Labaran wasanni da suke gudana a sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da suke gudana a fagen wasanni musamman irin wainar da ake toyawa a duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Wasannin Premier na ranar Lahadi
- Chelsea v West Bromwich Albion
- Manchester United v Tottenham Hotspur
- Southampton v Middlesbrough
- Liverpool v West Ham United
Leicester City da Manchester City, 'Yan wasan da za su taka-leda

Asalin hoton, BBC Sport
Yadda teburin gasar Premier yake

Asalin hoton, BBC Sport
Sakamakon wasannin mako na 15 gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images
Gasar Premier wasannin mako na 15

Asalin hoton, BBC Sport
Real Madrid da Deportivo
Real Madrid za ta karbi bakun cin Deportivo La Coruna a wasan mako na 15 a gasar La Liga a ranar Lahadi.
Real Madrid tana mataki na daya a kan teburi da maki 34, yayin da Deportivo ke matsayi na 16 da 13.

Asalin hoton, Getty Images
Swansea 3-0 Sunderland, Yadda ake murza-leda

Asalin hoton, BBC Sport
GOAL Burnley 3-1 Bournemouth
Hull 2-2 Crystal Palace, Yadda ake gara wasa

Asalin hoton, BBC Sport
GOAL Hull City 2-2 Crystal Palace, Adama Diomande na Hull City
GOAL Hull City 1-2 Crystal Palace, Wilfried Zaha na Crystal Palace
GOAL Swansea 2-0 Sunderland, Fernando Llorente a minti na 54
Damben: Garkuwan Shagon Alabo da Mahaukaci Teacher
Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu ne ya buge Mahaukaci Teacher daga Arewa a turmi na biyu a damben da suka yi a Dei-Dei a Abuja, Nigeria.
Bayanan bidiyo, A turmi na biyu Garkuwan Shagon Alabo ya yi nasara Fifa ta dakatar da wasu jami'an kwallon Afirka
Fifa ta dakatar da tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta Kudu Kirsten Nematandani, daga shiga harkokin wasanni tsawon shekara biyar, saboda an same shi da laifin kin bayyana almundahana da kuma kin bayar da hadin kai ga bincike.
Laifin ya danganci wasu wasannin sada zumunta ne guda uku na kasa da kasa da aka yi a Afrika ta Kudu kafin gasar cin kofin duniya ta 2010.
Haka kuma FIfa ta haramta wa wani tsohon jami'in hukumar kwallon Zimbabwe Jonathan Musavengana, da tsohon kocin Togo Banna Tchanile, shiga harkokin wasanni tsawon rayuwarsu sakamakon laifin cin hanci da rashawa.
Mista Musavengana yana da hannu ne a wata cuwa-cuwa da aka biya 'yan wasan kasar Zimbabwe kudi domin su bari a ci su, a wasanni a yayin wani rangadi na Asia a 2009.

Asalin hoton, Google
GOAL Hull 1-1 Crystal Palace, Christian Benteke na Crystal Palace
GOAL Swansea 1-0 Sunderland, Gylfi Sigurdsson a minti na 51
Watakila Mikel Obi ya bar Chelsea a Janairu
Bayanan sautiHira da aka yi da Mikel kan yadda ba ya buga wa Chelsea wasanni Yawan matan da ke wasanni ya karu a duniya
Yawan matan da ke wasanni akai akai a duniya ya kai yawan da bai taba kaiwa ba zuwa miliyan bakwai da dubu dari biyu da goma kamar yadda wani bincike ya nuna.
Binciken na kungiyar Sport England, ya gano cewa yawan matan da suke shiga wasanni ya karu da 250,000 tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da shirinta na wayar da kan mata su rika shiga wasanni (This Girl Can) a 2014.
Bambancin yawan maza da matan da suke wasanni ya ragu kamar yadda nazarin ya nuna zuwa miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin.
Haka kuma gaba daya an samu karin mutanen da ke wasanni akai akai maza da mata har 229,400, idan aka kwatanta da shekarar da ta wuce.

Asalin hoton, Mehr
GOAL Arsenal 2-1 Stoke City, Ozil
