INEC ta yi ƙarin rumfunan zaɓe 753 a Osun gabannin zaɓen jihar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu don samun wasu sabbi.

    Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. WAFCON 2022: Yadda 'yan wasan tawagar Super Fancons ke atisaye a Moroko

    Bayanan bidiyo, Gasar kwallon mata: 2022

    Tawagar Super Falcons ta Nageriya za ta buga wasan farko da Afirka ta Kudu ranar Litinin a gasar kofin Afirka da Morocco ke karbar bakunci.

    Najeriya, wadda ke rike da kofi uku a jere na 11 jimulla, za ta fafata a wasa na 14 da hukumar kwallon kafar Afirka za ta gudanar.

    Falcons tana rukuni na uku da ya hada da Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Botswana da za su kece Stade Moulay, Rabat, Morocco.

  3. Isra'ila ta ce ta daƙile hari da Hezbolah ta kai mata da jirage

    Jirgin Isra'ila

    Israila ta ce ta dakile harin da wasu jiragen sama marasa matuka uku na kungiyar Hezbolah da ke Lebanon wadanda suka so kai wa wata ma'ajiyar iskar gas ta kasar hari.

    Ma'adanar na yankin Karis ne na tekun Baharum, wanda suke takadama a kai tare da Lebanon.

    Rundunar sojon Israila ta ce daya daga cikin jiragen saman yakinta ne ya harbo daya daga cikin jiragen saman, yayin da sauran biyun naurar tare makamai a sama ta kawar da su.

    Sai dai kawo yanzu ba bu wani bayani daga kungiyar ta Hezbolah.

  4. 'Yan sanda na bincike kan zargin satar yara a Jihar Ondo

    Jihar Ondo

    Rundunar 'yan sandan Jihar Ondo a kudancin Najeriya ta ce tana bincike kan rahoton satar wasu yara a yankin Valentino na jihar.

    Rundunar ta faɗa wa BBC Pidgin ranar Asabar cewa matakin ya biyo bayan labarin da suka samu ne game da wani yunƙuri na sace yaran a loƙaci guda a yankin.

    Wani bidiyo da aka yaɗa a dandalin Twitter ya nuna yadda wasu mazauna yankin suka yi wa ofishin 'yan sanda tsinke don neman ƙarin bayani game da lamarin.

    Kakakin 'yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce suna kan bincike kuma ta yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.

    Jihar Kano ma da ke arewacin ƙasar ta daɗe tana fama da sace-sacen yara, abin da ya sa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamati na musamman don ganowa da kuma mayar da yaran da aka sace gida bayan kai su wasu yankuna da kuma sauya musu sunaye a Najeriya.

  5. Hotunan wasu daga cikin maniyatta Aikin Hajji cikin jirgin ƙasa daga Madinah zuwa Makkah

    .
    .
  6. Ana ci gaba da yaƙi a gabashin birnin Lysychansk na Ukraine

    ...

    Ana ci gaba da gwabza yaƙi a kusa da gabashin birnin Lysychansk na Ukraine, wanda shi ne birnin ɗaya da ya rage a yankin Luhansk da ba ya ƙarƙashin ikon Rasha.

    Wani mai magana da yawun rundunar tsaro ta Ukraine Ruslan Muzytchuk, ya musanta iƙirarin da wasu mayaƙa da Rasha ke goyon baya waɗanda ke cewa sun yi wa birnin ƙawanya.

    Hare-haren Rasha sun lalata layukan wutar lantarki da kuma layukan dogo a birnin Kharkiv.

    Babu wani rahoto da ke nuna cewa wani ya mutu.

  7. Hotunan yadda ake shirye-shiryen soma gasar kwallon kafar mata ta nahiyar Afirka

    //
    ..
    ...
  8. Adadin waɗanda zaftarewar ƙasa ta halaka a India ya kai 24

    .

    Hukumomi a arewa maso gabashin India sun bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon zaftarewar ƙasa wadda ruwan sama mai ƙarfi ta haddasa ya ƙaru zuwa 24.

    Wani sashe na wani tsauni ne ya yanko kan wani sansani na wucin gadi wanda aka yi domin ma'aikatan da ke ginin layin dogo a Jihar Manipur.

    Cikin waɗanda suka rasu har da sojoji 18. Sama da mutum 40 ne har yanzu ba a gani ba .

    Masu aikin ceto na ci gaba da haƙa rami da tona taɓo domin gano ko akwai masu rai da suka maƙale.

  9. Shin me ya hana cike gurbin ma’aikata a gwamnatin tarayyar Najeriya?

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren wannan shirin
  10. Kamfanin Google zai bayar da kariya ga masu son zubar da ciki a Amurka

    ..

    Kamfanin fasaha na Google, ya sanar da cewa zai goge bayanan da suka nuna wani daga cikin abokan hulɗarsa ya ziyarci asibitin zubar ciki, a daidai lokacin da ake fargaba kan hukuncin haramcin zubar da ciki da Kotun Kolin Amurka ta zartar.

    Shugaba Joe Biden ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta ɗauki matakin kare hakkin ƴancin mata idan jihohin Amurka suka ki amincewa da su yi balaguron zuwa zubar da ciki.

    Sai dai ana ganin babu wani abun a zo a gani da shugaba Biden zai yi kan wanna batun, watakila batun ya koma kamar na siyasa, ta yiwu a sanya shi cikin zaben tsakiyar wa'adi da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

  11. An kama ƙarin mutum biyu kan kisan telan da ya goyi bayan saɓo

    ..

    Ƴan sanda a arewacin jihar Rajasthan sun ce sun kama ƙarin mutum biyu da ke da alaƙa da kashe wani tela mai bin addinin Hindu, lamarin da ya janyo rikicin ƙabilanci.

    An kashe Kanhaiya Lal a shagonsa da ke birnin Udaipur a ranar Alhamis.

    Tun a baya dai ƴan sanda sun kama wasu Musulmai biyu sa'o'i kaɗan bayan harin. A wani bidiyo, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya ce an far wa telan ne sakamakon ya goyi bayan wasu kalaman ɓatanci da aka yi wa Annabi Muhammad (SAW, kalaman da wata tsohuwar jami'ar ƙasar yar jam'iar BJP ta yi.

  12. Ra'ayi Riga: Kamun ludayin gwamnatin Najeriya dangane da samar da tsaro

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren shirin
  13. INEC ta yi ƙarin rumfunan zaɓe 753 a Osun gabannin zaɓen jihar

    .

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta na Najeriya INEC ta ce an ƙara adadin rumfunan zaɓen da za a yi amfani da su a lokacin zaɓen gwamnan Jihar Osun.

    A wani saƙo da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce an ƙara adadin rumfunan zaɓen zuwa 3,763 a maimakon 3,010 da ake da su a baya.

    A ranar 16 ga watan Yulin nan ne dai ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

    Cikin waɗanda za su fafata akwai Yusuff Lasun na Labour Party da Akin Ogunbiyi na Accord Party da Gboyega Oyetola na APC Ademola Adeleke na PDP da Omigbodun Akinrinola na SDP.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Yunwa ta kashe yara biyu a Sudan ta Kudu

    ..

    Wasu yara biyu da wani babba ɗaya sun rasu sakamakon yunwa da ta kashe su a Sudan ta Kudu.

    Ma'aikatan agaji sun shaida wa BBC cewa mutuwar da aka samu ba ta rasa nasaba da dakatar da aka yi na kai kayan agaji ƙasar.

    A kwanakin baya ne dai shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya dakatar da raba abinci a wasu sassa na ƙasar saboda ƙarancin kuɗi.

    A watan Yunin da ya wuce, shirin ya ce yana buƙatar dala miliyan 426 domin ci gaba da raba abinci.

    Sai dai ba a samu wannan tallafin ba sakamakon ƙasashen duniya sun fi mayar da hankali kan rikicin da ya zarta na Sudan ta Kudu daga ciki har da yaƙin fda ake yi a Ukraine.

  15. Lafiya Zinariya: Shin me ke janyo warin balaga?

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren wannan shirin
  16. Ukraine na son Turkiyya ta tsare jirgin dakon kayan Rasha mai ɗauke da hatsi

    ...

    Mai gabatar da kara a Ukraine, ya bukaci gwamnatin Turkiyya ta tsare jirgin dakon kayan Rasha, wanda ta yi zargin ya na dauke da hatsin da suka sace daga daga birnin Berdyansk da ke tashar ruwan Baharul Aswad.

    Shafin intanet na dakon kaya ya nuna jirgin Rashar mai suna Zhibek Zholy, yana tashar ruwan Karasu da ke Turkiyya wadda ke yammacin birnin Santambul.

    Sai dai a baya-bayan nan Rasha ta musanta zargin na Ukraine, kan sace abinci nau'in hatsi a yankunan da sojinta suka yi wa kawanya.

    A wani bangaren kuma sojin Rasha sun ci gaba da kai munanan hare-hare a birnin Lysychansk, wanda shi ne kaɗai ke hannun sojin Ukraine a yankin Luhansk.

    Shugaba Volodymyr Zelensky, ya kuma zargi Rasha da ayyukan ta'addanci, bayan harin makamai masu linzamin da ta kai da tsakar dare a birnin Odessa mai tashar ruwa da ya hallaka sama da mutum 20.

  17. Girgizar ƙasa ta kashe mutum biyar da raunta 49 a Iran

    ..

    Aƙalla mutum biyar ne suka rasu, 49 kuma suka samu rauni sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.1 da ta afku a kudancin Iran a safiyar yau Asabar.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an samu jijjiga sau 24 mai ƙarfin maki 6.3 da 6.1 bayan ƙarfe biyu na dare agogon ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyar bajewar ƙauyen Sayeh Khosh da ke lardin Hormozgan.

    Jijjigar da aka samu ta baya-bayan nan ta faru da misalin 8:00 na safe, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito.

    Mai magana da yawun ɓangaren agajin gaggawa na ƙasar, Mojtaba Khaledi ya shaida wa gidan talabijin na ƙasar cewa rabin mutum 49 da suka samu rauni an sallame su daga asibiti.

  18. Masu zanga-zanga a Libya sun afka majalisar ƙasar

    .

    Masu zanga-zanga a Libya sun afka zauren majalisar ƙasar da ke gabashin birnin Tobruk kuma rahotanni na cewa sun cinna wa wani sashe na ginin majalisar wuta.

    Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi mai kauri ke tashi a saman wurin da kuma yadda masu zanga-zangar ke ƙona tayoyi.

    Ana ta gudanar da tattaki a sauran biranen ƙasar sakamakon ɗaukewar wutar lantarki da ake samu da tashin farashin kayayyaki da kuma rashin cimma matsaya a siyasar ƙasar.

    Libya dai na cikin rikici tun bayan tarzomar da ƙungiyar Nato ta goyi baya a 2011 ta yi sanadin hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi.

  19. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Jama'a barkanmu da safiyar Asabar, 02 ga watan Yulin 2022. A yau ma za m uc igaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.