Yadda Barcelona ta lallasa Liverpool

Gasar cin kofin Zakarun Turai wasan farko na daf da karshe tsakanin Barcelona da Liverpool a Camp Nou.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan and Umar Mikail

  1. Rufewa, Barcelona 3-0 Liverpool

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin kai-tsaye. Ku ci gaba kasancewa da BBC.

    Umar Mikail da Umar Rayyan ne ke maku fatan mu kwana lafiya.

  2. Karawa ta gaba, Barcelona 3-0 Liverpool

    A ranar Talata mai zuwa ne 7 ga watan Mayu kungiyoyin biyu za su sake karawa a filin wasa na Anfield a karo na biyu.

    Liverpool za ta yi kokarin rama kwallaye 3 kuma ta kara 1, sannan ta samu damar zuwa wasan karshe.

  3. Messi ya zama dodon 'yan Ingila, Barcelona 3-0 Liverpool

    Messi

    Barcelona ta yi nasarar doke Liverpool da ci 3-0 a wasan farko na daf da karshe a gasar Champions Leageu da suka fafata ranar Laraba.

    Barcelona ta ci kwallayen ta hannun Luis Suarez tsohon dan wasan Liverpool da kuma Kyaftin Lionel Messi wanda ya ci biyu.

    Kwallayen da Messi ya ci Liverpool sun zama 26 da ya ci kungiyoyin Ingila a karawa 33 da suka yi a gasar Zakarun Turai.

    Messi ya ci Chelsea kwallo 3 sai Arsenal da ya zura 9 a raga da Manchester City da ya ci 6 sai United da ya ci 4 da kuma Tottenham da ya ci biyu.

    Messi ya fuskanci Liverpool a wasan zagaye na biyu a gasar Champions League karawar zagaye na biyu, a lokacin dan kwallon tawagar Argentina yana da shekara 19 a kakar 2006-7.

    Ya kuma buga dukkan fafatawar biyu kuma da shi aka karkare wasannin da Liverpool ta yi nasara da ci 2-1 a Nou Camp, amma ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0.

    Da wannan sakamakon Barcelona ta yi nasara a wasa 32 a Champions League kenan a gida, inda ta ci 29 da canjaras 3.

    Wannan ne karon farko da Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Barcelona a wasan waje a fafatawa hudu da suka yi, inda kungiyar Anfield ta yi nasara a wasa biyu da canjaras biyu.

    Barcelona wadda ke shirin lashe kofi uku a bana ta kai wasan karshe a Copa del Rey da za ta buga da Valencia, kuma a ranar Asabar ta lashe kofin La Liga na bana kuma na 26 jumulla.

    Barcelona za ta ziyarci Anfield domin buga wasa na biyu na daf da karshe ranar 7 ga watan Mayu.

    Barcelona ta lashe kofin Zakarun Turai guda biyar, ita ma Liverpool biyar ne da ita.

    Barcelona ce ta fitar da Manchester United a wasan daf da na kusa da karshe, kuma watakila kungiyoyin Ingila su kasa kai wa wasan karshe.

    Tottenham ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0 a hannun Ajax ranar Talata.

    Yadda kungiyoyin suka murza-leda.

  4. Rio Ferdinand game da Messi, Barcelona 3-0 Liverpool

    "Na ji dadin kasancewa a raye, Wannan baiwa ce domin yanzu zan iya bai wa 'ya'yana labarin Messi. Shi ne yake tsara yadda wasa zai kasance," in ji Rio Ferdinand

  5. , Barcelona 3-0 Liverpool

    Wannan shi ne karo na biyu da Liverpool ke shan ruwan kwallaye har uku a gasar Zakarun Turai ta Champions League tun 2014, lokacin da Real Madrid ta cinye ta

  6. Messi ya cinye Liverpool, Barcelona 3-0 Liverpool

    Wai ta ina ma mutum zai fara ne!

    Liverpool sun yi ta buga wasa har wajen minti na 70 kafin Messi ya yunkuro da asirinsa da taimakon Lius Suarez.

    Bugun tazarar da Messi ya ci shi ne ya kawo karshe duk wani fata daga 'yan wasan Liverpool.

    Tun a minti 45 na farko Mane ya kamata ya farkje wa liverpool amma ya zubar da damar.

    Ya kamata wasan ya zama 5-0 ko ma 6-0, saboda irin damarmakin da Barcelona suka zubar, ciki har da ta mintin karshe wadda Dembele ya zubar.

  7. An tashi daga wasa, Barcelona 3-0 Liverpool

    Lafari ya busa tashi bayan minti 4 da aka kara. Daf da za a busa tashin Messi ya samu kwallo a cikin yadi na 18 din Liverpool amma ya buga ta yana neman Dembele. Dembele ya samu kwallon amma ya buga ta ga hannun Alisson.

    Messi
  8. , Barcelona 3-0 Liverpool

    Ana cikin minti 4 da aka kara, saura dakikoki a tashi daga wasa. Ousman Dembele na Barcelona ya shigo fili

  9. , Barcelona 3-0 Liverpool

    Messi ya jawo kwallo tun daga gidan Barcelona kuma ya mika Suarez a bakin ragar Liverpool. Suarez ya bugo yana neman Jordi Alba amma bai same shi. Barcelona sumn yi bugun kwana

  10. Messi ya ci bugun tazara, Barcelona 3-0 Liverpool

    Messi ya ci bugun tazara bayan da Liverpool suka yi kuskuren yin laifi a bakin ragarsu. Da alama sun manta cewa da Messi suke wasa

    Messi
  11. Liverpool sun yi canji, Barcelona 3-0 Liverpool

    Roberto Firmino ya karbi Wijnaldum

  12. GO Messi, Barcelona 1-0 Liverpool

    To wane ne ban da shi!

    Messi ya ci kwallon bayan da Suarez ya buga ta da gwiwarsa ta bugi turken sama. Shi kuwa Messi dama yana kusa, ya ajiye ta a kirji kuma ya saka ta a raga.

    Messi
  13. Coutinho, Barcelona 1-0 Liverpool

    An tsammaci Coutinho zai yi fata-fata da Liverpool, amma ga shi har an cire shi daga wasan kuma babu wani hari da ya kai mummuna. Ko ma dai mene ne, Su dai Liverpool a dadinsu

    Coutinho
  14. An yi canji, Barcelona 1-0 Liverpool

    Nelson Semedo ya canji Coutinho. Shi ne sauyin Barcelona na farko a wasan.

  15. Liverpool na danna Barcelona, Barcelona 1-0 Liverpool

    Barcelona

    Ga alama Liverpool ta sauya salon wasanta tun bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, inda yanzu take kai wa Barcelona munanan hare-hare a kokarinta na ganin ta farke kwallon da ta zura mata.

  16. Milner ya kai hari, Barcelona 1-0 Liverpool

    James Milner ya dadata kwallo da kyau amma Stegen ya hana masa ya kuma kama ta. An bugo kwallon ne daga gefe, inda Mane ya tsallake wa Milner don ya buga. Wasan ya yi kyau sosai.

  17. Mo Salah, Barcelona 1-0 Liverpool

    Mo Salah ya kai mummunan hari daga yadi na 23, inda Stegen ya tura kwallon da kyar.

  18. Wasa ya sake daukar zafi fa, Barcelona 1-0 Liverpool

  19. James ya kai wa Barcelona wawan hari, Barcelona 1-0 Liverpool

    An dawo hutun rabin lokaci, inda za a ci gaba da fatatawa.

    James Milner ya kai wa Barcelona wawan hari, amma golan Barcelona, Stegen, ya ture kwallon. Wannan ne hari na farko a falle na biyu na wasan

  20. An koma wasa, Barcelona 1-0 Liverpool