Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Rufewa
Anan zamu dakata da kawo muku labarai da rahotanni a wannan shfin namu da ke zuwar muku kai tsaye.
Ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu, domin samun wasu labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, har ma da wasu sauran nahiyoyin duniya.
Buhari Muhammad Fagge ke muku fatan mu kwana lafiya.
Wanne hali shugaban Amurka Donald Trump ke ciki
Likitocin da ke kula da lafiyar Shugaba Trump daga cutar Corona da ta kama shi sun ce yana ci gaba da samun sauki , kuma suna fatan za su iya sallamar shi daga asibiti a ranar Litinin.
Yayin jawabi game da halin da shugaban na Amurka ya ke ciki a harabar asibitin da aka kwantar da shi, Tawagar likitocin ta ce an ya yi amfani da abin iskar Oxygen, ba tare da bayyana adadin lokacin ya ɗauka ba.
Daya daga cikin likitocin, Sean Conley ya yi kokarin nuna irin halayyar ta shugaban da tawagar likitocinsa bayan ya kauce wa cewa a ranar Asabar an saka wa Mista Trump iskar oxygen.
'Yar jarida ta yi ɓatan dabo a Masar
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Masar sun tsare wata ƴar jaridar da ta bata a lokacin da take aikin daukar rahoton zanga-zanga a garin Luxor da ke kudancin kasar.
Ba a bar Basma Mustafa ta samu damar gana wa da lauya ba kuma har yanzu ba a san tuhumar da ake yi mata ba.
Tun a ranar Asabar ba a sake jin duriyarta ba a haduwar da ta yi da abokan aikinta na kafar al-Manassa lokacin da ta fada musu cewa wani dan sanda na bibiyarta.
Zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon harbin da ake zargin ‘yan sanda sun yi wa wani mutumin yankin.
Masar dai na cikin manyan kasashen da aka bayyana a matsayin masu kuntatawa yan jarida.
Rabon da a ci Man utd 4 a minti 45 din farko a Old Trafford tun 1957
Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta zuba wa Manchester United ruwan kwallaye har 6-1 a Old trafford.
Tun 1957 da Tottenham din suka taɓa cin United 4-3 a Old Trafford rabon da a ƙara yi wa kungiyar irin wannan cin kashin na kwallaye 4 a minti 45 din farko.
A minti 28 aka bai wa dan wasan gaban kungiyar Martial jan kati, wanda shi ne jan katin da aka fara bai wa kungiyar da wuri a shekara 16 a Premier.
Da wadannan kwallayen da Harry Kean da Son suka ci, yanzu sun ci kwallo 26 a junansu.
Jose Mourinho na daga cikin kocin kalilan da suka taɓa riƙe ƙungiya kuma bayan sun barta suka buga wasa suka ci ta biyar.
Manchester United ce kungiyar da aka bai wa bugun fenariti uku a jere a gida tun bayan Arsenal da ta yi hakan a 2016.
Yanzu dai Manchester United na matsayi na 16 a teburin gasar, gurbi daya ne tsakaninta da ukun ƙarshen tebur.
Ana zanga-zanagr adawa da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan
Asalin hoton, Getty Images
Masu
zanga-zanga a Sudan sun rufe tashar sauke kaya ta kasar da kuma titin da ya haɗar
birnin tashar ruwan ƙasar da Khartoom.
Rahotanni
na cewa masu adawa ne da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya wa hannu
tsakanin gwamnati da kawancen ‘yan tawaye a ranar Asabar.
Yarjejeniyar
ta mayar da hankali ne wajen ganin an kawo karshen rikicin da yake faruwa a
yankunan suke cikin wani hali kamar Darfur, amma masu zanga-zangar na cewa su
ba su goyon bayan sanya kungiyoyin ‘yan tawayen da ke gabashin kasar.
Sun kuma yi
ƙorafin shigowar kasashen waje cikin yarjejeniyar – wanda suke magana kan
Hdaddiyar Daular Larabawa.
Za a kafa gandun kiwon jakuna a Bauchi da Ebonyi
Asalin hoton, Getty Images
Cibiyar
bincike don bunƙasa kiwon dabbobi a Najeriya NAPRI da hadin gwiwar wasu abokan
hulda za su yaki tare domin samar da gandun kiwon jakuna a jihohin Bauchi da
Ebonyi.
Kamfanin
dillancin labarai na ƙasar NAN ya ruwaito shugaban cibiyar Farfesa Abdullahi
Mohammed na cewa sun kulla wata yarjejeniya da abokan huldarsu a watan Fabrairu
domin samar da jakai miliyan biyu a Najeriya nan da shekara biyar zuwa 10.
Farfesan ya
ce shirin zai iya samarwa da kasar kudin shiga da suka kai dala biliyan biyu a
ko wacce shekara.
Bayan bunkasa
kiwon jakai da shirin zai yi, zai kuma taimaka wajen fadada komar tattalin
arzikin kasar a bangaren kiwo da harkar noma.
Rikicin siyasa ya barke a Kenya
Asalin hoton, Getty Images
A kenya mutum
biyu sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani rikici da ya barke
tsakanin magoya bayan shugaban kasar Uhuru Kenyatta da na mataimakinsa William
Ruro.
Bangarorin
biyu sun yi ta jifan junansu da duwatsu tare da kona tayoyi yayin da Mista Ruto
ya je wata coci a wani yankin magoya bayan shugaban kasar.
Mista
Kenyatta da Mista Ruto sun dade suna hamayya da juna a siyasance, amma lokacin
da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta zarge su da tayar da hankali yayin
zabe, sai suka tayar da wani kawancen siyasa a 2013.
Rahotanni
na cewa tun bayan wannan lokacin ne suka fara faɗa da juna, saboda niyyar Mista
Ruto ta neman shugabancin kasar nan da shekara biyu masu zuwa, lokacin da Mista
Kenyatta zai sauka daga shugabanci.
Bikin ba da kyautuka na ƙabilar Oromo ya gudana cikin sabon salo
‘Yan ƙabilar Oroma da ke ƙasar Habasha sun gudanar da bikin mika kyautuka na shekara-shekara da suka saba yi, cikin wani yanayin tsaro
saboda fargabar barkewar rikicin siyasa.
Ba kamar
shekarun baya ba, a wannan shekarar daruruwan mutane ne suka halarci taron,
wanda ake kira Irrecha, da aka saba gudanarwa a Addis Ababa babban birinin
kasar da kuma birnin Bishoftu.
Hukumomi
sun ce an rage masu halartar ne saboda gudun kara yaduwar cutar korona.
Gabanin
bikin ‘yan sanda sun ce sun kama daruruwan mutane da suka shirya tayar da
rikicin a yayin bikin.
Zan shirya gagarumar zanga-zanga idan ba a soke SARS ba – Sowore
Asalin hoton, Sowore
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC a Najeriya kuma jagoran gangamin #RevolutionNow, Omoyele Sowore, ya yi barazanar shirya gagarumar zanga-zanga idan ba a rushe rundunar 'yan sanda ta SARS ba.
Sowore ya bayyana hakan ne a martanin da ya mayar wa rundunar 'yan sandan Najeriya game da umarnin da Sufeto Janar ya bayar na haramta wa SARS da sauran rundunoni na musamman kafa shigayen duba ababen hawa a kan tituna.
Mohammed Adamu ya bayar da umarnin ne a yau Lahadi biyo bayan ɓacin rai da 'yan Najeriya suka nuna a shafukan zumunta game da zargin cin zarafi da kashe mutane da suka ce dakarun rundunar SARS na yi.
An kafa SARS ne a ƙarƙashin rundunar 'yan sandan Najeriya domin daƙile laifukan fashi da makami da satar mutane da sauran mugayen laifuka.
"Wannan ɗaya ce daga cikin yaudara domin kawar da hankalin 'yan Najeriya," a cewar Sowore.
"Wajibi ne ku soke SARS a Najeriya baki ɗaya. Babu gudu babu ja da baya. Idan ba haka ba kuma za mu yi wa dukkanin ofisoshin 'yan sanda tsinke na jiha da tarayya baki ɗaya."
Dubban 'yan Najeriya ne suka hau shafukan sada zumunta tun daga daren Asabar domin nuna bacin ransu da kuma yin kiran da a kawo ƙarshen ayyukan SARS.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Wizkid ya caccaki Buhari kan 'yan sandan SARS
Asalin hoton, Twitter/Wizkid
Tauraron mawaƙin Najeriya Ayo Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari game da saƙon fatan samun sauƙi da ya aika wa Donald Trump na Amurka bayan ya kamu da cutar korona.
Wizkid ya nuna ɓacin ransa ne kan saƙon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter kan rashin lafiyar Trump yayin da 'yan Najeriya ke fafutikar neman kawo ƙarshen rundunar 'yan sanda ta SARS, wadda ake zargi da kisa da kuma cin zarafin 'yan ƙasa.
"Babu ruwanka da Donald Trump," in ji Wizkid yayin da yake yi wa Buhari martani. "Sars na kashe mutane kullum. Ka ɗauki mataki. Babu abin da ya shafe ka da Amurka. Ka mayar da hankali kan ƙasarka."
Dubban 'yan Najeriya ne suka hau shafukan sada zumuntar tun daga daren Asabar domin nuna bacin ransu da kuma yin kiran a kawo ƙarshen ayyukan rundunar, inda suka riƙa amfani da maudu'ai irinsu #EndSARS da #EndSarsSNow da #EndPoliceBrutality.
Dukkanin maudu'an uku na cikin waɗanda aka fi tattaunawa a kansu a dandalin Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Sufeton 'yan sanda ya umarci SARS su janye daga kan tituna
Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya umarci rundunar SARS da ke yaƙi da 'yan fashi da su janye daga kan tituna a faɗin ƙasar.
Wannan umarni ya biyo bayan kiraye-kirayen da 'yan Najeriya suka shafe daren Asabar da yinin Lahadi suna yi ne na a soke ayyukan rundunar a shafukan sada zumunta.
Mohammed ya kuma umarci dukkanin sauran rundunonin da ke aiki na musamman da su daina kafa shigayen duba ababen hawa a kan tituna.
Rundunonin da umarnin ya shafa sun haɗa da Special Tactical Squad (STS) da Intelligence Response Team
(IRT) da Anti-Cultism Squad.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin 'Yan Sanda Frank Mba ya aike wa manema labarai a yau Lahadi.
Zan ɗauki mataki kan 'yan sandan SARS – Gwamnan Legas
Asalin hoton, Twitter/Sanwo-Olu
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sha alwashin ɗaukar mataki a kan halayyar 'yan sandan rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami a Najeriya da 'yan ƙasar suka daɗe suna kokawa a kai.
A 'yan kwanakin nan, an yaɗa wasu bidiyo da dama a shafukan sada zumunta da ke nuna dakarun rundunar ta Special Anti Robbery Squad na karɓar kudi da kuma harbe mutane.
Dubban 'yan Najeriya ne suka hau shafukan sada zumuntar tun daga daren Asabar domin nuna bacin ransu da kuma yin kiran a kawo ƙarshen ayyukan rundunar, inda suka riƙa amfani da maudu'ai irinsu #EndSARS da #EndSarsSNow da #EndPoliceBrutality.
Dukkanin maudu'an uku na cikin waɗanda aka fi tattaunawa a kansu a dandalin Twitter.
Tuni da ma ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi kiran da a soke ayyukan rundunar bisa zargin aikata kisan babu gaira ba dalili da azabtar da waɗanda ake zargi da laifi.
"Rahotannin yin ƙwace daga mutanen da aka ɗauka domin su kare al'umma abu ne mai tayar da hankali," in ji Sanwo-Olu a wani saƙon Twitter.
"ina tabbatar muku cewa za a ɗauki matakin da ya dace kuma cikin gaggawa."
