Falasdinawa na murnar sako 'yan'uwansu da Isra'ila ta yi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas

  2. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan za mu dakata a yau, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  3. Na yi mamakin sakin da aka yi mana - Bafalasɗiniya

    .

    Daya daga cikin Falasɗinawan da ake tsare da su, aka kuma sake su a yau , mai suna Marah Bakeer, ta isa gidan mahaifiyarta a unguwar Beit Hanina da ke Birnin Kudus

    A shekarar 2015 ne aka kamata, a lokacin tana da shekara 16, aka kuma ɗaure ta shekara takwas da rabi saboda harin wuƙa da ta kai wa jami'in ɗan sanda a kan iyaka.

    Bakeer ta shaida wa manema labaran da ke dakon isarta gida cewa: "yarjejeniyar sakin namu na zuwa ne bayan da mutane da dama sun mutu, hakan ya sa ba mu yi murna ko jin daɗi ba".

    Ta ce an ɗaure ta ne a wani ɗaki na daban a gidan yarin, don haka ''ba mu da masaniya kan abin da ke faruwa a waje, ba m,u san halin da Gaza ke ciki ba''.

    "Labarin yarjejeniyar ya matuƙar ba mu mamaki," in ji ta.

    .
  4. 'Yan adawa sun ce ba za su amince da sakamakon zaɓen Madagascar ba

    'Yan adawar siyasa a Madagascar sun ce ba za su amince da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin makon da ya gabata ba, wanda ake sa ran ayyana shi gobe Asabar.

    A hukumance sakamakon na nuna cewa shugaban ƙasar, Andry Rajoelina, da ke neman wa'adin mulki na biyu ne ke kan gaba.

    'Yan adawar sun ce bai kamata a bar shugaban ƙasar ya yi takara ba saboda a shekarar 2014 ya samu takardar shaidar zama ɗan ƙasar Faransa.

    Dama dai ana ci gaba da aza ayar tambaya kan sahihancin zaɓen. kashi 60 na masu kaɗa ƙuri'a ba su yi zaɓe ba, yayin da 'yan adawa ke ci gaba da tayar da jijiyar wuya, kan zaɓen da suka bayyana da shiririta.

    'Yan takara 11 a zaɓen sun ce ba za a zarge su da duk wani tashin hankalin da ka iya biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen ba.

    A shekarar 2009 kwaɗayin mulki tsakanin manyan 'yan siyasar ƙasar, ya haifar da mummunan rikici da ya janyo wa ƙasar koma-baya ta fuskar tattalin arziki.

    Akwai fargabar yiwuwar maimata abin da ya faru a wancan lokaci.

  5. Musayar fursunoni yanzu aka fara - Biden

    .

    Shugaban Amuka Joe Biden ya ce musayar fursunoni da aka fara tsakanin Isra'ila da Hamas ''Farau ne na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai, shugaba Biden ya ce yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki, har sai an kammala sako duka mutanen da ake garkuwa da su.

    ''Ba za mu dakata ba, har sai an sako duka mutanen'', in ji shugaban na Amurka.

  6. Falasdinawa suna murnar sako 'yan'uwansu daga gidajen yarin Isra'ila

    Palestinians
    Bayanan hoto, An daga wani matashi da ke cikin mutanen da Hamas ta sako, a kafada, lullube da wata koriyar tuta

    Jimillar Falasdinawa 39 ne Isra'ila ta sako daga gidajen yarinta, kuma ana iya ganin yadda murna ta kaure a yankin Gabar Yamma, daidai lokacin da cincirincon mutane suka taru don yi musu maraba da komawa gida.

    Mata 24 da matasa 15 ne aka saki a kan iyakar wani shingen bincike na Beitunia, a kusa da Ramallah.

    Cincirindon mutane ne suka tarbe su inda suke karkada tutoci da harba tartsatsin wuta a sama.

    Palestinians
    Bayanan hoto, A tsallaken shingen bincike a Beitunia, wani rukunin maza dauke a kafada a cikin cincirindon mutane da ke karkada tutoci sama
    Palestinians
    Bayanan hoto, A gangaren titi kuwa, babban birnin Ramallah, ana iya ganin wani cincirindon mutane suna karkada tutocin Falasdin, a lokacin da suke jiran isowar mutanen da Isra'ila ta sako
  7. Ma'aikata sama da 3000 da muka gada, ba su cancanci a dauke su aiki ba - Gwamnatin Kano

    Gwamnatin Kano ta ce ta kammala aikin tantance dubban ma'aikatan da tsohuwar gwamnatin jiihar ta dauka a karshen wa'adin mulkinta, inda ta tabbatar da sama da mutum 9,000, a matsayin halastattu.

    A bangare guda kuma ta ce ma’aikata 3,234 daga ciki, ta gano cewa ba su cika ka'idoji ba, don haka ta soke daukar su aiki.

    Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan nazarin rahoton kwamitin da ya tantance ma’aikatan.

    A farkon hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya ba da umarnin dakatar da ma’aikata fiye da 12,000 daga aiki, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

    Ga karin bayani a cikin rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
  8. Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris

    .

    Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Nasir Idris na ranar 18 ga watan Maris a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kebbi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ayarin alkalai guda uku da suka saurari shari'ar, sun yanke hukuncin cewa karar da dan takarar gwamnan Kebbi na jam'iyyar PDP, Janar Aminu Bande (mai ritaya) ya daukaka, ba ta da tushe.

    A wani hukunci da alkalan dukkansu suka amince da shi karkashin jagorancin Mai shari'a Ndukwe Anyannwu, kotun daukaka karar ta cimma matsaya kan batutuwa guda biyar da Janar Bande ya shigar gabanta, inda ta bai wa Gwamna Nasir Idris gaskiya.

    Mai shari'a Anyanwu ya cimma matsayin cewa masu kara ba su iya tabbatar da zarge-zargen da suka yi a kan takardar kammala karatu ta mataimakin gwamnan na jam'iyyar APC, Abubakar Umar Tafida ba kamar yadda doka ta tanada.

  9. 'Ina fursunonin suke?' Cincirindon mutanen da suka taru a Gabar Yamma suna tambaya

    West Bank

    Cincinrindon sun kewaye motar kungiyar agaji ta Red Cross a shingen bincike na Beitunia da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda ake sa ran za a mika wa ƙungiyar fursunonin Falasɗinawa 39 da Isra'ila ke tsare da su.

    Mun ji labarin cewa an jikirta sakin fursunonin ne sakamakon samun wata 'yan tangarɗa da aka samu tsakanin wasu Falasɗinawa da jami'an tsaron Isra'ila.

    Cincirindon mutanen sun yi rera waƙoƙin da cewa "ina fursunonin suke, ina fursunonin suke ne?

  10. Labarai da dumi-dumi, Falasdinawan da Isra'ila ta sako sun isa Gabar Yamma

    Falasdinawan da Isra'ila take tsare da su sun isa shingen bincike na Beitunia checkpoint a Gabar Yamma da Kogin Jordan, kusa da Ramallah.

  11. Akwai mata biyu 'yan sama da shekara 70 a cikin waɗanda Hamas ta saki

    Yanzu muna samun tabbaci na sunayen wasu daga cikin mutanen da aka sako su, a wani bangare na yarjejeniyar Hamas da Isra'ila.

    Daya daga cikinsu ita ce Margalit Moses, mai shekara 78. 'Yan Hamas sun sace dattijuwar mai fama da cutar kansar ne, a Kibbutz Nir Oz ranar 7 ga watan Oktoba.

    An bayyana ta a matsayin mai son halittun ban ƙasa, wadda take ƙaunar zuwa tattaki don nishaɗi duk da matsalolin lafiyarta.

    Kungiyar da ke magana a madadin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su tare da danginsu, ta ce an san Margalit da yawan sakar riguna don jikokinta.

    Hamas Hostage released
    Bayanan hoto, Margalit Moses na ɗaya daga cikin mutanen da Hamas ta sako

    Adina Moshe, 'yar shekara 72, an sace ta ne ranar 7 ga watan Oktoba daga gidanta da ke Kibbutz Nir Oz zuwa Gaza, bayan 'yan Hamas sun hallaka mijinta Sa'id Moshe.

    Danginta sun shaida ta a cikin wani bidiyo da ke nuna ta a hannun wasu mayaƙan Hamas biyu a kan babura.

    Tana da 'ya'ya guda hudu kamar Maya da Yael da Sasson da kuma Amos.

