Abin da ba ku sani ba kan babbar kasuwar kifi ta Hadejia
An wallafa
Kasuwar kifi ta Hadejia na daga manyan kasuwannin kifi a arewacin Najeriya, wadda take samun kifi daga sassa daban-daban kuma ake kai kifin duk fadin kasar.
Daruruwan mutane ne ke hada-hada a kasuwar a kowace rana, inda ta zame musu wata babbar hanyar dogaro da kai.
To sai dai kasuwar na fama da babbar matsalar karancin ruwa da rashin ingantacciyar tsaftar kifi da ta muhalli.
Wasu 'yan kasuwar sun dora alhakin hakan a kan gwamnati, to amma gwamnatin na cewa tana bakin kokarinta wajen magance matsalar da kasuwar ke fuskanta.