Duk da cewa Gwamna Sanwo-Olu ya yi alƙawarin ɗaukar mataki, sai dai rundunar tana aiki ne a ƙarƙashin Gwamnatin Tarayyar Najeriya, abin da ke nuna cewa babu tabbaci kan irin matakin da gwamna zai iya ɗauka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Trump ya gode wa magoya bayansa
Shugaban Amurka Donald Trump ya gode wa magoya bayansa da suka taru a ƙofar asibitin da yake jinya.
Magoya bayan nasa sun taru a ƙofar Walter Reed Medical Center ranar Asabar ɗauke da tutar Amurka da huluna masu rubutun Make America Great Again - taken kamfe ɗin Mista Trump.
"Na gode muku sosai," Trump ya wallafa a Twitter a yau Lahadi.
Tun farko Trump ya bayyana a wani bidiyo yana faɗa wa Amurkawa cewa "zan dawo nan gaba kaɗan".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Amsoshin Takardunku: Bambanci tsakanin faɗuwar gaba da ajiyar zuciya
Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon wanda Buhari Muhammad Fagge ya gabatar, ya amsa tambayoyi kan abin da ke jawo ciwon shanyewar ɓarin jiki da kuma bambanci tsakanin faɗuwar gaba da ajiyar zuciya.
Bayanan sautiSaurari shirin ta hanyar latsa hoton da ke sama
Aljeriya ta fatattaki 'yan cirani 1,500 zuwa Nijar
Asalin hoton, Getty Images
Aljeriya ta tasa ƙeyar 'yan cirani 1,500 daga ƙasar zuwa Nijar, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida Kamel Beldjoud.
Ministan ya bayyana haka ranar Alhamis yayin wani taron jam'iyyar National People's Assembly (APN).
Da yake amsa tambayoyi game da hijirar da 'yan ƙasashen sahel ke yi zuwa cikin ƙasarsa, ministan ya ce "Aljeriya ta samar da tsarin yaƙi da gudun hijira ba bisa ƙa'ida ba," kamar yadda shafin kafar levenementniger.com ya ruwaito.
Ya ƙara da cewa: "Muna mutunta yarjejeniyoyi da alƙawura da muka saka wa hannu da suka shafi mutunta 'yancin ɗan Adam.
"Mun yi bakin ƙoƙarimmu wurin ganin cewa mun kare muradun ƙasarmu da kuma alaƙar da ke tsakanimmu da maƙwabtan ƙasashe."
A ƙarshe, ministan ya ce 'yan ƙasashe 44 abin ya shafa, waɗanda akasarinsu suka shiga ƙasar daga Nijar ta iyakar kudanci.
Saura kwana ɗaya a rufe kasuwar sayen 'yan ƙwallo
Bayan shafe mako 10 na jita-jita a kasuwar saye da musayar 'yan wasan ƙwallon ƙafa, har yanzu akwai ciniki masu ɗaukar hankali da ba a kammala ba yayin da za a rufe kasuwar a daren gobe Litinin.
Annobar korona ta hana manyan ƙungiyoyi kashe kuɗi duk da cewa wasu sun samu damar yin hakan.
A hukumance, za a rufe kasuwar da ƙarfe 11:00 na daren Litinin (agogon Najeriya), 5 ga watan Oktoba. Sai dai kasuwar za ta ci gaba da ci a tsakanin ƙungiyoyin da ke Ingila har zuwa 16 ga Oktoba.
Daga cikin manyan 'yan wasan da ake ganin har yanzu za su iya motsawa akwai:
Jadon Sancho mai shekara 20 daga Borussia Dortmund, wanda Manchester United ke nema
Dele Alli mai shekara 24 daga Tottenham Hotspur, wanda Paris St-Germain ke nema
Wilfried Zaha mai shekara 27 daga Crystal Palace, wanda ake alaƙantawa da Arsenal da Everton
Mesut Ozil mai shekara 31 daga Arsenal: Ana alaƙanta shi da Fenerbahce ta Turkiyya
Buɗe Makarantu: Gwamnan Kwara ya nome ciyawa a sakandare
Asalin hoton, KSG
Gwamnan Jihar Kwara - da ke tsakiyar Najeriya - AbdulRahman AbdulRazaq ya jagoranci sauran jami'an gwamnati domin girbe ciyawa a makarantar sakandare ta Mount Carmel College jiya Asabar a Ilorin, babban birnin jihar.
