Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh and Mustapha Musa Kaita
Sai da safe
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku
labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko
kuma na Instagram domin
bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a
kai.
Sebastien Haller ya koma Borussia Dortmund
Asalin hoton, Bundesliga
Sebastien Haller ya koma Borussia Dortmund daga Ajax kan kwantiragin kaka hudu.
Dan wasan ya ci kwallo 21 a babbar gasar kasar Netherlands da Ajax ta lashe a kakar 2021/22, kuma shi ne na uku a jerin wadanda suka ci kwallaye a Champions League mai 11, bayan Karim Benzema mai 15 da Robert Lewandowski mai 13.
Mai shekara 28 zai buga wasa karo na biyu a Bundesliga, bayan da ya ci kwallo 33 a Eintracht Frankfurt tsakanin 2017 zuwa 2019.
Labarai da dumi-dumi, ISWAP ta ɗauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje
Asalin hoton, Other
Ƙungiyar ISWAP da ke iƙirarin jihadi a Yammacin Afrika ta ɗauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
A wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a wani shafin intanet da ƙungiyar ta saba yaɗa farfaganda, ƙungiyar ta ce ta saki fursunoni da dama.
Hukumomin Najeriya dai sun ce akwai fursunoni sama da 400 da har yanzu ba a gansu ba tun bayan harin da aka kai gidan yarin.
Ukraine tana binciken laifukan yaki da ake zargin sojojin Rasha da aikatawa - Iryna Venediktova
Asalin hoton, Iryna Venediktova
Babbar
mai shigar da kara a Ukraine, Iryna Venediktova ta shaida wa BBC cewa tana
binciken sama da laifukan yaki 21,000 da ake zargin an aikata tun
bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.
Ta
ce ofishinta na karbar rahotannin laifukan yaki 200 zuwa 300 a kowace rana wanda
ake zargin an aikata.
Ms Venediktova
ta ce za a yi yawancin shari’o’i ne a bayan masu laifin, amma akwai alamar
tambaya ko za a yi adalci, kafin ci gaba da sauraron karar.
Ta kuma ce sojojin Rasha
da suka kashe tare da azabtarwa da kuma yi wa fararen hula fyade, nan ba da
jimawa ba za a gabatar da laifukan su a gaban kotu.
Iran za ta hana matan kasar da suka ki sanya hijabi shiga jirgin kasa
Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Iran ta ce za ta hana duk matar da ta ki sanya hijabi daga amfani da jirgin kasa a birnin Mashhad.
Wannan na zuwa ne bayan da wani farmaki da wasu da suka kira kansu da 'yan sanda suka yi, inda suka bai wa mata umarnin rufe kansu ko su fuskanci hukunci.
A wata tattaunawa da shugaban kasar, Ebrahim Raisi ya yi da jami'an gwamnati, ya kwatanta kin amfani da dokokin hijabi a matsayin ''yunkurin goyon baya ga cin hanci tsakanin al'ummar musulmi.''
Kalamansa na zuwa ne bayan wani gargadi da aka yi wa mata ma'aikata a lardin Fars na ko su saka hijabi ko a mayar da su gida ba tare da biyan su ba.
Saudiyya ta tanadi jiragen kasa domin jigilar Mahajjata
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Jiragen wadanda aka sanya wa suna Haramain za su taimaka wa Mahajjatan isa muhimman wurare
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Saudiyya ta kammala shirya jiragen da za su yi jigilar mahajjata daga Minna zuwa Dutsen Arafat a shirye-shiyen Aikin Hajjin bana.
Hukumar dai ta kwashe tsawon watanni tana kula tare da gwajin jiragen, domin tabbatar da lafiya da ingancinsu, don samun damar jigilar mahajjatan zuwa muhimman wuraren da za su ziyarta a yayin aikin hajjin.
Jiragen wadanda aka sanya wa suna Haramain za su taimaka wa Mahajjatan isa muhimman wuraren cikin hanzari da kwanciyar hankali.
Hukumomin tattara bayanan sirri sun ba ni kunya – Buhari
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu ya bayyana cewa hukumomin tattara bayanan sirri na ƙasar sun ba shi kunya bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata da dare.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai gidan yarin a ranar Laraba, kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
"Hukumomin tattara bayanan sirri sun ba ni kunya. Ta yaya ƴan ta'adda za su shirya, su ɗauki makamai su kai hari ga wurin da jami'an tsaro suke kuma su gudu?"
Shugaban ya shafe kusan minti 30 a gidan yarin kuma ya yi tambayoyi da dama.
"Ta yaya jami'an tsaron da ke gidan yarin suka gaza daƙile harin? Fursunoni nawa ne a ciki? Guda nawa ne za a iya bayar da bayaninsu? Jami'ai nawa ne ke aiki lokacin da lamarin ya faru? Nawa ne ke ɗauke da makami?
"Masu gadin gidan yarin sun hau kan hasumiya? Shin kemarar tsaro tana aiki?" Duka waɗannan tambayoyin shugaban ya yi su a gidan yarin.
Bayan haka shugaban ya ce yana buƙatar a kai masa cikakken bayani kan yadda wannan lamarin ya faru.
Hotunan yadda aka gudanar da jana'izar Babban Sakataren OPEC, Sanusi Barkindo
A yau aka gudanar da jana'izar Babban Sakataren Kungiyar OPEC, Dakta Muhammad Sanusi Barkindo wanda ya rasu a ranar Talata da dare.
An gudanar da jana'izar ne a birnin Yola da ke Jihar Adamawa
Asalin hoton, Salis Lawal
Asalin hoton, Salis Lawal
Asalin hoton, Salis Lawal
Buhari ya ziyarci gidan yarin Kuje
Asalin hoton, NGR presidency
Bayanan hoto, Kawo yanzu babu cikakken bayani kan abubuwan da ya yi a ziyarar da ya kai gidan yarin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin kasar bayan harin da aka kai kurkukun ranar Talata da daddare.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan abubuwan da ya yi a ziyarar da ya kai gidan yarin.
Sai dai hukumomi sun bayyana cewa 879 ne suka tsere daga gidan yarin, bayan mutanen da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kai masa hari.
Sanarwar da mai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.
Ministan tsaron kasar ya ce akwai yiwuwar mayakan kungiyar Boko Haram 64 ne suka tsare daga gidan yarin.
Harin dai na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da 'yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura.
Za mu afka wa Rwanda da yaki - Shugaban DR Kongo
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Sojojin DR Kongo
Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Félix Tshisekedi ya yi gargadin cewa kasarsa za ta iya far wa makwabciyarta Rwanda da yaki saboda tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Ya zargi kasar Rwanda da goyon bayan kungiyar 'yan tawaye ta M23.
Mista Tshisekedi na shirin gana wa da takwaransa na Rwanda Paul Kagame a ranar Laraba a Angola.
Mista Tshisekedi ya shaida wa jaridar Financial Times cewa dole Mista Kagame ya fadi gaskiya yayin ganawar tasu, kuma ya yadda cewa gwamnatinsa na goyon bayan kungiyar 'yan tawaye ta M23, wadanda suka durkusar da yankin gabashin kasar mai arzikin ma'adinai.
Mista Kagame dai ya sha musanta wannan zargi, yana mai cewa rigingimun da ke faruwa a kasar abu ne da ya shafi cikin gida, kuma babu hannun Rwanda a ciki.
Yunwa ta kashe yara 10, ta kwantar da 200 a asibitin Habasha
Hukumomi a kudancin Habasha sun ce yara goma sha uku ne suka
mutu sakamakon yunwa yayin da fari da tashe-tashen hankula ke ci gaba da shafar
kasar.
An kuma kwantar
da wasu yara dari biyu da arba'in masu fama da tamowa a asibiti.
Hukumomin agaji
sun ce kasar na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru
da dama bayan an kasa girbin amfanin gona.
Yara miliyan
bakwai ƴan kasa da shekaru biyar na fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki a kasashen gabashin Afrika da suka hadar da ita kanta Habasha da Somalia da kuma Eritiriya.
Jirgin ruwa ya kife da mutum 20 a Legas
Asalin hoton, Reuters
Akalla mutum biyu ne suka mutu, bayan kifewar wani jirgin ruwa a Legas.
An ceto mutum 15 daga 20 da ke cikin jirgin, yayin faruwar lamarin a yankin Victoria Island.
A wata sanarwa da shugaban hukumar kula da sufurin ruwa ta jihar Oluwadamilola Emmanuel, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba.
Ya kara da cewa kawo yanzu ba a kai ga gano fasinjoji uku ba.
Mista Emmanuel ya ce bayan faruwar lamarin jami'an hukumarsa sun garzaya wajen da lamarin ya faru domin kubutar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar hadarin,
Wadanda aka sace a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun yi kwana 100 a hannun ƴan bindiga
Asalin hoton, CHIBUIKEAMAECHI
Yau ne
fasinjojin jirgin kasa da `yan bindiga suka sace a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna
ke cika kwana 100 a hannun maharan.
Fiye da mutum hamsin ne, ake kyautata zaton suna hannun `yan bindigar, ciki
har da mata da kananan yara, kuma tun lokacin da aka sace su mahukunta ke
ikirarin daukar matakan kubutar da su amma har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.
Dangi da abokan arzikin wadanda
aka sacen sun yanke shawarar gudanar da zanga-zangar lumana don jan hankalin
mahukunta game da halin da `yan uwansu ke ciki.
A karshen watan Maris din da ya wuce ne `yan bindigan suka kai hari kann
jirgin kasan, inda suka kashe mutum takwas daga cikin fasinjojin da ke ciki
kana suka kama mutane da dama suka tafi da su. Kodayake daga baya sun saki wasu
bisa dalilai na jinkai kamar yadda `yan bindigan suka yi ikirari a cikin wani
bidiyo. Amma wasu rahotanni na cewa sun karbi miliyoyin naira kudin fansa.
Buhari ya rantsar da sabbin ministoci
Asalin hoton, BUHARI SALLAU
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministoci bakwai da Majalisar Dokokin ƙasar ta tatance a baya-bayan nan.
Ya rantsar da su ne gabanin taron Majalisar Zartarwar ƙasar na mako-mako yau Laraba.
Ministocin sun hadar da Umana Okon Umana daga jihar Akwa-Ibom a matsayin ministan Naija Delta, da Ikoh Henry Ikechukwu daga jihar Abia a matsayin ƙaramin ministan kimiyya da fasaha, da Umar Ibrahim El-Yakubu daga Kano a matsayin ƙaramin ministan ayyuka da gidaje.
Sauran su ne Goodluck Nanah Opiah daga jihar Imo, wanda ya rabauta da kujerar ƙaramin ministan ilimi, da Ekumankama Joseph Nkamah daga Ebonyi, a matsayin ƙaramin ministan lafiya, da Odum Udi daga Rivers a matsayin ƙaramin ministan muhalli, da Ademola Adewole Adegoroye daga Ondo a matsayin ƙaramin ministan suuri.
Shugaban ya taya su murna, tare da buƙatar su yi aiki tuƙuru don ciyar da ƙasar gaba.
Ina ganin 'yan Boko Haram ne suka kai harin gidan yarin Kuje - Ministan Tsaro
Kimanin Fursunoni 600 ne suka tsere a yayin harin da aka kai kan gidan yarin Kuje ranar Talata da daddare, kamar yadda Ministan Tsaro Bashir Magashi ya tabbatar wa BBC da safiyar yau Laraba.
Daga cikin fursunonin da suka tsere kimanin 300 sun mika kansu ga hukumomi don radin kansu a yayin da jam'an tsaro suka kamo wasu daga cikinsu.
Mimistan dai ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram, saboda a cewarsa akwai kimanin mayakan Boko Haram akalla 64 a gidan yarin.
Magashi ya kuma tabbatar da mutuwar jami'in Civil Defence daya.
Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar jam'in tsaro na Civil Defence daya.
A halin yanzu dai gidan yarin na karkashin ikon hukumomin kasar. Akwai dai a kalla fursunoni 994 a gidan yarin.
Harin na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da 'yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura.
Buhari zai kama hanyar zuwa Senegal
Asalin hoton, FEMI ADESINA
Yau ne shugaban Najeriya Muhamadu Buhari zai kama hanyar zuwa Dakar, babban birnin Senegal, don halartar taron ƙungiyar samar da ci gaban ƙasa da ƙasa ta IDA
Shugaban zai bar Najeriya ne a dai-dai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a ƙasar, inda a ƙasa da awanni 24 aka kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin kasar Abuja, aka kai wa tawagarsa hari a jihar Katsina, sannan kuma aka halaka mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar.
Barka da rana
Bayani kan maƙala
Marubuci, Imam Saleh
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
Masu karatu sannunku da jimirin ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi da muke sanar da ku irin wainar da ake toyawa kai tsaye a fadin duniya.
Nine dai Imam Saleh, sai ku sake gyara zama don mu ci gaba da kasancewa tare!
Labarai da dumi-dumi, Saudiyya ta tsawaita lokacin jigilar maniyyata
Asalin hoton, NAHCON
Hukumomin Saudiyya sun sanar da ƙarin lokacin jigilar alhazai zuwa kasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar aikin hajji na Najeriya ta fitar, ta ce matakin zai kwatar da hankalin aƙalla maniyyatan Najeriya kusan 3000 da suka maƙale.
Ta ce hakan ya biyo bayan doguwar tattaunawa tsakanin Najeriya da Saudiyya, karkashin jagorancin shugaban hukumar Zikrullah Hassan.
Hotuna: Ɓarnar da maharan gidan yarin Kuje suka yi
Bayanan hoto, Wasu mutane da ke tsaye suna tattauna abun da ya faru kenan
Ranar Talata da daddare ne wasu mahara da ba a san ko su wanene ba suka kai farmaki gidan yarin Kuje da ke babban birnin Najerya Abuja, inda bayanai ke cewa daga cikin fursunonin sun tsere.
Wani mutum da BBC ta zanta da shi ya bayyana cewa maharan sun yi ta kabbara tare da harba rokoki a cikin gidan yarin.
A cewar wani da lamarin ya faru a gabansa, 'yan bindigar sun ci karfin jami'an tsaro inda aka yi ta musayar wuta.
BBC ta ziyarci gidan yarin bayan faruwar lamarin, ga kuma hotunan irin ɓarnar da maharan suka yi.
Bayanan hoto, Wata mota da maharan suka banka wa wuta lokacin harin
Bayanan hoto, Wata motar raka fursunoni kenan da ita ma maharan suka ƙona
Bayanan hoto, Bayanai sun ce yanzu haka an jibge ɗumbin jami'an tsaro da dama a gidan yarin
Yadda aka hana shugaban hukumar Alhazan Najeriya tafiya Makka yayin da ɗumbin maniyyata ke watangaririya a filayen jiragen sama
Asalin hoton, NAHCON
An yi ta yaɗa bidiyon wata ƴar hatsaniya da ta faru a filin jirgin saman
Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin Najeriya, lokacin da shugaban hukumar alhazai ta jihar Neja Umar Makun Lapai ya hana shugaban hukumar alhazai ta kasar
NAHCON Zikrullah Hassan hawa jirgi don zuwa kasar Saudiyya.
Umar Makun Lapai ya tabbatar da faruwar lamari, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da
manema labarai daga Minna babban birnin jihar Neja.
Ya ce ba zai iya barin Shugaban Hukumar na kasa ya
tafi aikin hajji ba yayin da kashi hamsin cikin dari na maniyyatan jihar Neja
da sauran jihohin Najeriya ke nan a makale.
Ya ce a matsayinsa na shugaban hukumar alhazai ta
kasa NAHCON, bai kamata Zikrullah Hassan ya kama hanya ya tafi aikin Hajjin yayin
da adadin maniyyata da dama da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya basu
san makomarsu ba a bana.
A cewarsa kamata ya yi a ce shugabanni ne za su
kasance na karshe da za su tafi aikin hajji domin tabbatar da cewa ba a bar
wani maniyyaci a baya ba.