An bai wa Toure kociyan makarantar tamaula ta Tottenham

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin .......

  2. Benjamin Pavard
    Bayanan hoto, Wasu rahotanni na cewar idan Chelsea ta kasa daukar Kounde za ta anemi mamadin dan kwallon ciki har da 'yan wwasan Bayern Munich biyu Dayot Upamecano ko kuma Benjamin Pavard ko dan kwallon Inter Milan, Skriniar ko kuma na Villarreal, Pau Torres. Wadda ta wallafa batun ita ce 90min.
  3. Marcus Rashford ya ce a shirye yake ya koam kan ganiya a kakar bana a karkashin sabon koci Erik ten Hag.

    Kakar da ta wuce dan wasan tawagar Ingila bai taka rawar da ta dace ba, wasu na cewar tun cin zarafin da aka yi masa a Euro 2022 dan kwallon ya yi baya a sa kwazo a wasanninsa.

    Cikin watan Agusta za a fara gasar kwallon kafa ta bana, inda Manchestert United za ta buga Europa League, bayan da ta yi ta shida a bara.

    Marcus Rashford
  4. An bai wa Yaya Toure kociyan makarantar tamaula ta Tottenham

    An bai wa tsohon dan wasan Manchester City, Yaya Toure aikin kociyan makarantar koyon tamaula ta Tottenham.

    Wanda ya lashe Premier League uku yana tare da Tottenham tun daga watan Disamba, wanda ke kokarin samun horon da zai ba shi damar mallakar lasisin nahiyar Turai a fagen horar da kwallon kafa nan gaba.

    Yaya Toure
  5. Ko De Jong zai koma Chelsea ne?

    Sport ta wallafa yadda Chelsea ta shiga cinikin Frenkie dan kwallon tawagar Netherlands wanda Manchester United ke son dauka kan fara kakar bana.

    Ta kuma ce watakila dan kllwallon ya zabi komawa Chelsea, wadda farashinta ya yi kasa da wanda United ta maince da aka gindaya mata.

    Frenkie de Jong
  6. Har yanzu ba wani batu kan cinikin Youri Tieleman na Leicester City, bayan da ake alakanta shi da zai koma Arsenal ko Manchester United.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Nottingham Forest na shirin yin wani cinikin ....

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Dan wasan Manchester United, James Garner ya ce ya sa ran zai buga wasanni sosai a kungiyar a bana, amma bai ga alamar hakan ba - saboda haka a shirye yake ya sake zuwa buga wasannin aro a kakar nan.

    Mai shekara 21 ya taka rawar gani a wasan aro a Nottingham Forest a Championship a 2021-22.

    Dan kwallon baya fatan yin zaman benci, sadoda haka ya zabi ya sake zuwa wata kungiyar buga wasannin aro.

    James Garner
  10. Chelsea ta rufe hanyar da Barcelona za ta dauki masu tsaron bayanta

    Bayan da ake hangen Chelsea za ta yi rashin daukar Kounde,Sport ta wallafa cewar kungiyar Stamford Bridge ta rufe duk wata hanya da Barcelona za ta dauka mata masu tsaron bayanta da suka hada da Marcos Alonso da kuma Cesar Azpilicueta.

    Chelsea
  11. Mara ya ce ya koma Southampton kungiyar da ta dace da shi

    Sekou Mara ya ce ya koma Southampton bai yi zaben tumun dare ba, kuma ita ce kungiyar da ta dace da shi domin bunkasa sana'arsa ta kwallon kafa.

    Shi ne na shida da kungiyar ta dauka a bana, bayan mai tsaron raga Gavin Bazunu da Mateusz Lis da mai tsaron baya Armel Bella-Kotchap da mai buga tsakiya Romeo Lavia da kuma Joe Aribo da suka koma Southampton a bana.

    Mara
  12. 'Yan wasa uku ne a tarihi suka lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka a kuma shekara ya lashe kofin nahiyar Afirka.

    'Yan wasan sun hada da

    • Emmanuel Amunike a 1994
    • Patrick M'Boma 2002
    • Sadio Mane 2022
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Southamptoppn ta dauki Sekou Mara na shida kenan a bana

    Southampton ta dauki dan wasa na shida a bana, bayan da ta kammala cinikin Sekou Mara daga kungiyar Faransa, Bordeaux.

    Mai shekara 19 ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka hudu a kungiyar da ke buga Premier League.

    Sekou Mara
  14. Sakamakon wasannin damben gargajiya

    Karawar da aka fafata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Naigeria ranar Litinin.

    Inda Gudumar dan Jamilu daga Jamus ya doke Dan Fulanin Bahagon Mai Maciji daga Kudu - da wanda Bahagon Inda daga Arewa ya buge Autan Ebola daga Kudu.

    Sauran wasannin canjaras aka yi ba kisa tsakanin Shagon Bahagon Dage daga Kudu da Dan Dabar Autan dan Bunza daga Arewa da wasan Inda daga Jamus da Dan Sama'ila Shagon Alabo daga Kudu.

    Damben gargajiya
    Bayanan hoto, Damben da aka buge Dan Fulanin Bahagon mai maciji
  15. Scamacca ya amince da kunshin yarjejeniya a West Ham

    The Guardian ta wallafa cewar Scamacca ya amince da kunshin yarjejeniyar da West Ham ta gabatar masa.

    Ta kara da cewar zai saka hannu kan kwantiragin kaka biyar.

    Scamacca
  16. Carlos Alcaraz ya daura damarar jan ragamar mataki na daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya, bayan da ya zama matashi na farko da ya shiga jerin biyar din farko tun bayan bajintar Rafael Nadal.

    A jadawalin da hukumar kwallon tennis ta fitar ranar Litinin dan kasar Sifaniya yana mataki na biyar duk da doke shi da Lorenzo Musetti ya yi a wasan karshe a gasar da aka yi a Hamburg din Jamus.

    Hakan ya sa mai shekara 19 ya zama matashin da ya yi wannan tabukawar, bayan Nadal.

    Carlos Alcaraz
  17. Saura kwana biyu a yi bikin bude wasannin Commonwealth Games a Birmingham.

    Za a fara wasannin gadan gadan ranar Juma'a - inda mata za su fara da gasar da ake linkaya da tuka keke da kuma gudu a lokaci daya.

    Mai shekara 34, mai rike da kambun, Flora Duffy daga Bermuda ta tabbatar da cewar wannan ita ce gasar karshe da za ta fafata a Commonwealth Games...

    Flora Duffy
  18. Za a dakatar da kungiya idan magoya bayanta suka shiga filin wasa a lokacin gasar Premier League a bana da sauran wasannin tamaula a Ingila a kakar 2022/23.

    Hakan na daga cikin matakan da aka dauka tsaurara don kawo karshen halayyar magoya baya wajen shiga filin tamaula.

    An ci karo da koma baya a karshen kakar da ta wuce, inda 'yan kallo suka dunga shiga filin wasa da hakan kan zama barazana - haka kuma duk wani dan kallo ko magoyin baya da ya tada abuwan tartsatsin wuta ko mai tayar da hayaki, za a hana shi shiga stadiya har abada.

    Pitch invaders
  19. An yi wa sabon dan kwallon West Ham Aguerd tiyata bayan rauni

    Likitoci sun yi wa sabon dan wasan da West Ham United ta dauka a watan Yuni, Nayef Aguerd tiyata, bayan raunin da ya ji a wasan sada zumunta da Rangers.

    Mai shekara 26 ya koma West Ham daga Rennes mai buga Ligue 1 kan fam miliyan 30.

    West Ham ta sanar da cewar ''Dan kwallon tawagar Morocco zai ci gaba da yin jinya a Rush Green karkashin kulawar likitocin kungiyar''.

    Aguerd ya fara yi wa West Ham wasan farko a karawar sada zumunta da ta yi da Reading.

    Nayef Aguerd
  20. Barcelona sun yi atisaye da safiyar Talata

    Salon taba kwallo sau daya tal....