Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi

An wallafa

Jama'a da dama ne suka fito kan tituna a birnin Rangoon na kasar Burma, bayanda aka sako jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi, daga daurin talala.

Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, Jama'a da dama ne suka fito kan tituna a birnin Rangoon na kasar Burma, bayanda aka sako jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi, daga daurin talala.
Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, Mis Suu Kyi ta shafe shekaru 17 tana zaman talala, da kuma kusan shekaru 21 a daure saboda tana nuna adawa da gwamnatin mulkin sojin kasar.
Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, An shiga rudani a cikin birnin, bayanda magoya bayanta suka taru domin jiran fitowarta. Yayinda jami'an tsaron kasar Burma sun ja daga, wasunsu dauke da tiyagas.
Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, Sai dai magoya bayanta da suka taru a hedkwatar jam'iyyarta ta National League for Democracy (NLD), sun fara murna tun kafin a tabbatar da labarin sakin na ta.
Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, Bayanda labarin ya tabbata, Aung San Suu Kyi ta bayyana a wajen gidan, inda ta shafe shekaru da dama a tsare ba tare da samun damar ganawa da jama'a ba.
Jama'a sun yi dandazo a gidan Aung San Suu Kyi
Bayanan hoto, A birnin Delhi na kasar India, jama'a da dama suka yi kaura daga Burma, sun fito kan tituna domin nuna farin cikinsu.