Real Madrid ta gabatar da Antonio Rudiger

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo muku karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin da muka kawo muku na kai tsaye kan cinikayyar 'yan wasa da wasu labaran wasanni na wannan ranar.

    Za ku iya tafka muhawara a labaran da muke kawo muku a BBC Hausa Facebook da kuma Twitter.

    Za ku iya saurarar shirin labaran wasanni a radiyo da karfe 8:30 agogon Najeriya da kuma washe gari da karfe 6:30 da kuma 7:30 agogon Najeriya tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW.

    Da fatan za ku tara a shirinmu na gobe kai tasye, mu wuni lafiya.

  2. Za a zakulo masu cin zarafin 'yan wasa a kafar sada zumunta

    Hukumar kwwallon kafa ta duniya, Fifa za ta yi hadin gwiwa da kungiyar kwararrun 'yan wasan tamaula don zakulo massu cin zarafin 'yan wasa a kafar sada zumunta.

    Wani rahoto ya bankado sako 400,000 da aka ci zarafin 'yan wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 da kuma gasar kofin Afirka da aka yi a Kamaru a bana.

    Binciken da aka yi an gano cewar 'yan wasan da suka barar da fenariti a wasan karshe a Euro 2020 sune aka fi cin zarafi a kafar sada zumuntar.

    Saka and Rashford
  3. Sakamakon damben Kano ranar Lahadi da yammaci

    Dambe Dogon Sisco da Shagon Yalo dan Zuru, shi ne kadai wasan da aka yi canjaras a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano Nigeria.

    Sauran dambatawar mazaje sun sha kasa:

    Dogon Habu Cingam ya doke Shagon Shatima

    Shagon Dada daga ya buge Dogon Bahagon Audu Argungu

    Shagon Bahagon Mancha ya doke Shagon Saiwa

    Bahagon dan kanawa ya yi nasara a kan Mustaphan dan Shago

    Dan Butsalle ya doke Bahagon Zayyanu

    Manu Shagon Garkuwa ya buge Shagon Ali Kanin Bello

    Bahagon Ali Kawoji ya doke Rabe Shagon Ebola

    Damben Gargajiya
    Bayanan hoto, Damben da Bahagon Ali Kawoji ya buge Rabe Shagon Ebola
  4. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikayyar 'yan wasa

    Idan Manchester United ta kasa daukar De Jong, to za ta karkata ga dan wasan tsakiya na Wolves da Portugal Ruben Neves, mai shekara 25. (Fabrizio Romano, givemesport)

    An bai wa Newcastle damar sayen dan bayan Ivory Coast Eric Bailly, mai shekara 28, daga Manchester United. (Mirror)

    Haka kuma an gaya wa Newcastle din (The Magpies) cewa sai ta biya fam miliyan 50 idan tana son dan wasan gaba na gefe na Bayer Leverkusen da Faransa Moussa Diaby. (Sun)

    Cristiano Ronaldo, ya yi maraba da shirin Manchester United na kokarin nemo wani sabon dan wasan gaba. (Express)

    Ruben Neves
  5. An tsayar da rana sake damben Joshua da Usyk, Damben boksin

    An tsayar da ranar 20 ga watan Agusta domin sake dambatawa tsakanin Anthony Joshua da Oleksandr Usyk a Saudi Arabia.

    Dan damben Burtaniya, Joshua na fatan lashe kambunan WBA da IBF da kuma WBO da ya rasa a wasan da suka yi a cikin watan Satumba a filin wasa na Tottenham Hotspur a bara.

    Boxing
  6. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikayyar 'yan wasa

    Kociyan Holland kuma tsohon mai horas da 'yan wasan Manchester United Louis van Gaal ya taka rawa wajen hana dan bayan Holland na kungiyar Ajax Jurrien Timber, mai shekara 21, tafiya Old Trafford. (Marcel van der Kraan, Sky Sports)

    Wakilin dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek ya ce tsohon kociyan kungiyar ta Blues Maurizio Sarri na sha'awar daukan dan wasan mai shekara 26 zuwa Lazio. (Metro)

    Ajax ta sanya wa Sebastian Haller farashin yuro miliyan 40 (fam miliyan 34.3), inda Borussia Dortmund ke sha'awar dan gaban na kasar Ivory Coast mai shekara 27. (90min)

    Sunderland da Huddersfield da Bristol City sun taya matashin dan wasan tsakiya na AFC Wimbledon dan Ingila mai shekara 21 Jack Rudoni, fam miliyan daya da sauran tsarabe-tsarabe. (Sun)

    Ruben Loftus-Cheek
  7. Frankfurt ta kusan kammala sayen Frankfurt

    Wadda ta lashe Europa League na bana, Eintracht Frankfurt ta kusan kammala daukar dan kwallon tawagar Jamus, Mario Gotze daga PSV Eindhoven, in ji wasu rahotanni ranar Litinin.

    Mario Gotze
  8. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikayyar 'yan wasa

    Chelsea za ta nemi bayani daga Manchester City din a kan dan bayanta Nathan Ake, dan Holland. (Telegraph)

    Romelu Lukaku, na shirin komawa Inter Milan aro daga Chelsea a kan kudi fam miliyan takwas da rabi da sauran tsarabe-tsarabe da kungiyoyin suka amince a tsakaninsu. (Mail)

    Manchester United na shirin kara sabon tayi a kan dan wasan tsakiya na Barcelona da Holland Frenkie de Jong. (Fabrizio Romano)

    Nathan Ake
  9. Watakila Luis Enrique zai bar tawagar Sifaniya

    Luis Enrique zai ci gaba da zama kociyan tawagar Sifaniya zuwa karshen kakar 2023.

    Koda yake wasu rahotanni na cewar kociyan zai bar tawagar da zarar an kammala gasar kofin duniya a Qatar da za a fara tsakanin Nuwamba zuwa Disambar 2022.

    Sai dai kuma wasu rahotannin na cewar watakila Sifaniya ta rarrashi Enrique ya ci gaba da zan ragama zuwa karshen kakar 2023.

    Luis Enrique
  10. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikayyar 'yan wasa

    Tottenham na fatan doke abokiyar hamayyarta ta arewacin London Arsenal a zawarcin dan wasan Manchester City kuma dan Brazil Gabriel Jesus, ta kwadaita masa wasan Zakarun Turai da ta samu gurbi. (Mirror)

    Shi kuwa dan wasan Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27, yana tambayar jama'a yanayin rayuwa a yammacin London yayin da Chelsea ke neman saye shi. (Athletic)

    Manchester City dai ta yi watsi da tayin farko na fam miliyan 21 da rabi da Chelsea ta yi wa dan wasan dan asalin kasar Jamaica. (Fabrizio Romano)

    Gebriel Jesus
  11. Shagon Audun Tunga ya buge Autan dan Bunza

    Ranar Lahadi a damben naira 100,000 Shagon Audun Tunga Guramada ya doke Autan dan Bunza a turmi na uku a gidan wasa da ke Marabar 'Nyanya a jihar Nasarawa, Najeriya.

    Bayanan bidiyo, Shagon Audun Tunga ya buge Autan dan Bunza
  12. Kalidou Koulibaly na murnar zagayowar ranar haihuwarsa

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. West Ham ta kammala daukar Nayef Aguerd

    West Ham United ta sanar da kammala daukar dan wasan Rennes, mai tsaron baya, Nayef Aguerd kan fam miliyan 30.

    Kungiyar da ke buga Premier League ta sanar da cewar dan wasan mai shekara 26 ya amince da kunshin kwantiragin kaka shida.

    Dan wasan ya buga karawa 66 a Rennes, tun bayan da ya koma kungiyar Faransa daga Dijon.

    Nayef Aguerd
  14. Liverpool ta kammala daukar Ramsay

    Liverpool ta kammala cinikin matashin dan wasa, mai shekara 18, Calvin Ramsay daga Aberdeen kan yarjejeniyar kaka biyar kan fam miliyan 4.2.

    Cikin kunshin yarjejeniyar har da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 2.5 da biyan kaso 17.5 ga Aberdeen idan Liverpool za ta sayar da matashin.

    Dan wasan zai shiga cikin 'yan wasan Liverpool kai tsaye, babu batun bayar da aronsa ga wata kungiyar.

    Calvin Ramsay
  15. Teburin gasar Firimiyar Najeriya bayan wasan mako na 34

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Sakamakon gasar Firimiyar Najeriya mako na 34

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Nketiah zai saka riga mai lamba 14 a bana

    Dan kwallon Arsenal, Eddie Nketiah ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar, domin ci gaba da taka lerda a Gunners.

    Tun farko kwantiraginsa zai kara a Emirates a karshen watan nan, wanda ya buga wasa 92 da cin kwallo 23, tun bayan da ya fara buga tamaula a kungiyar a 2017.

    Eddie Nketiah
  18. An kama auna koshin lafiyar Rudiger a Real Madrid

    Likitoci sun kammala auna koshin lafiyar Antonio Rudiger a asibitin Sanitas La Moraleja University a shirin da Real Madrid ke yi na gabatar da shi a matakin sabon dan wasanta.

    Antonio Rüdiger
  19. Lampard ya cika shekara 44 da haihuwa

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Barkanmu da saduwa a wannan lokaci

    Jama'a barkanmu da rana barkanmu da shiga wannan shafin da ke dauke da labaran cinikayyar 'yan kwallo da wasu labarin wasanni a rana irin ta yau Litinin.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW zan kasance da ku daga yanzu zuwa karfe 2;00 na yammaci.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa kai tsaye a BBC Hausa Facebook da kuma a Twitter.