Musafahar kafa tarihi

An wallafa

Ana kallon musafahar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da tsohon jagoran kungiyar IRA Martin McGuiness a matsayin wani abu da ya kafa tarihi. To ga hotuna nan na wadansu lokutan da aka yi musafahar da ta kafa tarihi.

Shugaba Richard Nixon da Jagora Mao Zedong
Bayanan hoto, A wata ziyara mai matukar muhimmanci zuwa China a watan Fabrairun 1972, Shugaba Richard Nixon na Amurka ya yi musafaha da jagoran Jam'iyyar Kwaminis Mao Zedong bayan kasashen biyu sun yi shekaru ba sa ga-maciji da juna.
Shugaba Anwar Sadat yana musafaha da Firayim Minista Menachem Begin
Bayanan hoto, Firayim Ministan Isra'ila Menachem Begin ya marabci Shugaba Anwar Sadat na Masar da musafaha lokacin da Sadat din ya ziyarci Isra'ila a watan Nuwamban 1977—ita ce ziyara ta farko da wani shugaban kasar Larabawa ya kai. Watanni 16 bayan nan kuma aka yi wata musafahar ta kulla yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kaow karshen yake-yaken da aka kwashe shekaru 30 ana yi.
Shugaba Mikhail Gorbachev da Shugaba Ronald Reagan
Bayanan hoto, Manyan tarurruka tsakanin Shugaba Mikhail Gorbachev na Tarayyar Soviet da Shugaba Ronald Reagan na Amurka sun bude kofar wani sabon zamani a dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu. A Geneva aka yi na farko a cikin wadannan tarurrukan a watan Nuwamban 1985. A wannan hoton ana ganin shugabannin biyu a Fadar Kremlin a watan Yunin 1988, kafin su fara babban taronsu na karshe.
FW de Klerk da Nelson Mandela
Bayanan hoto, Shugaba FW de Klerk da Nelson Mandela - wanda ya fito daga gidan jarun watanni uku kafin wancan lokacin - suna musafaha a Cape Town, Afirka ta Kudu, ranar 4 ga watan Mayun 1990. A lokacin ne suka bayar da sanarwar wata yarjejeniya ta tattauna yadda za a kawo karshen mulkin tsiraru farar fata. Shekaru hudu bayan nan kuma, Mista Mandela ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci Afirka ta Kudu.
 Yitzhak Rabin (a hagu) da Yasser Arafat
Bayanan hoto, Firayim Minista Yitzhak Rabin na Isra'ila (a hagu) da Jagoran Falasdinawa Yasser Arafat suna musafaha a fadar gwamnatin Amurka ta White House ranar 13 ga watan Satumba, shekara ta 1993. Wannan ne karo na farko da mutanen biyu, wadanda kafin nan ba sa ga-maciji da juna, suka yi musafaha a bainar jama'a. Da wannan musafaha aka rattaba hannu a kan Yarjejeniyar Samar da Zaman Lafiya Tsakanin Larabawa da Isra'ila.
Tony Blair da Muammar Gaddafi
Bayanan hoto, Yayin wata ziyara da ya kai Libya, Firayim Ministan Burtaniya Tony Blair yana musafaha da Kanar Muammar Gaddafi. Bayan musafahar a wani tanti ranar 25 ga watan Maris na 2004, Mista Blair ya ce akwai fatan samun "sabuwar kyakkayawar dangantaka".
Robert Mugabe da Morgan Tsvangirai
Bayanan hoto, Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe da jagoran 'yan adawa a wancan lokacin Morgan Tsvangirai sun amince su tattauna a kan makomar siyasar kasar, yayin da suka yi musafaha a wurin ganawar da suka yi a Harare, babban birnin kasar a watan Yulin 2008. Wannan ne ya kai ga yarjejeniyar da aka kulla mai cike da tarihi watanni biyu bayan nan.
Sarauniya Elizabeth ta Biyu ta yi musafaha da Mataimakin Firimiyan Ireland ta Arewa kuma tsohon kwamandan IRA Martin McGuiness a Belfast ranar 27 ga watan Yuni, a wani abin da ake ganin lokaci ne mai matukar muhimmanci a shirin tabbatar da zaman lafiya a yankin Ireland ta Arewa.
Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth ta Biyu ta yi musafaha da Mataimakin Firimiyan Ireland ta Arewa kuma tsohon kwamandan IRA Martin McGuiness a Belfast ranar 27 ga watan Yuni, a wani abin da ake ganin lokaci ne mai matukar muhimmanci a shirin tabbatar da zaman lafiya a yankin Ireland ta Arewa.