Zaidu Sanusi: Yadda za ku gane dillalan kwallon kafa na bogi

Bayanan bidiyo, Bidiyon hira da Zaidu Sanusi
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Dan wasan kwallon kafa na Najeriya da ke yi wa kungiyar kwallon kafa ta FC Porto wasa, Zaidu Sanusi, ya bayyana hanyoyin da masu sha'awar kwallon kafa za su gane dillalan bogi.

Zaidu Sanusi ya shaida wa BBC Hausa cewa duk wani dillali da zai nemi kudi wajen mutum kafin ya ba shi damar haduwa da turawa masu kungiyoyin kwallo na bogi.

"A lokacin da na je Turai ko sisi ban ba da ba, bature ne ya turo min duk takardu da ake bukata kuma na tafi Turai domin shi bature baya son kudinka," in ji shi.

Zaidu ya ce ya taba fuskantar wariyar launin fata a kasar Portugal amma bai damu ba saboda kudi yaje nema kuma tunda yana aikinsa na kudi bai damu ba.

Ya kara da cewa Hukumar Kwallon kafa ta FIFA tana kokari wajen hana wariyar launin fata.

Tuni dan wasan kwallon kafan ya ya fara jin yaren Portugal.

Har wa yau, ya ce ya na sha'awar ganin matasa daga Najeriya su na ci gaba a fagen kwallon kafa.

Zaidu yace yana farin ciki sosai da gudunmawar da ya ke baiwa kungiyar sa ta FC Porto kuma yana burin ya sake cin kofi da yawa.

A Najeriya kuwa, Zaidu ya ce yana da burin ganin ya ciwa kasar kwallaye da dama nan gaba.