Lana Nusseibeh: Bafalasɗiniyar da ke takarar shugabancin MDD
Asalin hoton, Getty Images
Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsayar da wata karamar ministar harkokin waje a matsayin yar takarar da za ta gaji Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da zarar wa'adinsa na biyu ya kare a karshen wannan shekarar.
Lana Nusseibeh ta yi aiki a matsayin jakadiyar Abu Dhabi a Majalisar Dinkin Duniya na fiye da shekara goma.
Wakilin BBC ya ce Idan aka zabe ta, Ms Nusseibeh, wadda asali ƴar Falasdin ce , za ta zama mace ta farko da za ta jagoranci wannan ƙungiya, kuma ta biyu daga yankin Gabas ta Tsakiya bayan Boutros Boutros Ghali.
Akwai wasu ƴan takara shida da ke fafatawa, inda Rebeca Grynspan daga kasar Costa Rica ke kan gaba da tazara kadan a kuri'un zaben share fage.
An sauke wani malami daga limanci a Bauchi saboda zargin yi wa Tinubu kamfe
Asalin hoton, Getty Images
An sauke Limamin masallacin unguwar Madina da ke cikin garin Bauchi daga muƙaminsa bayan da aka zarge shi da yaɗa manufofin sake zaɓar shugaban Najeriya Bola Tinubu a cikin wa'azinsa.
Rahotanni sun ce limamin mai suna Dahiru Abubakar na amfani da lokutan huɗuba bayan kammala sallolin farilla wajen bayyana ra'ayoyi da ake kallon suna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana kan lamarin, Liman Dahiru Abubakar ya ce a wa'azinsa yana jan hankalin jama'a ne cewa Shugaba Tinubu ba shi ne silar wahalhalun tattalin arziki da matsalolin tsaro ba, yana mai cewa waɗannan ƙalubalen suna da alaƙa da abin da ya kira "alamomin ƙarshen zamani."
"Na kasance ina wa'azin mutane su daina ɗora alhakin matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki a kan Shugaba Tinubu. Ina kuma ƙarfafa musu gwiwa su sake zaɓensa tare da ba shi wata dama a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da manufofinsa," kamar yadda Daily Trust ta ambato sgi yana cewa.
Ya ci gaba da cewa wa'azinsa ya fi karkata ne kan tsoron Allah da kuma daina ɗora wa shugabanni laifin matsalolin tsaro, musamman Tinubu, domin Allah kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli ta hanyar amsa addu'a.
"A wa'azina nakan mayar da hankali kan tsoron Allah da ayyukanmu na yau da kullum. Na kan kawo misalan matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu ƙasashen Afirka kamar Sudan, Chadi da Mali, sannan in tambaya ko Tinubu ne ke da alhakin abin da ke faruwa a waɗannan ƙasashe."
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce matsalar kwamitin da limamin ba ta taƙaitu ga zargin yaɗa manufofin Tinubu kaɗai ba.
"Babbar matsalarmu da shi ita ce ba wai yaɗa manufofin Tinubu kawai yake yi ba, har ma da yadda yake tara mutane a gaban masallaci, kuma wani lokaci yakan shiga cikin masallacin ne da gangan domin tattauna harkokin siyasa."
Mutane sama da 800,000 za su iya rasa muhallansu a Somalia - IOM
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kusan mutum 874,000 na iya rasa matsugunansu a Somalia cikin watanni uku masu zuwa sakamakon ambaliya.
Hukumar ta ce kogunan da ke cika da ruwa da kuma mamakon ruwan sama na barazana ga al'ummomin da tuni suke fama da fari da kuma yawan ƙaura.
Shugaban IOM a Somalia, Manuel Marques Pereira, ya ce akwai fargabar cewa dubban iyalai za su rasa gidajensu na makonni. Ya ce mutane da dama sun riga sun kaurace wa muhallansu, kuma ba su da isassun hanyoyin da za su dogara da su wajen tinkarar sabon bala'in.
Ya kuma yi kira da a samar da kuɗaɗe cikin gaggawa domin taimaka wa mutane kare gidajensu da rayukansu.
Sabbin hasashen da IOM da Hukumar ƴan gudun hijira ta Denmark (DRC) suka fitar sun nuna cewa mutum 874,319 na iya ƙaura daga gidajensu tsakanin Oktoba da Disamba, inda ambaliya za ta haddasa kashi 92 cikin 100 na wannan ƙaurar.
Gargaɗin na zuwa ne yayin da Somalia ke shiga lokacin damina, tare da hasashen samun ruwan sama fiye da yadda aka saba sakamakon tasirin El Niño.
IOM ta ce ya zuwa yanzu ta samu kashi 14.4 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen da take buƙata domin shirin tunkarar ambaliyar.
Tuni dai alamun ambaliya suka fara bayyana a yankuna kamar Doolow, Jowhar da Baidoa, yayin da ake hasashen cewa Beledweyne da Gaalkacyo za su kasance daga cikin wuraren da za su fi fuskantar barazanar ƙaura sakamakon ambaliya.
Masu zanga-zanga sun tayar da hayaniya wajen taron Trump
Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zanga sun tayar da hayaniya a wani gangamin da Shugaba Trump ya gudanar a jihar South Carolina kafin zaben tsakiyar wa'adi da ke tafe a Amurka.
Jami'an tsaro sun kori akalla masu zanga-zanga goma daga wurin taron da aka yi a Jami'ar Clemson, wanda Mista Trump ya halarta, da nufin kara wa sanata Darline Graham na jam'iyyar Republican kwarin gwiwa.
Wani mai zanga-zanga ya kira Mista Trump maci amana kuma ya yi nemi da a saki bayanan Jeffrey Epstein.
Wani kuma ya kira shi mai aikata laifukan yaki. Mista Trump ya bayana masu zanga-zangar a matsayin sojojin haya kuma ya yaba wa wani mai goyon bayansa da ya cusa wa daya daga cikinsu naushi.
Ana ci gaba da luguden wuta tsakanin Rasha da Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da artabu tsakanin Rasha da Ukraine, duk da cewa Shugaba Trump ya bayyana ra'ayinsa na cewa bangarorin da ke yaki da juna a yanzu sun fi kusa da kawo karshen yaƙin fiye da kowane lokaci tun farkon rikicin.
Rasha ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Kyiv, babban birnin Ukraine, kwana guda bayan ta amince da sabon zagayen tattaunawar zaman lafiyar.
Magajin garin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya bayyana cewa mutum shida ne suka jikkata sakamakon hare-haren.
Duk da wadannan hare-hare da Rasha ke kai wa, Shugaban Ukraine ya bayyana goyon bayansa ga shawarar Amurka na sake fara tattaunawa da Rasha.
Ya ce ganawar da Steve Witkoff ya yi da Rasha na da matukar muhimmanci, abin da muka fahimta daga ganawar shi ne Rasha na goyon bayan tattaunawa tsakanin kasashen mu uku
Iran ta ce ta tarwatsa jiragen ruwa huɗu a tekun Fasha
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ruwa ta dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan wasu jiragen ruwa huɗu da take sanya ido a kansu a arewa maso tsakiyar Tekun Fasha.
Dakarun sun ce lamarin ya faru ne yayin da jiragen ke jigilar man fetur zuwa wani jirgi, inda daga bisani gobara ta tashi a cikinsu.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana jiragen ruwan a matsayin waɗanda suka karya doka, tana mai cewa sun bi hanyoyin ruwa da ba su dace ba.
Iran ta ce ba za ta amince da wasu hanyoyin da jiragen ruwa ke amfani da su a kudancin mashigin Hormuz ba, duk da cewa ana amfani da su wajen zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Rundunar ta kuma ce wasu jiragen ruwa uku sun yi hatsari a daren Laraba bayan sun taka nakiyoyin da aka dasa a cikin ruwan a yammacin mashigin Hormuz, lamarin da ya haddasa gobara.
A cewarta, yawan irin waɗannan haɗurran na da alaƙa da amfani da hanyoyin ruwa da ta ce ba su da tsaro.
A ƙarshen sanarwar, rundunar ruwa ta IRGC ta zargi sojojin Amurka da ci gaba da abin da ta kira tsokana a yankin.
Ta kuma yi gargadin cewa ci gaba da irin waɗannan matakai na iya janyo martani mai faɗi da zai shafi sansanonin sojin Amurka da ke yankin.
Assalam alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.
Kamar dai jiya, yau ma Rabi'atu Kabir Runka ke muku fatan an wayi gari lafiya domin kawo muku wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa