Abin da ya sa ake kyamar bakaken-fatar Amurka saboda salon gashin kansu

Bayanan bidiyo, Abin da ya sa ake kyamar bakaken-fatar Amurka saboda salon gashin kansu
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Bakaken-fatar Amurka suna ci gaba da rungumar salon gyara gashin da Allah ya halicce su da shi. Sai dai suna fuskantar tsangwama a makarantu da kamfanoni a fadin Amurka.

An kori kananan yara daga makarantu saboda salon gashin kansu, yayin da manya kuma ke fuskantar kora daga wuraren ayyukansu.

Wakiliyar BBC a Amurka, Chelsea Bailey, ta bibiyi silar wanna nuna wariya da ta zama ruwan-dare da kuma kokarin da ake yi wajen yin watsi da wannan kyama: