An dawo da dokar hana hawa babur a Jihar Katsina

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Jabir Mustapha Sambo

  1. An daure mai goyon bayan Trump sama da shekara bakwai

    Guy Reffitt
    Bayanan hoto, Kotun ta kuma bukaci a yi masa maganin tabin hankali

    Kotu a Amurka ta daure dan wata kungiyar bata-gari daga jihar Texas, wanda aka same shi da laifin kutse a ginin Majalisar Dokokin Amurka, Capitol, sama da shekara bakwai a gidan yari.

    Hukuncin nasa shi ne mafi tsawo da aka yi wa wani da ke da hannu a tarzomar da aka yi a ginin majalisar a shekarar da ta wuce, inda magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump suka kai hari a yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar.

    Guy Reffitt ya kuma yi barazanar harbe 'ya'yansa idan suka sake suka gaya wa hukumar binciken manyan laifuka ta kasar, FBI a game da shi.

    Shedar bidiyo da aka duba ta nuna yadda Guy Reffitt yake jagorantar masu tarzomar su hau matattakalar benen daga wajen ginin, a wannan rana ta 6 ga watan Janairun 2021.

    Mai shari'ar Dabney Friedrich ta ce kalaman Mista Reffitt da suka nuna yana son hambarar da majalisar abin tayar da hankali ne da ke da nasaba da shifcin gizo.

    Haka kuma ta haramta masa alaka da kungiyoyin bata-gari tare da bayar da umarnin a yi masa maganin tabin hankali.

  2. Ana fargaba kan karewar yarjejeniyar dakatar da bude-wuta a Yemen

    Mayakan Houthi
    Bayanan hoto, A gobe Talata ne yarjejeniyar za ta kare, amma ana rokon da a tsawaita ta

    Manyan kungiyoyin agaji 30, sun bukaci bangarorin da ke yaki da juna a Yemen, su tsawaita wa’adin wucin gadi na dakatar da bude wuta wadda za ta kare a gobe Talata.

    Dakatar da bude wutar watanni biyu da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta, wadda ta fara a watan Afirilu da kuma aka sake sabuntata da karin wata biyu zuwa goben, ba ta wadatar ba a cewar kungiyoyin.

    Rahotanni sun ce kungiyoin agajin ciki har da Oxfam, da Islamic Relief da Save the Children, sun bayyana dakatar da bude wutar da cewa ita ce mafi tsawo tun bayan barkewar yakin basasa a Yemen.

    Mayar da jigilar jiragen sama a birnin Sanaa da ke hannun 'yan tawaye ta bayar da damar kai sama da mutum 8000 asibiti domin ba su kulawar gaggawa.

  3. Duniya na dab da hadarin wargajewa saboda makaman nukiliya - MDD

    Antonio Guterres
    Bayanan hoto, Mista Guterres ya yi gargadin duniya na daf da fadawa yakin nukiliya

    Shugaban majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa duniya na fuskantar gagarumin hadarin makaman nukiliya fiye da kowa ne lokaci tun bayan yakin cacar-baka.

    Antonio Guterres ya yi wannan gargadi ne a New York, inda ya bukaci shugabanni da su karfafa yarjejeniyar hana bazuwar makaman na kare-dangi.

    Babban Sakataren ya ce a yanzu kiris ya rage wa duniya ta rushe gaba daya, inda take bakin hadarin wargazata ta makamin nukiliya.

    Haka shi ma Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya maimaita wannan gargadi a kan Koriya ta Arewa da kuma burin Iran na mallakar makaman nukiliya.

    Shi kuwa shugaban Rasha Vladimir Putin, ya aika da wasika ne wadda a ciki ya ke jaddada cewa gwamnatinsa tana kan alkawarinta na mutunta yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya.

    Mista Putin ya ce babu wanda zai yi nasara a yakin nukiliya.

  4. Ana zargin 'yan-sintiri da kashe malamin makarantar allo a Jihar Kano

    Sufeto Janar na Najeriya Usman Alkali Baba

    Ana zargin 'yan kungiyar sintiri (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

    Shi dai Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Qur'ani ne a unguwar, inda yake da daruruwan almajirai.

    Ana zargin 'yan kungiyar sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro.

    Jaridar Premium Times ta intanet ta ruwaito cewa dan malamin, Ibrahim ya sheda mata cewa, ''Mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola.

    Sai ya je ya dauki yaron, sai kawai wata mata ta yi masa ihu, tana ce masa barawon yaro.''

    ''Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo 'yan kungiyar sintirin da sauran jama'ar unguwar wadanda suka rufe shi da duka,'' in ji dan.

    Ya kara da cewa, ''Daga nan sai suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Daga baya ya fadi ya suma.''

    Ya ce,'' Bayan da wasu 'yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda ya cika a hanya.''

    Dan malamin ya sheda wa jaridar cewa 'yan-sanda sun kama shugaban 'yan-sintirin na unguwar, mai suna Munkaila, inda ake bincikensa a caji ofis na Rijiyar Zaki.

  5. An dawo da dokar hana hawa babur a Jihar Katsina

    Mutane a kan babur

    Rundunar 'yan-sandan jihar Katsina ta Najeriya ta sanar da dawo da dokar hana amfani da babur a fadin jihar.

    Rundunar ta bayyana hakan ne wata hudu bayan da gwamnatin jihar ta dage dokar ta dan wani lokaci domin bayar da dama ga jama'a su sarara a lokacin azumi.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar Gambo Isah, ya fitar ya ce an sake dawo da dokar ne sakamakon karuwar hare-hare da barazanar 'yan ta'adda da sauran miyagu wadanda ke amfani da babura.

    Dokar ta hana amfani da babura daga karfe goma na dare zuwa shida na safe a cikin birnin Katsina. Su kuwa kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaron sosai dokar na farawa ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

    Jihar Katsina kamar sauran jihohi da dama na yankin arewa maso yamma da kuma wasu sassan na arewa masu tsakiya suna fama da matsalar hare-haren barayin daji.

    Hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallinsu.

  6. An kwantar da tsohon jami'in Rasha mai adawa da yakin Ukraine a asibiti magashiyan

    Anatoly Chubais
    Bayanan hoto, Ana zargin guba aka sanya wa tsohon wakilin na Shugaban Rasha

    An kwantar da daya daga cikin manyan masu adawa da yakin da Rasha take yi da Ukraine, a wani asibiti inda ya ke cikin halin rai-kwa-kwai-mutu-kwa-kwai.

    Anatoly Chubais wakili na musamman ne ga Shugaba Vladimir Putin, amma ya yi murabus a watan Maris tare da nuna kin amincewa da mamayar Ukraine.

    Bayanai sun nuna cewa tun bayan samun labarin rashin lafiyar daya daga cikin mai adawa da fadar ta Kremlin, ake ta yada jita-jitar guba aka sanya wa Mr Chubais.

    Haka kuma an samu labarin mutuwar wani dan Rasha da ya tsere daga kasar kan batun mamayar Ukraine.

    Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dimitry Peskov, ya ce suna yi wa Mr Chubais fatan samun lafiya.

  7. Likitoci a nisan duniya sun hadu ta kwamfuta suka raba tagwaye da ke manne ta kwakwalwa

    Yara manne
    Bayanan hoto, A tiyatar karshe kadai ma'aikata sama da 100 sun shafe sama da sa'a 27 suna aikin

    Likitoci sun yi nasarar raba wasu tagwaye 'yan shekara uku 'yan kasar Brazil da suke manne ta kai ta hanyar amfani da siddabarun kwanfuta.

    Likitoci sun yi wa Bernardo da Arthur Lima, wadanda aka haifa da kwakwalwa a hade tiyata har guda bakwai a birnin Rio de Janeiro, ta hanyar karbar umarni daga wasu kwararrun likitocin da ke nisan duniya a asibitin Great Ormond Street Hospital da ke birnin London.

    Kwararrun likitocin a Brazil da Birtaniya sun shafe watanni suna gwajin yadda za su yi amfani da fasahar (virtual realiy) wajen yi wa tagwayen tiyata.

    Yaran bayan aikin

    Kungiyar da ta dauki nauyin aikin raba yaran, Gemini Untwined ta ce tiyatar na daya daga cikin irinta mafiya wahala da sarkakiya da aka yi.

    Aikin karshe kadai ya dauki sama da sa'a 27, tare da ma'aikatan lafiya kusan dari daya.

    Likitan da ya kafa kungiyar a 2018, da ta dauki nauyin aikin Noor ul Owase Jeelani ya bayyana shi a matsayin aikin fasaha na sabon zamani.

    Ya ce a karon farko a tarihi likitoci a kasashe biyu sun hadu a lokaci daya ta hanyar fasaha, sanye da na'urori a kansu suka yi amfani da hotunan kwamfuta suka yi tiyata a kan tagwaye.

  8. Gwamnan Kogi ya dakatar da Sarkin Eganyi saboda matsalar tsaro

    Yahaya Bello

    Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar kasar ta dakatar da mai martaba Sarkin Eganyi, Alhaji Musa Isa Achuja daga mukaminsa, sakamakon tabarbarewar tsaro a yankinsa.

    Gwamna Alhaji Yahaya Bello ne ya ba da umurnin dakatar da mai martaba sarkin, wanda aka fi sani da Ohi, daga mukamin nasa, bisa zarginsa da sako-sako da al'amuran da suka shafi tsaro a yankin karamar hukumar Ajaokuta.

    Gwamnan ya dauki matakin dakatar da sarkin ne bayan wani bincike da jami`an tsaro suka yi, wanda aka karshe suka cafke sarkin.

    Kazalika gwamnan ya ba da umurnin a rubuta wasikar tuhuma ga shugaban karamar hukumar Ajaokuta, Honorabul Mustapha Aka`aba domin ya wanke kansa dangane da yadda tsaro ya tabarbare a yankin.

    A ranar Asabar din ta da wuce ne wasu `yan bindiga suka yi wa wasu `yan sanda uku, ciki har da DPO da kuma wasu `yan sa-kai su biyar kwanton-bauna a yankin karamar hukumar Ajakutan, harin da ya yi sanadin mutuwarsu su takwas baki daya.

    A cikin wata sanarwa, wadda mai magana da yawun gwamnan, Mohammed Onogwu ya sanya wa hannu, gwamna Yahaya Bello ya gargadi sarakunan jihar baki daya da su guji hada-baki ko taimaka wa miyagu ta kowace hanya wajen yin aika-aika a jihar, yana cewa gwamnatinsa za ta sa kafar-wando guda da duk mutumin da ke goya wa `yan ta`adda baya, komai girmansa.

    Har wa yau, gwamnan ya haramta wa shugabannin kananan hukumi yin bulaguro zuwa wajen yankunansu ba tare da wani kwakkwaran dalili ba kuma ko da akwai dalili sai sun samu amincewar yin bulaguron.

    A karshen makon da ya wuce al`umomin Jidda-Bassa da karamar hukumar Ajaokuta suka kai kuka wurin DPO, cewa wasu `yan bindiga suna far musu cikin gonakai, suka kwashe musu amfanin gona.

    Daga nan ne shugaban `yan sandan ya hada mutanensa da wasu `yan sa-kai suka bazama domin ceto al`umma, amma sai suka yi rashin sa`a suka fada tarkon `yan bindigan, wadanda suka yi musu kwanton-bauna, suka halaka su.

  9. An gudanar da zanga-zangar kin jinin dakarun MDD a Kongo

    UN

    An gudanar da zanga-zanga a birnin Beni kan kin jinin ayyukan jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

    Gwamman mutane sun shiga zanga-zangar kwana guda, bayan zargin wasu jami’an Majalisar na harbe akalla mutane biyu da jikkata wasu 15 a kan iyakar kasar da Uganda.

    Sai dai Majalisar Dinkin Duniyar ta ce tuni aka cafke jami’an na ta don fuskantar shari'a.

    A bangare guda kuma an gudanar da bikin jana’zar sojojin Majalisar Dinkin Duniyar da ke cikin mutane 20 da aka kashe a makon da ya gabata, lokacin wata tarzoma duk dai kan kosawa da zamansu a Congon.

    Yawancin ‘yan kasar na cewa sojojin sun gaza bai wa farar hula kariyar da suke bukata, daga hare-haren mayakan jihadi da suka addabi kasar.

  10. Gwamnatin Kenya ta ce ba za ta rufe Facebook ba gabanin zabe

    kenya

    Gwamnatin Kenya ta ce ba za ta rufe shafin sada zumunta na Facebook ba, duk da barazanar da hukumar haɗin kan ƙasa ta yi na dakatar da shi.

    A makon jiya hukumar haɗin kai ta ƙasa (NCIC) ta ce ta aika wa Meta, kamfanin da ke da Facebook, sako cewa suna neman a mayar da martani game da zarge-zargen kalaman tunzura jama'a a shafin gabanin zaben da za a yi.

    NCIC ta yi barazanar dakatar da ayyukan kamfanin idan har a cikin kwana bakwai bai bi dokar da aka sa masa ta toshe kalaman kiyayyar da ke yaɗuwa a kasar ba.

    Amma Ministan Fasaha ya nemi karin bayani game da tsarin dokar da NCIC ke amfani da ita domin dakatar da Facebook.

    Shi ma Ministan Harkokin Cikin Gida Fred Matiang'i a wata sanarwa ta daban, ya ce gwamnati ba ta da niyyar rufe kafofin sada zumunta kuma ta nisanta kanta da sanarwar NCIC.

    Sai dai a martanin da Facebook ya mayar, ya ce ya ƙara inganta hanyoyin toshe kalaman kiyayya ko kuma tunzura jama'a musamman lokacin zabe.

  11. NDLEA ta rufe gidan abincin da take zargin ana sayar da kayan maye a Kano

    NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da kama kusan mutum 51 a Kano.

    Hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mutanen ne bayan samun korafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurbata tarbiyar ya'yansu.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai sayar da magungunan jabu zuwa gidan yari na tsawoin shekaru uku, tare da biyan tarar naira 200,000.

    Can ma a birnin Legas da ke Kudancin kasar NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa.

    NDLEA ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da suka hada da nau'ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari uku da saba'in da biyar.

  12. An gurfanar da mutum 82 da zargin fyade a Afrika ta Kudu

    S AFRICA

    Wasu mutum 82 zasu gurfana gaban kotu a Afirka ta Kudu ranar Litinin a kan zargin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, da yunƙurin kisan kai, da mallakar abubuwan fashewa, da kuma wasu laifukan da suka saɓawa dokokin shige da fice.

    Ƴan sanda sun ce wadanda ake zargin basu rasa alaka da zargin aikata fyaɗen taron dangin da a ka yi wa wasu mata takwas a lokacin da suke daukar bidiyon wata waka.

    Lamarin ya faru ne ranar alhamis a Krugersdrop, da ke yammacin Johannesburg.

    Hukumomi sun ce matan da aka yi wa fyaden yan shekaru 19 ne zuwa 37.

    Ɗaya daga cikin waɗanɗa abin ya shafa ta gaya wa wata jarida cewa, mutanen sun zo rataye da barguna da takunkumi a fuska, sannan suka tunkare su suna harba bindiga a sama.

    Ta kara da cewa wani tsoho daga cikin wadanda ake zargin ya bai wa matasan da su yi musu fyaɗe sannan su yi musu sata.

    Lamarin ya sa al'ummar Afirka ta Kudu sun kadu, inda wasu suka nanata kiraye-kirayen yin amfani da sinadarin kashe sha'awa ga wadanda aka kama da laifin aikata fyade.

  13. Ba za mu sake tsawaita wa'adin rajistar katin zabe ba- INEC

    INEC

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ba zata sake bude kofar mallakar katin zabe ba ga yan kasar, bayan cikar wa'adin ranar 31 ga watan Yulin 2022.

    Kwamishinan Hukumar mai kula da sashen ilmantar da al'umma kan mallakar katin, Festus Okoye, ya fada wa BBC cewa sun bai wa jama'a duk irin lokacin da suke bukata don mallakar katin.

    Akan haka yace ba za su sake tsawaita lokacin yankar rajistar ba, lura da yadda lokaci ke kure musu.

    INEC ta ce tana so ta mayar da hankali ne ga sauran ayyukan da ke kan jadawalin zaben na 2023, kuma dole sai ta rufe yankar katin ne za ta iya samun ci gaba.

    A ranar 28 ga watan Yuni ne hukumar zaben ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar zuwa ranar 31 ga watan Yulin 2022, bayan bukatar hakan daga bangarori daban-daban na kasar.

  14. Cutar kyandar biri ta fara kisa a India

    MONKEYFOX

    Hukumomi a Indiya sun tabbatar da mutuwar wani mutum da ya kamu da cutar ƙyandar biri.

    Mutumin mai shekara 22 ya mutu ne ranar Asabar, bayan ya dawo daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

    Hukumomin lafiya a jihar Kerala sun ce an tabbatar da ƙwayar cutar a jikin mutumin bayan mutuwarsa.

    Wannan ne karo na hudu da aka samu mace-mace sanadin cutar a wajen Afrika.

    Yanzu haka an killace mutum 20 da aka tabbatar sun yi hulda da mutumin kai tsaye, da suka hada da wasu da ya buga kwallo da su.

    A watan da ya gabata ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cutar kyandar biri a matsayin cutar da ke bukatar agajin lafiya na gaggawa.

  15. ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu

    Asuu

    Kungiyar Malaman Jami'o'i a Najeriya ta ASUU ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu.

    Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin Najeriya, yanzu kuma gashi ta kara wata daya.

    Idan har aka shafe wasu makonni hudu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban jami'o'in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

    Sanarwar da ASUU ta fitar na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita ne bayan kammala wani zaman gaggaawa na jiga-jigan kungiyar ranar Lahadi a Abuja.

    Hakama ASUU ta gode wa ƙungiyar Kwadago ta NLC, da sauran kungiyoyin da suka mara mata baya wurin yin zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo karshen yajin aikin.

    Kungiyar Malaman Jami'ar ta kara da cewa ta tsawaita yajin aikin ne da mako hudu, lura da cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta nuna wata alama ta kawo karshen zaman daliban a gida ba.

    Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin Najeriya da gaza cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka ƙulla, ciki har da batun inganta rayuwar malaman da kuma dambarwar shigar da kungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi.

  16. An yi jana'izar wani babban limamin Yahudawa a Isra'ila

    Mourners carried the body of Rabbi Weiss through central Jerusalem

    Dubbai ne suka halarci jana'izar Rabbi Weiss, daya daga cikin mashahuran malaman Yahudawa a Isra'ila.

    Weiss ya mutu ne ranar Asabar yana da shekara 95, an kuma rufe shi a makabartar Mount of Olives da ke Jerusalem.

    Ya mutu ne bayan jinya a asibiti, bayan kamuwa da wata ƙwayar cuta da ba a bayyana ba a farkon shekara.

    Rabbi Weiss na daga cikin Yahudawa da ke da tsattsauran ra'ayi kan abun da ya shafi addini, kuma ya yi ta samun rashin jituwa da jami'an tsaro kan haka.

    Weiss, wanda aka haifa a Slovakia na daga cikin daruruwan yahudawa da aka kubutar daga kisan kiyashin Holocaust.

  17. An dawo da dokar hana hawa mashin a jihar Katsina

    MASARI

    Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta tabbatar da haramcin hana hawa mashin a duka fadin jihar.

    Hakan na zuwa watanni hudu bayan da gwamnatin jihar ta dage haramcin na wucin gadi, don sauƙaƙa wa al'umma gudanar da ibadar Azumin watan Ramadana.

    Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce saka dokar ya zama dole lura da yadda a baya bayannan yan ta'adda ke amfani da mashunan wurin kai hare-hare.

    "Ana jan hankalin al'umma cewa an dabbaka dokar hana hawan mashin daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safen kowace rana."

    Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa a jihohin da suka fi fama da hare-hare dokar za ta fara ne daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

    Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya dake fama da hare-haren yan bindiga, da suka addabin yankin, lamarin da ya hada da makwabtanta Kaduna da Zamfara.

  18. Iran ta ce za ta iya ƙera makamin nukiliya

    IRAN

    Shugaban hukumar kula da makamashi ta Iran ya ce sun tara sinadarin da ka iya ƙera makamin ƙare dangi na nukiliya, duk da ba su da niyyar ƙera makamin a yanzu.

    Kalaman Mohammad Eslami sun jaddada na wani babban mai bayar da shawara a ƙasar kan batun.

    Kuma hakan ya jefa shakku kan sanin gaskiyar matakin da Iran take ɗauka wurin tara sinadarin Uranium.

    Dama Iran ta cigaba da tara sinadarin tun bayan da yarjejeniyar da aka kulla da ita ta samu cikas.

    Yarjejeniyar ta 2015 ta fara tangal-tangal, tun bayan da Amurka ta janye kanta, ta kuma tsaurara wa gwamnati a Tehran takunkumi.

    Iran ta sha nanata cewa shirinta na samar da makamashin nukiliya ba shida alaka da kera wani mugun makami, to amma kasashen Yamma da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki basu gamsu da hakan ba.

  19. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta haramta aibata jami'anta a fina-finai

    IGP Nigeria

    Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin dan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.

    IG Usman Baba ya kara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.

    Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.

    Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami'an yan sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.

    Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ta ce "ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ƴan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan sanda."

    Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al'umma.

  20. Ƴan ƙungiyar Taliban sun yi gumurzu da masu gadin iyakar Iran

    The Taliban have in the past clashed with Iranian forces on the border (file picture, February 2022)

    Kungiyar Taliban da ke mulkin Afganistan sun fafata da masu gadin kan iyakar Iran a kan iyakar ƙasashen biyu.

    Mayakan sun ce an kashe daya daga cikinsu a fadan da aka yi a ranar Lahadi a kan iyakar da ke tsakanin lardin Nimroz na Afghanistan da Hirmand na Iran.

    Kowace ƙasa ta ɗora wa ɗayar laifi akan lamarin, wanda shi ne fada na baya-bayan nan da aka yi tun bayan da kungiyar Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan shekara daya da ta wuce.

    A watan da ya gabata, Iran ta ba da rahoton mutuwar daya daga cikin masu gadinta a wani lamari da ya faru a wannan yanki.

    Ba a san hakikanin yanayin fadan na baya-bayan nan ba, amma wani rahoton Iran ya ce an fara harbe-harbe ne a lokacin da kungiyar Taliban suka yi kokarin ɗaga tutarsu a yankunan da ba na Afghanistan ba.

    Rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba a bangaren Iran.