Zaben kasar Brazil cikin hotuna

An wallafa

Magoya bayan Dilma Rousseff suna murnar nasarar da ta samu ta lashe zaben Brazil a kan titunan kasar.

Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Magoya bayan Dilma Rousseff suna murnar nasarar da ta samu ta lashe zaben Brazil a kan titunan kasar.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Mis Rousseff, 'yar shekaru 62, ba a taba zabarta kan wani mukami ba. Za ta gaji shugaba Lula wanda zai sauka bayan shafe wa'adi biyu kan karagar mulki, abinda ya haifar masa da farin jini a wurin jama'ar kasar.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Ta kada Jose Serra na jam'iyyar Social Democratic Party a zagaye na biyu. Kwararran dan siyasa ne, kuma ya yi takara da shugaba Lula a shekara ta 2002.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Babbar kotun zabe ta kasa ta bayyana cewa Rousseff ta lashe kashi 56 cikin dari yayinda abokin hamayyarta ya lashe kashi 44.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, A jawabin da ta gabatar jim kadan bayan samun nasararta, Mis Rousseff ta ce burinta shi ne na fitar da 'yan kasar miliyan ashirin daga kangin talauci.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Shugaba Lula ne ya zabi Rousseff ta gaje shi. Zai bar ofis a watan Janairu, kiyasi ya nuna farin jininsa ya kai kashi 80 cikin dari, sakamakon yadda ya farfado da tattalin arzikin kasar.
Zaben kasar Brazil cikin hotuna
Bayanan hoto, Duka Mis Rousseff da Jose Serra sun nemi goyon bayan jam'iyyar Green Party, wacce dan takararta Marina Silva ya samu kuri'u miliyan 20 a zagayen farko, amma ya ki goyawa kowannensu baya.