Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a shirinmu na ranar Litinin.
Labaran wasannin karshen mako
Labaran wasanni kai tsaye kan abubuwan da ke gudana a duniyar wasanni da wainar da ake toyawa a kasuwar musayar 'yan kwallo ta nahiyar Turai.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Manchester United da Leicester City, 'Yan wasan da za su buga wa Leicestet tamaula
Foxes XI: Schmeichel, Simpson, Morgan, Maguire, Fuchs, Mahrez, Ndidi, James, Albrighton, Okazaki, Vardy.

Asalin hoton, BBC Sport
Manchester United da Leicester City, 'Yan wasan da za su yi United kwallo
Manchester United Wannan karon za a fara wasa da Anthony Martial, shi kuma Marcus Rashford yana benci.
United XI: De Gea, Valencia, Bailly, Jones, Blind, Pogba, Matic, Mata, Mkhitaryan, Martial, Lukaku.

Asalin hoton, BBC Sport
Ronaldo ne gwarzon dan kwallon Turai na bana
Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice a Turai a shekarar nan a bikin da aka yi a Monaco.
Dan wasan ya doke abokan takararsa da suka hada da Lionel Messi na Barcelona da mai tsaron ragar Juventus, Gianluigi Buffon.

Asalin hoton, Getty Images
Jadawalin gasar Europa
Arsenal tana rukunin da ya kunshi BATE Borisov da Cologne da kuma Red Star ta Belgrade a gasar Europa League da aka raba jadawali a ranar Juma'a.
Wannan ne karon farko a shekara 20 da Gunners, wacce ta yi ta biyar a kan teburin Premier da aka kammala za ta buga gasar ta Europa a bana.

Asalin hoton, Getty Images
Floyd Mayweather da Conor McGregor
A tsakar daren Asabar za a yi damben boksin tsakanin Floyd Mayweather da Conor McGregor, shin wa zai yi nasara a karawar?

Asalin hoton, Getty Images
Dembele shi ne na biyu mafi tsada da aka saya a bana

Asalin hoton, Getty Images
Damben da Autan Faya ya buge Shagon Dan Jamilu
Wasu wasannin damben gargajiya da aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria ciki har da wasan da Shagon Buzu ya yi nasara a kan Shagon Babangida.
Wasannin mako na uku a gasar Premier, Sauran karawa tsakanin United da Leicester

Asalin hoton, BBC Sport
Teburin gasar Firimiyar Nigeria, Bayan wasannin mako na 35

Asalin hoton, LMCNPFL
Dembele zai saka lambar Neymar a Barcelona
Bayan da Barcelona ta amince ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund, Ousmane Dembele kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5 domin ya maye gurbin Neymar.
Kungiyar za ta bai wa dan kwallon riga mai lamba 11 ta Neymar, kuma a ranar Litinin za ta gabatar da shi ga magoya bayanta.

Asalin hoton, Barcelona FC
Newcastle 3-0 West Ham
Konta na shirin buga gasar tennis ta US Open
A makon gobe ne za a fara gasar kwallon tennis ta US Open, kuma tuni Johanna Konta ta fara shirin yadda za ta taka rawar gani a wasannin.
Konta 'yar Burtaniya za ta fara wasan farko da Aleksandra Krunic ta Sabia wacce ke mataki na 77 a jerin 'yan wasan da ke kan gaba a kwallon tennis a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Deportivo Alaves da Barcelona, La Liga wasan mako na biyu
'Yan wasa 18 da Barcelona ta ziyarci Alaves da su : Ter Stegen, Cillessen, Semedo, Piqué, Rakitic, Sergio, Denis Suárez, Iniesta, Messi, Mascherano, Paulinho, Deulofeu, Paco Alcácer, Jordi Alba, Sergi Roberto, André Gomes, Aleix Vidal da kuma Umtiti.

Asalin hoton, Barcelona FC
Huddersfield 0-0 Southampton

Asalin hoton, bbc
Huddersfield Town 0-0 Southampton, Sun je hutu

Asalin hoton, Getty Images
Crystal Palace 0-1 Swansea, Tammy Abraham
Wasannin mako na uku a gasar Premier

Newcastle 1-0 West Ham, Joselu
An bai wa Miguel Britos jan kati, Wartford 0-0 Brighton

Asalin hoton, Getty Images
