Sai da safenku
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye.
Sai kuma gobe za mu kawo wasu sabbi. Kafin nan, ku duba ƙasa don karanta rahotannin da muka kawo a yau Lahadi.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Mustapha Musa Kaita and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye.
Sai kuma gobe za mu kawo wasu sabbi. Kafin nan, ku duba ƙasa don karanta rahotannin da muka kawo a yau Lahadi.

Asalin hoton, EPA
'Yan sanda a Denmark sun ce an kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata a harbe-harbe da aka yi a wani rukunin kantunan da ke Copenhagen babban birnin kasar.
Ba a san manufar dan bindigar ba wanda 'yan sanda suka ce dan asalin kasar ne.
Wadanda suka shaida lamarin sun yi magana kan hargitsin da aka shiga lokacin da aka ji karar harben-harben bindiga a rukunin kantuna na Fields Mall da ke gabashin birnin.

Asalin hoton, NAHCON
Hukumar alhazai ta Najeriya ta jaddada cewa tana da ƙwarin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage a ƙasa yayin da ake shirin rufe jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a daren yau Lahadi.
Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na alhazan Najeriya.
Daga ƙarfe 12:00 na daren yau Lahadi wa'adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu ƙarin awanni na ci gaba da aikin.
Yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Lahadi, NAHCON ta ce tana da ƙwarin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.

Asalin hoton, Other
An yi jana'izar Nura Mustapha Waye, daraktan fim in Izzar So mai dogon zango da ake nunawa a dandalin Youtube.
An gudanar da jana'izar ce a unguwarsu ta Goron Dutse da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.
Sanarwar rasuwarsa a safiyar yau Lahadi ta bai wa mutane mamaki saboda ba a san shi da wata rashin lafiya ba kuma lafiya kalau aka rabu da shi, kamar yadda makusantansa suka bayyana.
Nura ya kasance daraktan fina-finai da dama ciki har da Izzar So, wanda ke jan hankalin masu kallo musamman matasa a shafukan sada zumunta.
Tuni wasu daga cikin taurarin Kannywood suka yi ta'aziyya ga Nura, suna mai bayyana shi a matsayin mutumin kirki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Rasha ta ce yanzu haka ita ce ke da cikakken iko kan birnin Lysychansk da ke gabashin Ukraine, iƙirarin da Ukraine ɗin ba ta tabbatar ba zuwa yanzu.
Ministan Tsaro na Rasha Sergei Shoigu ya faɗa wa Shugaban Ƙasar Vladmir Putin cewa dakarunsa sun ƙwace yankin Luhansk baki ɗayansa.
Tun da farko, shugaban yankin Chechnya mai zaman kansa, Ramzan Kadyrov, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna mayaƙan gwamnatin yankin a tsakiyar birnin na Lysychansk.
A can yammaci kuma, an ci gaba da luguden wuta a kan garin Slovyansk, har ma an kashe mutum aƙalla shida.
Yankunan Donetsk da Luhansk ake kira Donbas mai ma'aikatu.

Asalin hoton, FRSC
Mutum aƙalla 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan na Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Lahadi.
Mai magana da yauwn hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa a Najeriya, Bisi Kazeem, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:20 na dare a ranar Asabar a kusa da Gadar Isara, inda hatsarin ya ritsa da mutum 25.
Mista Kazeem ya ƙara da cewa gudun wuce kima da kuma karya ƙa'idojin tuƙi ne suka haddasa hatsarin da ya jawo mutuwar mutanen.
Mutum shida daga cikin 25 ɗin maza ne, da mace ɗaya, sai kuma yaro namiji ɗaya. Sai dai kuma ba a iya tantance sauran mutum 17 ba.
Karo da motocin suka yi ya haifar da fashewa da tashin gobara, inda ya ƙunshi motoci uku, a cewar sanarwar da Mista Kazeem ya saka wa hannu.

Asalin hoton, Peter Obi
Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa haƙuri da ra'ayoyi mabambanta na ƴan Najeriya don kada hakan ya hana yin maja da wasu jam'iyyu a nan gaba.
Mista Obi ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gode wa magoya bayan nasa dangane da irin haɗin kan da suke ba shi.
Jan kunnen nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa yunurinsu na yin haɗaka da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai yi nasara ba saboda sun kasa daddalewa kan wanda za a mara wa baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa duk da an san halin da ake ciki a Najeriya na fushi da takaici, "ya zama wajibi a yi amfani da kuzarin da ake da shi wurin samun goyon bayan wasu da kuma haɗin kai".
Obi ya yi kalaman ne bayan Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai iya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2023.
Waɗannan kalamai na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda magoyan Obi suka dinga sukarsa da kalamai marasa daɗin ji.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Nura Mustapha
Darakta a masana'antar fina-finan Kannywood Nura Mustapha Waye ya rasu.
An sanar da rasuwarsa a safiyar yau Lahadi bayan an wayi gari an ga ya rasu.
Nura dai ya kasance daraktan fina-finai da dama ciki har da shirin nan mai dogon zango na Izzar So.
Tuni dai wasu daga cikin jaruman Kannywood suka soma yin ta'aziyya ga Nura inda suka yi addu'ar Allah ya yi masa gafara.

