Za a gabatar da Neymar gaban kotu kan zargin zamba da cin hanci
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Za a gabatar da Neymar gaban kotu kan zargin zamba da cin hanci
Bayan shekara tara da Neymar daga Brazil ya koma Barcelona zai fuskanci kotu kan zargin yin abin da bai kamata ba a lokacin cinikin.
Ana zargin dan kwallon tawagar Brazil, wanda yanzu ke taka leda a Paris St Germain da aikata zamba da cin hanci.
Za a fara sauraren kakar ranar 17 ga watan Oktoba, kenan wata daya saura a fara gasar kofin duniya a Qatar a bana.
Wasu fitattun mutane suna daga cikin wadanda za a gurfanar.

Asalin hoton, Reuters
- Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin 'yan wasa
Mai horas da Barcelona Xavi ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba kungiyar ta iya dawo da Lionel Messi ba a halin da ake ciki kasancewar dan wasan na da kwantaragi da Paris St-Germain, sai dai ya ce ba a san yadda hali zai yi ba a nan gaba.(Goal)
Mai tsaron raga na kungiyar Leicester City, Kasper Schmeichel ya amince ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Nice da ke Faransa, sai dai har yanzu ba a kammala amincewa da batun ba kasancewar har yanzu Leicester din ba ta samu wanda zai maye gurbinsa ba. (L'Equipe - in French)
Shugaban Leicester City, Aiyawatt Srivaddhanaprabha ya ce ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta nuna sha’awar daukar dan wasa Youri Tielemans duk kuwa da cewa kwantaraginsa da kungiyar za ta kare ne a kaka mai kamawa. (Metro)
Everton na son ganin ta dauko dan wasan Sporting Lisbon mai shekara 23 Ruben Vinagre, wanda ya rinka yin wasa a kungiyar Wolves. (Liverpool Echo)
Southampton ta nuna aniyarta ta dauko dan wasan Manchester City mai shekara 19 Sam Edozie, wanda ake sa ran zai tafi Bayer Leverkusen. (Mail)

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Wolves, Raul Jimenez zai yi jinyar makonni
Dan kwallon Wolves, Raul Jimenez zai yi jinyar makonni bayan raunin da ya ji a lokacin wasannin sada zumunta don tunkarar kakar bana.
Jimenez mai shekara 31 sai sauya shi aka yi a karawar da Wolves ta doke Besiktas 3-0.
Wolves za ta fara gasar Premier League da Leeds United ranar 6 ga watan Agusta.

Asalin hoton, Getty Images
Nottingham Forest na shirin daukar wani mai buga wasa daga tsakiya
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin 'yan wasa
Juventus dai za ta sanya ido kan Werner ko kuma dan wasan Manchester United, Anthony Martial idan ta gaza dauko dan wasa Alvaro Morata daga Atletico Madrid. (Sky Sports)
Yunkurin kungiyar Tottenham na dauko dan wasa Weston McKennie zai iya cin karo da tangarda bayan da abokin wasansa da suke kungiyar Juventus Paul Pogba ya samu rauni a gwiwa.(Mail)
- Rangnick 'ba ya jin dadin' aiki a Man Utd
- Lukaku ba ya son komawa AC Milan, Arsenal na zawarcin Hickey
- Magoya bayan Man Utd sun yi zanga-zangar 'lumana'
Chelsea ta fara mayar da hankalinta kan dauko mai tsaron baya na Inter Milan Denzel Dumfries bayan da yunkurinta na sayo Jules Kounde daga Sevillake neman ya ci tura. (Evening Standard)

Asalin hoton, Getty Images
- Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
West Ham ta sayi Gianluca Scamacca daga Sassuuolo
West Ham ta dauki Gianluca Scamacca daga Sassuolo kan fam miliyan 30.5.
Scamacca zai koma buga gasar Premier League kan yarjejeniyar kaka biyar da cewar za a iya tsawaitata.
Mai shekara 23 shi ne na biyu a yawan zura kwallaye a raga a gasar Serie A da aka kammala mai 16 a raga cikin wasa 36.

Asalin hoton, PA Media
- Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
'Yar wasan Ingila, Dina Asher-Smith ta janye daga gasar Commonwealth Games sakamakon raunin da ta yi.
Asher-Smith ta ji raunin ne a wasannin gasar wasan tsalle tsalle da guje guje ta duniya a Eugene, Oregon.
Ta lashe tagulla a tseren mita 200 a gasar da aka kammala a karshen mako.
Fulham ta dauki Kevin Mbabu daga Wolsburg
Fulham ta kammala daukar dan wasan tawagar Switzerland, Kevin Mbabu daga Wolfsburg kan yarjejeniyar kaka uku.
Mai shekara 27 wanda ya buga wasa uku a Premier League a Newcastle United,ya koma Craven Cottage kan fam miliyan 6.4.
Mbabu ya koma Wolfsburg daga Young Boys a 2019 ya kuma buga wa kungiyar da ke Bundesliga wasa 66.
Mbabu ya yiwa Switzerland wasa 22, tun bayan da ya fara taka mata leda a 2018.

