Zanga-zanga a Ukraine

An wallafa

'Yan sanda a Ukraine sun kaddamar da hari kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Yanukovych, lamarin da ya kashe mutane 25.

'Yan sanda a Ukraine sun kaddamar da hari kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Yanukovych, lamarin da ya kashe mutane 25.
Bayanan hoto, 'Yan sanda a Ukraine sun kaddamar da hari kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Yanukovych, lamarin da ya kashe mutane 25.
Ana kokarin kawar da abubuwan da masu zanga-zanga su ka kafa, inda Shugaba Yanukovych ya zargi shugabannin 'yan sanda da janyo tarzoma.
Bayanan hoto, Ana kokarin kawar da abubuwan da masu zanga-zanga su ka kafa, inda Shugaba Yanukovych ya zargi shugabannin 'yan sanda da janyo tarzoma.
Bayan an kasa sansantawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa, shugaban ya bukaci jagororin 'yan adawa su nisanta kansu da masu tsatsauran ra'ayi.
Bayanan hoto, Bayan an kasa sansantawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa, shugaban ya bukaci jagororin 'yan adawa su nisanta kansu da masu tsatsauran ra'ayi.
Masu rajin kare hakkin bil adama sun ce gwamnati ce ta janyo tashin hankalin.
Bayanan hoto, Masu rajin kare hakkin bil adama sun ce gwamnati ce ta janyo tashin hankalin.
Dakarun gwamnati sun kwace iko da babban dandalin birnin Kiev a karon farko tun a watan Disamba.
Bayanan hoto, Dakarun gwamnati sun kwace iko da babban dandalin birnin Kiev a karon farko tun a watan Disamba.
'Yan sanda sun kaddamar da hari a dandalin Independence inda suka bankawa tantunan 'yan adawa wuta.
Bayanan hoto, 'Yan sanda sun kaddamar da hari a dandalin Independence inda suka bankawa tantunan 'yan adawa wuta.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta ce akalla mutane 25 ne suka mutu a bangaren 'yan adawa da kuma jami'an tsaro.
Bayanan hoto, Ma'aikatar kiwon lafiya ta ce akalla mutane 25 ne suka mutu a bangaren 'yan adawa da kuma jami'an tsaro.
Mutane da dama sun samu raunuka a cikin kwanakin da aka shafe ana bata kashi.
Bayanan hoto, Mutane da dama sun samu raunuka a cikin kwanakin da aka shafe ana bata kashi.
An soma zanga-zanga a karshen watan Nuwamba, lokacin da Shugaba Viktor Yanukovych ya ki amince da kulla yarjejeniya da kungiyar tarayyar turai - EU.
Bayanan hoto, An soma zanga-zanga a karshen watan Nuwamba, lokacin da Shugaba Viktor Yanukovych ya ki amince da kulla yarjejeniya da kungiyar tarayyar turai - EU.
Rikici ya barke a wajen ginin majalisar dokokin kasar.
Bayanan hoto, Rikici ya barke a wajen ginin majalisar dokokin kasar.