Asalin hoton, Reuters
Ɗaruruwan mutane ne suka taru a Khartoum babban birnin Sudan a rana ta huɗu domin gudanar da zanga-zanga kan mulkin da sojoji suke yi a ƙasar.
A ranar Alhamis, an kashe masu zanga-zanga tara a yayin da suka yi arangama da jami'an tsaro - wanda wannan shi ne lamarin da ya fi ƙazanta da ya faru a ƙasar tsawon watanni.
Ko a jiya Asabar sai da hukumomin ƙasar suka rufe wata gada da ta bi ta kan Kogin Nilu domin hana waɗanda ke ƙoƙarin tattaki cikin Khartoum.
Masu gagwarmaya na ta shirya tattaki a cikin birnin da sauran biranen ƙasar inda suke neman a dawo da mulkin dimokraɗiyya ƙasar.
Sama da mutum 100 ne dai aka kashe tun bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar a Oktobar bara.

Gwamnatin Sri Lanka ta ce makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe ƙarin mako guda sakamakon ƙarancin man fetur ɗin da ya addabi ƙasar.
Ma'aikatar ilimi ta ƙasar ta ce za a gudanar da ƙarin darusa a lokacin hutu mai zuwa domin maye gurbin waɗanda za a tsallake.
Tun da farko dai an rufe makarantun ƙasar ne na mako biyu a daidai lokacin da ƙasar Sri Lanka fetur ɗinta ya kusan yin ƙarƙaf.
Sri Lanka dai na ta gwagwarmayar shigar da abinci ƙasar da man fetur da kuma magunguna sakamakon yadda darajar kuɗin ke ƙara shan wuya a kasuwar duniya.

Dakarun Rasha sun yi wa birnin Lysychansk da ke gabashin Ukraine ƙawanya, wanda shi ne birni na ƙarshe da dakarun Ukraine ke da ƙarfin iko da shi a yankin Luhansk.
Kamfanin dillancin labarai na TASS ne ya ruwaito ministan tsaro na Rasha yana bayyana hakan, sai dai sojojin Ukraine ba su ce komai ba dangane da wannan lamari.
A birnin ne ƴan awaren da Rasha ke goyon baya ke gwabza yaƙi da Kyiv tun baya da rasha ta soma kutse cikin Ukraine a 2014.

Asalin hoton, Reuters
Ministan tattalin arziki na Argentina, Martin Guzman, ya yi murabus, sakamakon ɓarakar da ta kunno kai a gwamnatin haɗaka, kan yadda ake tafiyar da matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da ita.
A watan Maris da ya wuce, Mista Guzman, ya cimma yarjejeniya da asusun bada lamuni na duniya IMF kan biyan makudan bashin da ake bin kasar, dala biliyan 44, hakan na nufin za a rage kuɗaɗen da ake kashewa wanda daman Argentina na fama da matsalar.
Amma a lokacin mataimakiyar shugaban kasa mai karfin fada aji Cristina Fernandez de Kirchner ta ki amincewa da hakan tana son kara kashe kudi domin magance talauci.
A wata wasika da ya aike wa shugaba Alberto Fernandez, Mista Guzman ya ce wanda zai gaje shi ya na bukatar hadin kan daukacin gwamnati.

Asalin hoton, VVGLADKOV
Aƙalla mutum uku ne suka mutu sanadiyyar wata fashewa a birnin Belgorod da ke kan iyakar Rasha da Ukraine, kamar yadda gwamnan lardin Vyacheslav Gladkov ya sanar.
Gwamnan yankin a cikin sanarwar ya ce fashewar ta shafi wasu gungun gidajen 11 da kuma wasu gidajen tsirarun al'umma aƙalla 39.
Ya kara da cewa fashewar ta kuma ankarar da na'urar kariya daga hare-hare ta samaniya.
Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tantance sahihancin bayanan gwamnan, kuma ya zuwa yanzu babu wani martani daga Ukraine.
Gwamnan dai ya wallafa bayanin ne a shafinsa na mahajar aikewa da sakonni ta telegram.
Dubban fararen hula da sojoji ne dai suka rasa rayukansu tun bayan Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine da sunan kwance mata damara da kuma kawar da masu akidar NAZI.
Haka nan kuma akalla mutum miliyan 12 suka bar gidajensu sanadiyyar mamayar.
Kasashen yamma dai sun mayar da martani ta hanyar bai wa Ukraine gudumawar makamai da kakaba wa Rasha takunkumi, wadda jigo ce wurin samar da makamashi a duniya kuma mai karfin nukiliya.

Asalin hoton, Twitter
A yau Lahadi za a gudanar da taron koli na kasashen ƙungiyar ECOWAS a birnin Accra na Ghana.
Shugabannin ƙasashen za su tattauna kan batun sake ƙaƙaba wa ƙasashen Mali, da Burkina Faso da Guinea takunkumi kan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.
Tuni ƙungiyar ta dakatar da su daga cikinta. Mali wadda ta fuskanci tashin hankali sama da shekara 10, ta fi ko wa jin jiki kan takunkumin tattalin arziki da ECOWAS ta sanya mata a watan Janairu lokacin taron kolin da aka yi.
Guinea da Burkina Faso kuwa an yi musu gargaɗi matukar suka gaza miƙa mulki salin-alin ga gwamnatin farar hula, to za su ɗanɗana kudarsu ta hanyar lafta musu takunkumi.
Jama'a barkanmu da safiyar Lahadi, 03 ga watan Yulin 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.