Asalin hoton, Getty Images
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin 'yan wasa
Dan wasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong zai iya zuwa Chelsea ne kadai idan ya bar kungiyarsa ta Barcelona, sai dai Chelsea din ba za ta iya biyan shi kudin da Manchester United ke da niyyar ba shi ba idan zai koma United din.(Sport - in Spanish)
Shugaban kungiyar Atletico Madrid Enrique Cerezo ya ce bai san ko wane ne ya kirkiri jita-jitar cewa Cristiano Ronaldo zai koma kungiyar ba daga Manchester United domin a cewar sa a halin yanzu wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. (El Partidazo de COPE, via Eurosport)
Newcastle United na nuna sha’awarta ta dauko dan wasan Chelsea dan asalin kasar Jamus Timo Werner mai shekara 26. (Christian Falk, head of football at Bild)

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta dauki matashi Mathys Tel daga Rennes
Bayern Munich ta kammala daukar matashi mai shekara 17, Mathys Tel daga Rennes.
Tel, wanda ya yi wa tawagar Faransa kyaftin ta matsa 'yan shekara 17 a lokacin da suka lashe kofin nahiyar Turai, shi ne na biyar da Bayern ta dauka a kakar nan.
Ya buga wa Rennes karawa 10 a babbar gasar tamaula ta Faransa da aka kammala.
Daraktan wasannin Bayern Hasan Salihamidzic ya ce ''Tel daya ne daga fitattun matasa a taka leda a Turai'' kuma ''kungiyoyi da dama na son daukar dan kwallon.''
Tuni Bayern ta dauki Matthijs de Ligt da Sadio Mane da Ryan Gravenberch da kuma Noussair Mazraoui.
Haka kuma Robert Lewandowski ya bar Jamus ya koma Barcelona da taka leda a kakar nan.

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ta kammala sayen mai tsaron baya, Nordi Mukiele daga RB Leipzig kan yarjejeniyar kaka biyar.
Dan kwallon tawagar Faransa ya yi kaka hudu yana taka leda a Jamus, bayan da ya koma can daga Montpellier,.
Ya kuma taimaka da Leipzig ta kai karawar daf da karshe a Europa League da kuma daukar German Cup a kakar da ta wuce..
Ya buga wasa 145 a kungiyar da ke buga Bundesliga da cin kwallo 10 da bayar da 11 aka zura a raga.

Asalin hoton, Getty Images
Ingila ta kai wasan karshe a babbar gasa karon farko bayan shekara 13
Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta yi nasara a kan Sweden a jiya a filin wasa na Bramall Lane.
Karon farko da Ingila ta kai wasan karshe a babbar gasa tun bayan shekara 113.
Wannan shi ne wasa na hudu da Ingila ta yi nasara a kan Sweden a fafatawa 27 da suka yi a tksanainsu.
Tawagar kwallon kafa ta mata ta Sweden ita ce ta biyu a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a duniya, bayan Amurka ta daya.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Euro 2022

Asalin hoton, Euro 2022
Rangers ta dauki dan wasan Turkiya mai tsaron baya Ridvan Yilmaz kan kwantiragin kaka biyar daga kungiyar Besiktas kan kudi sama da fam miliyan biyar har da karin tsarabe-tsarabe.
Mai shekara 21 ya yi wasa 72 a Besiktas, bayan da ya fara kungiyar tun daga matashi da ya yi wa tawagar kasar karawa shida.
Yilmaz ya lashe babbar gasar tamaula ta Turkiya a 2020/21 a Besiktas, zai maye gurbin Calvin Bassey, wanda ta sayarwa da Ajax kan sama da fam miliyan 19.
Haka kuma kungiyar ta dauki Ben Davies daga Liverpool da kuma dan kwallon tawagar Scotland, John Souttar daga Hearts.

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta raba gari da Ramsey
Aaron Ramsey ya bar Juventus, bayan da kungiyar mai buga Serie A ta sanar da soke sauran yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
A makon jiya ne mai shekara 31 ya bar sansanin Juventus a Amurka da ta je buga wasannin sada zumunta.
Ramsey ya koma Juventus a 2019, tsohon dan kwallon Arsenal ya dunga karbar albashin fam 400,000 duk mako.
Sai dai dan kwwallon ya buga rabin kakar da ta wuce a Rangers, waddda ya yi wa wasannin aro.

Asalin hoton, Getty Images
Suarez zai sake komawa kungiyarsa Nacional wadda tun yana da kuruciya
Tsohon dan kwallon Liverpool da Barcelona, Luis Suarez ya ce ya amaince zai koma kungiyarsa ta Nacional, wadda ya fara tun yana da kuruciya a Uruguay.
Mai shekara 35, bai da yarjejeniya kawo yanzu tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Atletico Madrid a karshen kakar da aka kammala.
Ana sa ran Suarez zai koma Nacional a kalla lokacin da za a fara gasar kofin duniya a cikin watan Nuwamba.

Asalin hoton, Getty Images
Barkanmu da kasancewa
Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni da yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ke gudana a rana irin ta yau.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin da fatan za ku kasance da BBC Hausa a koda yaushe.
Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter.
