyar ƙara sauti, ko wuri ko ƙara bidiyon da wasu masu amfani da TikTok suka yi.
"Wadannan siffofi za su sa saƙon rubutunku ya zama mai ƙayatarwa da damar faɗi-in-faɗa kamar kowanne bidiyo ko hoto," in ji TikTok.
TikTok, mallakar kamfanin ByteDance ne na kasar China.
Kasar Girka dai har yanzu na fama da matsanancin zafi da kuma mummunar gobarar dajin da ke ƙara kamari.
Ga hotunan da ke nuna halin da Girka ke ciki game da gobarar dajin.

Asalin hoton, SPYROS BAKALIS / AFP

Asalin hoton, LEFTERIS DAMIANIDIS / EPA

Asalin hoton, NICOLAS ECONOMOU / REUTERS

Asalin hoton, NICOLAS ECONOMOU / REUTERS

Asalin hoton, NICOLAS ECONOMOU / REUTERS

Asalin hoton, ANGELOS TZORTZINIS / AFP

Asalin hoton, NICOLAS ECONOMOU / REUTERS

Asalin hoton, Trade Union Congress/Facebook
Kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya, ta baiwa gwamnatin kasar wa’adin kwanaki goma sha hudu domin cimma matsayar da za ta rage radadin cire tallafin mai da ‘yan Najeriya suka shiga ko kuma fuskantar zanga-zangar ma’aikata.
A halin yanzu Najeriya na fama da matsalar tsadar rayuwa. Farashin sufuri da farashin abinci na ci gaba da hauhawa tun a watan Mayu bayan da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar, Mista Nuhu Toro ya shaida wa BBC a ranar Talata cewa kungiyar ba ta ji dadin tafiyar hawainiyar da ake yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin ba.
“Wani bangare na fahimtar da muka yi da gwamnati shi ne cewa a cikin makonni 8 ya kamata a samar da ingantattun matakan tallafi wadanda za a iya tabbatar da su kuma za a aiwatar da su cikin lokacin da aka amince."
"An kafa wasu ƙananan kwamitoci da za su yi aiki don warware matsalolin. Amma makonni hudu bayan hakan, ƙananan kwamitocin uku ne kawai suka nuna cewa sun yi wani abin a zo a gani. Wasu kwamitocin ba su fara aiki ba."
"Mun bayar da shawarar biyan mafi karancin albashi na N200,000 (kimanin $300) amma kamar yadda muke magana, kwamitin da ke aiki kan mafi karancin albashi bai zauna ba.”
Kungiyar ta bayar da wa’adin ranar 19 ga watan Agusta domin kammala tattaunawa ko kuma ta dauki wani mataki na kare ma’aikata da talakawa daga halin kuncin tattalin arziki.
Baya ga fara rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin mulki, TUC ta ce ya kamata gwamnatin tarayya da jihohi su rage yawan almubazzaranci da kuma rage yawan kudin da ake kashewa.
An dai nuna bacin rai game da karin farashin man fetur a fadin ƙasar inda a baya-bayan nan kungiyoyin kwadago suka yi barazanar janyewa daga tattaunawa da gwamnati.
Kungiyoyin sun zargi gwamnati da cire tallafin man fetur ba tare da fara aiwatar da matakan dakile illar da za ta yi wa ‘yan Najeriya ba.

Asalin hoton, Getty Images
Binciken da wata ƙungiyar masana yanayi ta duniya ta yi ya nuna cewa ba lallai ne a yi fama da tsananin zafin da aka yi a baya-bayan nan a Turai da Amurka ba, ba don dumamar yanayi da mutane ke haddasawa ba.
Ƙungiyar kula da yanayin ta duniya ta yi gargaɗi kan fuskantar tsananin zafin a nan gaba, zai iya fin yawa matuƙar ba a rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli cikin sauri ba.
A watan Yuni ne aka fi fuskantar yanayin zafi a duniya, inda a Turai, da sassan Amurka, da Mexico da China yanayin ya kai har sama da maki 45 a ma'aunin salsiyas.
Lamarin da ya haifar da mummunar gobarar daji, da raba dubban mutane da muhallansu.

