Hotunan gasar Premier ta Ingila

An wallafa

Arsenal 1-0 West Ham: Filin wasa na Emirates ne ya karbi bakuncin karawar 'yan gari daya tsakanin Arsenal wacce ke haskakawa da kuma West Ham wacce ba ta taka rawa sosai.

Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Arsenal 1-0 West Ham: Filin wasa na Emirates ne ya karbi bakuncin karawar 'yan gari daya tsakanin Arsenal wacce ke haskakawa da kuma West Ham wacce ba ta taka rawa sosai.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, An kai ruwa rana sosai kafin Arsenal ta kwaci kanta a wannan wasa, inda ana saura minti biyu a tashi, Alex Song ya zira kwallo dayan da ta raba gardama.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Blackburn 1-2 Chelsea: Blackburn ce ta fara zira kwallo a minti na 22 da fara wasa ta hannun Benjani.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Kafin daga bisani Nicolas Anelka ya ramawa Chelsea, tare da taimakon Didier Drogba.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Chelsea ba su taka rawa ta azo a gani ba, amma sun samu nasarar jefa kwallo ta biyu ta hannun Ivanovic ana saura minti shida a tashi.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Manchester United 2-0 Tottenham: Spurs sun zubar da damarmaki, kafin Nemanja Vidic ya fara zirawa United kwallon farko, sannan daga bisani Nani ya ci ta biyu.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Wolves 2-1 Manchester City: Emmanuel Adebayor ne ya fara zirawa City kwallo ta hanyar bugun Fanareti a minti na 23.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Wolves sun karbe ragamar wasan a minti na 57, bayanda 'yan bayan City suka kasa cire kwallon da aka bugo, abinda ya baiwa David Edward damar zira kwallon a ragar City.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Kociyan City Roberto Mancini na tsaka mai wuya bayanda aka doke su sau biyu a jere.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Newcastle 5-1 Sunderland: Newcastle ta casa abokiyar hamayyar ta Sunderland da ci 5-1, inda Keven Nolan ya zira kwallaye uku.
Hotunan gasar Premier ta Ingila
Bayanan hoto, Bolton 0-1Liverpool: Liverpool na ci gaba da farfadowa bayan da ta doke Bolton da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Reebok.