Gasar La Liga: Sevilla ta doke Real Betis 2-0

Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan ci gaba da aka yi da gasar La Liga da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassa na duniya

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba.

    Za a buga wasa biyu a La Liga ranar Juma'a

    Sai a makon gobe za a ci gaba da Premier League da Serie A.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheri.

  2. sevilla 2-0 Betis

    Kai tsaye
  3. Sevilla 2-0 Beis

    Kai tsaye
  4. Wasannin mako na 29 a gasar La Liga

    Kai tsaye
  5. An tashi was - Sevilla 2-0 Real Betis

    Sevilla ta hada maki uku tana nan a mataki na uku a kan teburin La Liga, biye da Real Madrid ta biyu da tazarar maki shida,

  6. Sevilla 2-0 Real Betis

    An kusan tashi wasan na hamayya kuma tuni tsakar dare ya yi a birnin Sevilla.

  7. Sevilla 2-0 Real Betis

    Nuna kwarewa da Jaoquin ya yi wanda wata kwallo da ya buga ta je gun Nabil Fekir yana gudu kai tsaye, shi kuma ya buga kwallon amma ta yi fadi ta yi wajen fili.

  8. Sevilla 2-0 Real Betis

    Ana buga wasan ne da kuwa ta 'yan kallo da aka nada ake sawa a lokacin wasa, haka kuma a kwai hotunan 'yan kallo da aka kafa a allo aka dora kan kujerun zama.

  9. Sevilla 2-0 Betis

    Betis ta tagaza inda Emerson ya yanke dan wasa ya kuma bugo kwallo cikin da'ira ta 18 ta Sevilla kuma Borja ya sa kai amma ta yi fadi.

  10. Sevilla 2-0 Real Betis

    Sevilla ta koma saura maki uku tsakaninta da Real Madrid wadda take ta biyu a teburi.

  11. An kara kwallo - GOAL - Sevilla 2-0 Real (Fernando)

    BKwallon mai kyau da Lucas Ocampos na Sevilla ya bugo nan da nan Fernando ya samu ya kuma zura a raga.

  12. Sevilla 1-0 Real Betis

    Ya kamata Betis ta kara sa kwazo a wannan wasan na hamayya idan ba haka ba kwallaye da yawa za su iya shiga ragarka kuwa.

  13. An ci kwallo - Sevilla 1-0 Real Betis (Lucas Ocampos)

    Lucas Ocampos ta sa riga mai lamba biyar bai kuma ba ta lokaci ba wajen zura kwallo a raga kuma na biyar da ya ci a jere a La Liga.

    Kungiyoyin da ya ci

    vs. Espanyol vs. Getafe vs. Osasuna vs. Atlético Madrid da kuma Real Betis

    Dan wasan kungiyar da ya yi wannan bajintar shi ne Álvaro Negredo a shekarar 2011.

    kAI TSAYE
  14. An bai wa Sevilla fenariti, Sevilla 0-0 Real Betis

    An bai wa Sevilla fenariti bayan da Marc Bartra ya haye bayan Luuk de Jong kuma alkalin wasa ba wata tantama ya nufi wurin buga fenariti ya kuma nuna da hannunsa.

  15. Sevilla 0-0 Real Betis

    Jesus Navas na tunanin an yi masa ba daidai ba yana ganin ya kamata a dauki mataki. amma alkali bai ga komai ba, saboda haka ya nufi VAR.

    Babu wani hukuncin da aka dauka

  16. An koma wasa Sevilla 0-0 Real Betis

  17. Kungiyoyin za su iya canja 'yan wasa biyar a wannan karawar.

    Sai dai sau uku ake so kayi don gudun ba ta lokaci.

    Ko dai ka sauya 'yan wasa uku da farku sannan kasa biyu ko daidai daga baya kar dai kayi sauya ya wuce zuwa uku.

    Ana nufin zaka iya fara sa biyu sai ka kara sa biyu sannan ka sa daya daga karshe duk yadda kungiya ke son yi.

  18. Sevilla 0-0 Real Betis

    Real Beti ta ci wasa daya kacal daga 13 da ta buga a waje a gasar L Liga ta bana da canjaras shida aka doke ta karawa shida.

    Kakar wasa da ta yi karancin samun nasarori a karawar waje tun bayan kakar 2013/14.

  19. An je hutu

    Har yanzu babu ci a wasan na hamayya tsakanin Sevilla da Real Betis.

  20. Za a soma musayar 'yan kwallo kafin gama kakar wasan bana - Fifa

    Sabbin dokokin da Hukumar kwallon Kafa ta Duniya, Fifa, ta fitar ranar Alhamis sun amince kungiyoyi su bude kasuwar musayar 'yan kwallo kafin a kammala kakar wasa ta bana.

    Fifa ta ce ta dauki matakin ne sakamakon jinkirin da annobar korona ta kawo a harkokin wasanni a duk fadin duniya.

    Tuni shugaban Premier League Richard Masters ya ce ba za su bari kungiyoyin kwallon kafar Ingila su bude kasuwar musayar 'yan kwallo ba kafin ranar 25 ga watan Yuli, bayan an kawo karshen jinkirin da aka yi.

    Galibin hukumomin gasar kwallon kafar Turai suna da irin wannan niyya, amma sabbin dokokin Fifa za su ba su damar soma musayar 'yan kwallo da wuri.

    Kazalika Fifa ta sanar cewa za a kyale 'yan wasa su buga wasa a kungiyoyi uku - sabanin kungiyoyi biyu - a kakar wasa daya.

    Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da Gasar Premier, inda kowacce kungiya za ta buga wasa akalla tara, yayin da su ma FA Cup, Zakarun Turai da Gasar Europa ake sa ran kammala su.

    Kai tsaye