Hotuna: Zanga- zanga a Libya

An wallafa

A karo na farko, zanga-zangar da ake yi ta kin jinin gwamnati a Libya ta watsu zuwa tsakiyar babban birnin kasar, Tarabulus, wato Tripoli.

A karo na farko, zanga-zangar da ake yi ta kin jinin gwamnati a Libya ta watsu zuwa tsakiyar babban birnin kasar, Tarabulus, wato Tripoli.
Bayanan hoto, A karo na farko, zanga-zangar da ake yi ta kin jinin gwamnati a Libya ta watsu zuwa tsakiyar babban birnin kasar, Tarabulus, wato Tripoli.
Rahotanni sun bayyana cewa dimbin masu zanga-zanga sun kwashe sa’o’i da dama a titunan birnin a daren jiya Lahadi suna kiran a kawar da gwamnatin Kanar Muammar Gaddafi.
Bayanan hoto, Rahotanni sun bayyana cewa dimbin masu zanga-zanga sun kwashe sa’o’i da dama a titunan birnin a daren jiya Lahadi suna kiran a kawar da gwamnatin Kanar Muammar Gaddafi.
An kuma ba da rahoton jin karar bindigogi da kona gine-ginen ciki har da ofisoshin 'yansanda.
Bayanan hoto, An kuma ba da rahoton jin karar bindigogi da kona gine-ginen ciki har da ofisoshin 'yansanda.
Wannan ya biyo bayan karbe iko da birnin Benghazi ne da rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun yi.
Bayanan hoto, Wannan ya biyo bayan karbe iko da birnin Benghazi ne da rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun yi.
Daya daga cikin 'ya'yan Kanar Gaddafi, Saif al-Islam al-Gaddafi, ya yi jawabi a gidan talabijin na kasar yana alkawarin shiga tattaunawa nan da sa'o'i arba'in da takwas, da nufin gyaran kundin tsarin mulki, wanda ya ce zai haifar da sauye-sauyen siyasa.
Bayanan hoto, Daya daga cikin 'ya'yan Kanar Gaddafi, Saif al-Islam al-Gaddafi, ya yi jawabi a gidan talabijin na kasar yana alkawarin shiga tattaunawa nan da sa'o'i arba'in da takwas, da nufin gyaran kundin tsarin mulki, wanda ya ce zai haifar da sauye-sauyen siyasa.