'Ya'yan awakin da ke sa likitoci farin-ciki

Bayanan bidiyo, 'Ya'yan awakin da ke sa likitoci farin-ciki
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Yanayi na galabaita da surutu da ake fama da shi a asibitoci yana yin tasiri kan ma'aikata da majinyata.

Sai dai wani asibiti a Amurka ya dauki matakin mu'amala da 'ya'yan awaki masu kyawu a matsayin hanyar rage damuwar da ke tsakanin ma'aikata da majiyyata.

Ana kai wa likitoci da ma'aikatan jinya 'ya'yan awakin inda suke rungumarsu domin huce takaici da yanayi na galabaita.