Asalin hoton, CBN
Babbar kotun tarayya a birnin Legas ta bayar da belin gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a kan naira miliyan 20, bayan ya shafe mako shida a hannun hukumar ‘yan sandan sirri ta DSS.
Mista Emefiele ya ƙi amsa laifin da ake tuhumar sa a kai guda biyu na mallakar bindiga guda ɗaya da harsashi 23, zargin da rundunar ‘yan sandan sirri ta gabatar.
A ranar Talata ne gwamnan bankin da aka dakatar ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya bayan umarnin wata kotu na gurfanar da shi ko kuma a sake shi daga hannun hukumar DSS.
A watan jiya ne, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sanar cewa Emefiele yana hannunta kwana guda bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa daga aiki.
A hukuncin da aka yanke a ranar Talata, alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Mista Emefiele a gidan yari na Ikoyi, da ke Legas har sai an kammala cika ka'idojin belinsa.
"An dage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba."

Asalin hoton, AFP
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi ga wasu manyan jami'an gwamnatin Mali uku da aka ce su ne ke jagorantar ayyukan dakarun sojin Wagner na Rasha a ƙasar ta yammacin Afirka.
Mutanen uku sun haɗar da ministan tsaron Mali da babban hafsan sojin sama da mataimakin hafsan hafsoshi, in ji sakataren wajen Amurka Antony Blinken.
Ya ce mace-macen fararen hula ya ninka sau uku tun bayan tura dakarun Wagner zuwa ƙasar Mali a watan Disamban 2021, inda ya ƙara da cewa "da yawa a cikin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da sojojin Mali suka kai ne tare da sojojin haya na ƙungiyar Wagner".
Washington da ƙawayenta sun shafe tsawon shekaru suna ƙaƙaba wa Wagner da magoya bayanta takunkumi, inda aka zargi kungiyar masu fafutuka da take hakkin bil'adama da yaɗa labaran karya. A Janairu, gwamnatin Washington ta nada Wagner a matsayin "kungiyar masu aikata laifuka a duniya".
A makon jiya ne, Birtaniya ta kakaba takunkumi ga wasu mutane 13 da ke da alaƙa da Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali da Sudan.
Tun bayan da sojojin Faransa suka fice daga Mali a watan Agustan da ya gabata da kuma buƙatar janyewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya a can, gwamnatin mulkin sojan Mali da ta kwace mulki a watan Mayun shekarar 2021, ta koma Wagner.
Ana tunanin Wagner yana da dakaru kusan 1,000 a ƙasar Sahel wadda ta kasance cibiyar rikicin jihadi da tashe tashen hankula na siyasa tsawon shekaru.

Asalin hoton, CBN
An gurfanar da gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da aka dakatar, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas a safiyar Talata bisa zargin aikata laifuka biyu da suka hada da mallakar makamai da alburusai ba bisa ka'ida ba.
An gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo, bayan shafe sama da makonni shida da kama shi da hukumar DSS ta yi.
Bayan fafutuka da lauyan Emefiele ya yi na kalubalantar tsare shi na tsawon lokaci da hukumar DSS ke yi, ‘yan sandan sirrin suka gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 13 ga watan yuli saboda da matsin lamba da ke kansu.
Da ya bayyana a gaban mai shari’a Oweibo, Emefiele ya ƙi amsa laifin da gwamnati ke tuhumarsa da shi.
Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Joseph Daudu ne ya jagoranci sauran lauyoyin da ke kare Emefiele.
Shugaba Bola Tinubu dai ya dakatar da Emefiele a matsayin shugaban babban bankin Najeriya ne a ranar 9 ga watan Yuni, 2023. Kwana daya bayan haka, hukumar DSS ta tabbatar da cewa ta kama Emefiele.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar shari'ar Amurka na shirin gurfanar da jihar Texas a gaban kotu, a kan wasu shingaye da ta sanya a kogin Rio Grande don hana bakin haure daga Mexico wucewa.
Babban lauyan Amurka mai kula da yankin yammacin Texas,Jaime Esparza,ya ce shingayen sun saɓa wa dokar zirga-zirga a ruwa.
Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karine Jean-Piyer, ta ce gwamnan jihar ta Texas- Greg Abbott- na jefa rayuka cikin haɗari.
Ta ce "ya ci gaba da nuna irin wannan rashin tausayi wajen ci gaba da wannan tsari da aka daina amfani da shi lokaci mai tsawo, abun da yake yi na da haɗari, kuma yana shafar abun da muke son cimmawa."
Sai dai a wata sanarwa da gwamna, Gregg Abbot, ya fitar ta kafar sada zumunta, ya ce kundin tsarin mulkin Amurka ya bai wa Texas ikon kare iyakokinta, ya kuma zargi shugaba Joe Biden da rashin aiwatar da dokokin shige da fice na tarayya.