Labaran wasanni da suke gudana a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da suke gudana a fagen wasanni musamman irin wainar da ake toyawa a duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin, sai mako mai zuwa

  2. Liverpool da Manchester City, 'Yan wasan da za su buga wa Man City

    Man City XI: Bravo, Zabaleta, Stones, Otamendi, Kolarov, Fernandinho, Yaya Toure, Sterling, Silva, De Bruyne, Aguero

    Masu jiran kar-ta-kwana: Caballero, Clichy, Sagna, Fernando, A Garcia, Iheanacho, Navas

    gASAR pREMIER WASAN MAKO 19
  3. Liverpool da Manchester City, 'Yan wasan da za su buga wa Liverpool

    Liverpool XI: Mignolet, Clyne, Lovren, Klavan, Milner, Henderson, Wijnaldum, Can, Lallana, Mane, Firmino.

    Masu jiran kar-ta kwana: Karius, Lucas, Moreno, Alexander-Arnold, Ejaria, Origi, Sturridge.

    Gasar Premier mako na 19
  4. An kammala wasu wasannin Premier

    Gasar Premier mako na 19
  5. GOAL Swansea 0-3 Bournemouth, Joshua King

  6. GOAL GOAL - Manchester United 2-1 Middlesbrough, Paul Pogba na United

  7. GOAL Manchester United 1-1 Middlesbrough, Anthony Martial

  8. Tevez ya fi kowa albashi a 'yan kwallo

    Tsohon dan wasan gaba na Manchester City da Man United Carlos Tevez ya zama dan kwallon da ya fi daukar albashi a duniya, da fan dubu 310, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati, bayan ya koma Shenhua ta China.

    Shanghai ta dauki dan wasan na gaba dan Argentina mai shekara 32, daga kungiyar Boca Juniors, amma babu wani cikakken bayani da aka bayar kan yarjejeniyar, amma an ce kwantiragin na shekara 2 ne.

    Sai dai wasu rahotanni sun ce Shanghai wadda tsohon kocin Brighton Gus Poyet ya koyar, ta amince da kwantiragin a kan kusan fan miliyan 40 tare da biyan dan wasan albashin fan 310,000, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati.

    Gasar Premier mako na 19
  9. Sakamakon wasannin Premier mako na 19

    Gasar Premier mako na 19
  10. Serena Williams za ta auri Alexis Ohanian

    Fitacciyar 'yar wasan kwallon tennis, Serena Williams, ta yi amfani da kafar sada zumunta ta Reddit wajen sanar da baikonta tare da Alexis Ohanian.

    Williams ta sanar da baikon da tayi da Ohanian daya daga cikin mamallakin Reddit ta hanyar rubutacciyar waka.

    'Yar wasan tennis din ta ce ya gayyace ta Rome, birnin da suka fara haduwa, inda ya bukaci ta aure shi, kuma nan da nan ta amsa masa.

    Gasar Premier makop na 19
  11. GOAL Manchester United 0-1 Middlesbrough, Grant Leadbitter

    Grant Leadbitter

  12. Dambe: Mahaukaci Teacher da Garkuwan Shagon Alabo

    Bayanan bidiyo, Dambe da aka yi tsakanin Mahaukacin Teacher da Garkuwan Alabo
  13. GOAL Burnley 3-0 Sunderland, Andre Gray na Burnley

  14. GOAL Chelsea 2-1 Stoke City, Willian na Chelsea

  15. Watford za ta sayo 'yan wasa a Janairu

    Kociyan Watford, Walter Mazzari zai sayo karin 'yan kwallo idan aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula a watan Janairu. 

    Kociyan na fama da rashin 'yan kwallo tara da suka ci karo da yin jinya ko wadanda aka dakatar daga wasa bayan da suka yi laifi. Cikin 'yan wasa sun hada da Roberto Pereyra da Valon Behrami da Adrian Mariappa da Isaac Success da kuma Adlene Guedioura. 

    Haka shi ma Ben Watson ba zai buga wasa ba, yayin da aka dakatar da Miguel Britos.

    Gasar Premier mako na 19
  16. GOAL Chelsea 1-1 Stoke City, Bruno Martins Indi na Stoke City

  17. Chelsea 1-0 Stoke, Yadda ake gara wasan

    Gasar Premier mako na 19
  18. GOAL Chelsea 1-0 Stoke City, Garry Cahill

  19. GOAL Swansea 0-1 Bournemouth, Benik Afobe

  20. GOAL Leicester City 1-0 West Ham, Islam Slimani