    "Za ta so komawa don ci gaba da bayar da taimako wajen rainon jikokinta da ke zaune a Kibbutz da kuma komawa ga harkokin da take sha'awa: girke-girke da shuke-shuke da karanta littattafai," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.

    Hamas hostage released
    Bayanan hoto, Adina Moshe na ɗaya daga cikin mutanen da Hamas ta sako a yau Juma'a
  12. Dakarun Isra'ila za su yi wa mutanen da Hamas ta sako rakiya zuwa asibiti

    .

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na musamman za su yi wa mutanen da Hamas ta sako rakiya zuwa asibitin Isra'ila inda iyalai da dangin mutanen ke jiransu.

    Rahotonni sun ce an yi wa mutanen gwaje-gwajen lafiya tun da farko, inda yanzu kuma suke kan hanyar zuwa asibiti domin ƙara basu kulawar da ta dace, kafin a miƙa su ga iyalansu.

    ''Dakarun sojin Isra'ila da sauran jami'an tsaronmu za su ci gaba da aiki don tabbatar da mutanen sun isa gidajensu'' Kamar yadda rundunar sojin Isra'ilar ta bayyana.

  13. Qatar ta yi karin bayani a kan mutanen da Hamas ta sako yau

    Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce Hamas ta sako 24 a cikin mutanen da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza a yau.

    A wani sako da ta wallafa a dandalin X, wani magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce rukunin wadanda aka sako din sun kunshi 'yan Isra'ila 13 da 'yan kasar Thailand 10 da kuma wani dan kasar Philippines daya.

    Qatar ce ta shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Tun farko, fira ministan Thailand ya ce 'yan kasarsa mutum 12 Hamas ta sako.

  14. An yi ta sowa lokacin da motocin Red Cross suka tsallaka cikin Masar daga Gaza

    Bayanan bidiyo, Kalli yadda aka kaure da sowa lokacin da motocin Red Cross suka tsallaka cikin Masar daga Zirin Gaza

    Wannan ne lokacin da motocin jif dauke da mutanen da Hamas ta sako suka shiga cikin Masar daga yankin Zirin Gaza.

    Kungiyar ba da gaji ta Red Cross ta tabbatar cewa mutum 24 ne Hamas ta sako. Kuma sun samu rakiyar jami'an Red Cross takwas da wani likita guda daya.

  15. Falasdinawa sun yaba wa yarjejeniyar da cewa 'yar karamar nasara ce

    Cincirindon mutanen da suka taru yayin da duhun almuru ya fara sauka a shingen bincike na Beitunia - inda dangi da magoya baya suka tsaitsaya suna jiran isar fursunoni.

    Wata 'yar karamar nasara ce, kamar yadda wasu suka bayyana.

    “Alama ce ta kyakkyawan fata ga Falasdinawa da kuma 'yan Isra'ila,” a cewar Mohammed Khatib, “cewa tsagaita wutar za ta ci gaba kuma za a dakatar da kashe-kashe”.

    “Za mu so faruwar wannan al'amari ba tare da a ce Hamas ta kwashi mutanen da ta yi garkuwa da su ba,” ya shaida wa BBC, “amma ba don su ba, Isra'ila ba za ta bar wadannan mutanen su fito ba.”

  16. 'Yan Isra'ila na jiran mutanen da Hamas ta sako a wani asibiti

    Israel
    Bayanan hoto, Cibiyar lafiya ta Schneider a Petah Tikva, cikin Isra'ila inda ake sa ran za a kai mutanen da Hamas ta sako
    Israel
    Bayanan hoto, Mutane sun tsaye a jikin shingen asibitin suna kallo, yayin da suke jiran zuwan mutanen da Hamas ta sako bayan garkuwa da su
    Israel
    Bayanan hoto, A ciki, an shirya zauren karbar baki don maraba da su
    Israel
    Bayanan hoto, An kuma tanadar wa kananan yaran da ke cikin mutanen da Hamas ta sako, kayayyakin wasa
    IDF
    Bayanan hoto, A lokaci guda kuma daga wajen asibitin, ana iya ganin wata motar asibiti da ke jiran isar mutanen da aka yi garkuwa da su
  17. Labarai da dumi-dumi, An kai 'yan kasar Thailand 12 da Hamas ta sako zuwa asibitin Tel Aviv

    Dangane da 'yan kasar Thailand 12 da Hamas ta sako, bayan garkuwa da su a Gaza, kafofin labaran Thailand sun ba da rahoton cewa mutanen da aka yi garkuwa da su, sun tsallaka cikin Isra'ila ta mashigar Rafah kuma an kai su cibiyar lafiya ta Shamir da ke kudancin Tel Aviv.

    A can ne za su samu kulawar likitoci sannan an ba da rahoton cewa za su zauna a cibiyar har tsawon sa'a 48.

    An sako su a karkashin wata yarjejeniya daban-daban da Qatar da kuma Masar suka shiga tsakani da Hamas, wani jami'i da ya yi karin haske game da tattaunawar ya ce.

    Jami'in ya ce 'yar kasar Thailand din da Hamas ta sak dukkansu maza ne.

  18. Labarai da dumi-dumi, Red Cross ta tabbatar da fara aikin sada mutanen da aka sako da danginsu

    Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta tabbatar da cewa an fara aikin "sada mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma wadanda Isra'ila ke tsare da su da danginsu".

    Kungiyar dai zuwa yanzu ba ta tabbatar da ko mutum nawa ne jami'anta suka karba ba, sai dai ta bayyana aikin a matsayin wani al'amari mai "gabobi da yawa a rana guda" wanda zai kunshi tabbatar da kai kayan agaji zuwa Gaza.

    Muna sa ran samun karin bayani daga Red Cross, da cikakken bayani a kan adadin mutanen da aka sako, nan gaba a yau.

  19. Isra'ila za ta saki Falasdinawa 39 da take tsare da su

    Jimillar Falasdinawa 39 da ake tsare da su ne, ake daf da saki daga gidajen yarin Isra'ila a ranar Juma'a da nufin musaya da wani rukunin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

    Yarjejeniyar - wadda Qatar ke shiga tsakani - ta kunshi dakatar da fada na tsawon kwana hudu.

    Ana zargin mutanen da Isra'ilan ke tsare da su bisa aikata laifuka daban-daban, kama daga jifa da duwatsu da kuma yunkurin aikata kisan kai.

    An ba da rahoton cewa motocin bas-bas na kungiyar ba da agaji ta Red Cross sun isa gidan yarin Ofer prison a yankin Gabar Yamma da ke karkashin mamaya, suna jiran a saki mata Falasdinawa 24 da kuma maza 15 'yan kasa da shekara 18.

    Za a kai su wani shingen binciken sojojin Isra'ila a Gabar Yamma daga nan kuma za a bar su, su koma gidajensu a cewar hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila.

    An zabo mutanen da za a saki ne daga jerin mata da kananan yara 300 da Isra'ila ta tattara.

  20. Hotuna: Yadda Falasɗinawan da yaƙi ya ɗaiɗaita a Gaza ke komawa gida

    Yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki huɗu tsakanin Isra'ila da Hamas ta fara aiki tun da farko, Falasɗinawa da yaƙi ya ɗaiɗaita na ta ƙoƙarin komawa gidajensu a Zirin Gaza.

    A kudancin Gaza, dakarun tsaron Isra'ila sun yi ta ajiye takardu da ke bai wa mutane shawarar kada su shiga arewacin Gaza, inda ta suka ce tsagaita wuta da aka yi na wucin-gadi ne, kuma arewacin Gaza fagen yaƙi ne.

    Gaza
    Bayanan hoto, Falasɗinawa da yaƙi ya ɗaiɗiata a birnin Khan Younis ke ƙoƙarin komawa gidajensu a safiyar yau bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki huɗu ta fara aiki
    Gaza
    Bayanan hoto, Akwai dogayen layuka a mashigar Rafah kusa da iyaka da Masar yayin da kayan agaji ke isowa Gaza domin rabawa
    Gaza
    Bayanan hoto, Takardu da sojojin Isra'ila suka ajiye a Rafah ya gargaɗi Falasɗinawa kan tafiya zuwa arewacin Gaza, inda suka ce tsagaita wutar da aka yi na wucin-gadi ne
    Gaza
    Bayanan hoto, A can birnin Khan Younis, a kudancin Gaza, wani yaro Bafalasɗine da yaƙi ya ɗaiɗaita ɗauke da kayayyakinsa