A gobe Litinin ne za a koma makarantu a faɗin jihar domin fara sabuwar shekarar karatu ta 2020/2021.
Gwamnan ya ce ya aikata hakan ne domin ya ƙarfafa gwiwar mazauna jihar wurin kula da ma'aikatun gwamnati da ke yankunansu.
Daga cikin waɗanda suka yi masa rakiya akwai jagoran Majalisar Dokokin Jihar, Magaji Olawoyin da kuma shugaban kwamitin mahalli, AbdulRazaq Jiddah.
Asalin hoton, KSG
Daga nan sai gwamnan ya zagaya harabar makarantar, wadda ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan ta shafa.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar ta umarci shugabannin makarantu da kuma makarantu masu zaman kansu da kar su karɓi kuɗin zangon karatu na uku daga hannun iyayen yara.
Kwamishinar Ilimi Hajia Fatimah Bisola Ahmed ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar ya fitar, tana mai cewa sabuwar shekarar karatu za ta fara ne daga gobe Litinin, 5 ga watan Oktoba.
An dai rufe makarantu a Najeriya yayin da ake tsaka da karatu tun a watan Maris a yunƙurin mahukunta na daƙile yaɗuwar annobar cutar korona.
An ci gaba da aikin Umara a Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta amince 'yan ƙasarta da ma 'yan kasanshen waje su fara aiwatar da ibadar Umara a bana bayan wata bakwai da rufe harkokin ibadar saboda annobar korona.
Za a bai wa maniyyata dubu shida damar shiga Masallacin Harami da ke birnin Makka a kashin farko a yau Lahadi.
Za a buƙaci mutane su sanya takunkumi sannan su kiyaye sharaɗin nesa-nesa da juna.
Asalin hoton, Haramain Sharifain
Wakilin BBC ya ce hukumomin Saudiyyar sun tsara bai wa maniyyatan damar yin ibada ne a rukuni huɗu, yayin da za a fara da mutum 6,000 ranar Lahadi.
Adadin zai ci gaba da ƙaruwa a kwanaki masu zuwa har zuwa lokacin da masallacin zai cika.
Za a riƙa yin feshin kashe ƙwayoyin cutuka sau 10 a kullum a masallacin na harami.
A farkon watan Nuwamba ne ake sa ran Saudiyya za ta buɗe ƙofofinta ga maniyyata 'yan ƙasashen wajen domin shiga ƙasar don yin ibadar ta Umara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƙarin mutum 160 ne suka kamu da korona a Najeriya
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 59,287 bayan da aka gano ƙarin mutum 160 da suka kamu da cutar ranar Asabar.
A cewar NCDC, adadin mamatan da cutar ta kashe ya zuwa yanzu ya kai 1,113.
Kazalika an samu karin wadanda suka warke daga cutar a ranar Asabar, abin da ya sa jumullar yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 50,718.
A ranar ta Asabar, Jihar Rivers ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar inda aka samu mutum 42, sai kuma Legas da mutum 32.
Jihar Filato na da mutum 21, sai Abuja Babban Birnin Tarayyar Najeriya mai mutum 18, da Kaduna mai mutum 14.
Ogun na da mutum 11, Katsina mutum 10, yayin da jihohin Kwara da Ondo da kuma Imo na ke da mutum 3-3 a kowacce jiha da suka kamu.
Anambra da Abia da kuma Oyo na da mutum 1-1 da suka kamu kowaccensu.
Assalamu Alaikum
Fatan masu bibiyarmu sun tashi lafiya. Umar Mikail ke muku barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye daga sassan duniya.
Amma za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta.