Labaran wasannin karshen mako

Labaran wasanni kai tsaye kan abubuwan da ke gudana a duniyar wasanni a ranar Asabar da wadanda za a yi a Lahadi.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a mako mai zuwa

  2. Wasu wasannin dambe da aka yi a Abuja

    Bayanan bidiyo, Wasanni hudu aka yi canjaras a damben Dei-Dei
  3. Za a yi damben kasa a Jigawa, Nigeria

    Hukumar wasan damben gargajiya ta Nigeria ta tsayar da ranar Juma'a 24 da Asabar da Lahadi domin buga wasan dambe na kasa a Hadejia, jihar Jigawa Nigeria.

    Wasannin za a yi ne domin raya al'adar wasan Bahaushe da kuma farfado da dambe a jihar ta Jigawa.

    Kai tsaye
  4. Kenya ta dauki koci Paul Put

    Hukumar kwallon kafar Kenya ta sanar da daukar Paul Put a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar.

    Put, mai shekara 61, ya saka hannu kan yarjejeniyar horar da Harambee Stars.

    Kai tsaye
  5. Ko kun san waye Sadio Mane?, Zaben gwarzon dan kwallon kafa na BBC na 2017

    Kalli bayani kan Sadio Mane, daya daga cikin 'yan wasan da ke takarar cin kyautar gwarzon dan wasan Afirka ta shekarar 2017 ta BBC.

    Bayanan bidiyo, Ko kun san waye Sadio Mane?
  6. Arsenal ta ci Tottenham 2-1

    A karon farko Arsenal ta ci Tottenham 2-0 a fafatawa bakwai da suka buga a gasar Premier a wasan mako na 12 da suka kara a ranar Asabar.

    Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Shkodran Mustafi sannan Alexis Sanchez ya kara ta biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci.

    Kai tsaye
  7. Ko kun san waye Naby Keita?, Zaben gwarzon dan kwallon kafa na BBC na 2017

    kalli bayani game da Naby Keita, daya daga cikin masu takarar cin kyautar gwarzon dan wasan Afirka na BBC na shekarar 2017

    Bayanan bidiyo, Ko kun san waye Naby Keita?
  8. Rukunin gasar kofin Afirka ta CHAN, Gasar kofin Afirka ta 'yan wasan da ke taka-leda a gida

    Group A (Casablanca)MoroccoGuineaSudanMauritaniaGroup B (Marrakech)Cote d’IvoireZambiaUgandaNamibiaGroup C (Tangier)LibyaNigeriaRwandaEquatorial GuineaGroup D (Agadir)AngolaCameroonCongoBurkina Faso

    Kai tsaye
  9. Za a fara gasar Firimiyar Nigeria a 2018

    Bayan da aka fara yi wa 'yan kwallon gasar Firimiyar Nigeria lasisi, ana sa ran fara atisayen tunkarar kakar badin tsakanin 11 zuwa 17 ga 2017.

    Za kuma a fara gasar a ranar 14 ga watan Janairun 2018.

    Kai tsaye
  10. Ko kun san waye Victor Moses?, Zaben gwarzon dan kwallon kafa na BBC na 2017

    Kalli bayani game da Victor Moses, daya daga cikin masu takarar zama gwarzon dan kwallon Afirka na BBC

    Bayanan bidiyo, Ko kun san waye Victor Moses?
  11. Dortmund ta dakatar da Aubameyang

    Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang a matakin da ta dauka na ladabtar da shi.

    Dan wasan tawagar kwallon kafar Gabon ba buga wa Dortmund wasan Bundesliga da ta fafata da VFB Stuttgart a ranar Juma'a.

    Dortmund ta sanar da dakatar da dan kwallon mai shekara 28 bisa mayar wa da wani magoyin baya martani da ya yi tambaya a shafin sada zumunta na Twitter, amma kungiyar ba ta fayyace komai ba.

    A bara ma sai da Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang, bayan da ya je Italiya ba tare da sanin kungiyar ba.

    Wasa ya fara juya wa Dortmund baya, inda ta yi rashin nasara a fafatawa uku daga hudu da ta yi kwanan nan a Bundesliga ta kuma koma ta uku a kan teburin gasar bana.

    Kai tsaye
  12. Atletico Madrid da Real Madrid

    A ranar Asabar za a buga wasan hamayya a gasar cin kofin La Ligar Spaniya tsakanin Atletico Madrid da Real Madrid; wannan ne kuma karo na 20 da za su fafata tun daga shekarar 2014.

    Kai tsaye
  13. Ko kun san waye Pierre-Emerick Aubameyang?, Zaben gwarzon dan kwallon kafa na BBC na 2017

    Kalli bayani game da Pierre-Emerick Aubameyang, daya daga cikin 'yan wasan dake takarar kyautar gwarzon dan wasan Afirka na shekarar 2017 ta BBC.

    Bayanan bidiyo, Ko kun san waye Pierre-Emerick Aubameyang?
  14. Arsenal 2-0 Tottenham, Alexis Sanchez

    Kai tsaye
  15. Arsenal 1-0 Tottenham, Shkodran Mustafi

    Kai tsaye
  16. Ko kun san Mohammd Salah?, Zaben gwarzon dan kwallon kafa na BBC na 2017

    Abu daya zai sa ba za a taba mantawa ba da Mohammed Salah a tarihin kwallon kafa a Masar, saboda kwallo mafi muhimmaci da ya ci wa kasarsa a ragar Congo ana dab da a hure wasan da suka kara a watan Oktoba, wanda ya ba kasar nasarar shiga gasar cin kofin duniya karon farko bayan shekaru 27.

    Bayanan bidiyo, Ko Kun san waye Mohammad Salah?
  17. Arsenal 0-0 Tottenham

    Kai tsaye
  18. Gasar French Legue 1 wasannin mako na

    Paris Saint-Germain vs FC Nantes

    EA Guingamp vs SCO Angers

    RC Strasbourg vs Stade Rennais

    Toulouse vs FC Metz

    Dijon vs ES Troyes AC

    Kai tsaye
  19. Arsenal 0-0 Tottenham

    Arsenal: Cech, Koscielny, Mustafi, Monreal, Bellerin, Ramsey, Xhaka, Kolasinac, Ozil, Sanchez, Lacazette. Subs: Mertesacker, Wilshere, Ospina, Iwobi, Welbeck, Maitland-Niles, Coquelin.

    Tottenham Hotspur: Lloris, Sanchez, Dier, Vertonghen, Trippier, Sissoko, Dembele, Eriksen, Davies, Alli, Kane. Subs: Son, Vorm, Llorente, Foyth, Aurier, Winks, Walker-Peters.

    Referee: Mike Dean

  20. Muhawarar da kuke tafka wa a BBC Hausa Facebook

    Mahmud Salihu Kaura Namoda: Arsenal za ta yi rugu rugu da Tottenham, da ma irin wannan wasa munfi samun galaba a kanta. Up Gunners.

    Musa Hadirin Asuba Damagaram: To bbc muna tare da ku sai dai mu a niger bama kamaku wallahi ya kamata a samu wani gidan redio da za mu dinga jin gasar Premier.

    Mustapha Salisu Gusau: Ai Tottenham yau za ku kwashi kashinku a hannun Arsenal Domin wannan wasa na Arsenal ne. UP Real Madrid