Daruruwan yara sun zama marayu a wasu kasashen Afrika sakamakon cutar Ebola da ta kashe iyayensu.
Bayanan hoto, John dan shekaru biyar daga gundumar Lofa a Liberia, cutar Ebola ce ta kashe iyayensa. Lokacin da suka mutu, babu wanda ya nuna sha'awar daukansa domin kula da shi.
Bayanan hoto, A garin Bomi na Liberia, Maiatta mai shekaru 16 da Jenneh mai shekaru 12 da Musa mai shekaru biyar da Larmie 'yar shekara daya da kuma Hawa 'yar watanni shida su ne ka dai suka rage a gidansa saboda illar cutar Ebola.
Bayanan hoto, A wasu lokuta kungiyoyin coci da mutanen gari ne ke ciyar da Musa da sauran 'yan uwansa saboda maraici.
Bayanan hoto, Har yanzu a garin Bomi, Pascaline mai shekaru 14 da Naomi 'yar shekaru 12 da Yonger 'yar shekaru 11 da kuma Blessing 'yar shekaru biyu suna zaune a gida babu iyaye.
Bayanan hoto, Babbar yarsu Fatu, mai shekaru 28 ta ce mahaifinsu ne ya soma kamuwa da cutar Ebola. Sannan mahaifiyarsu ta rasu bayan kwanaki 14 kafin karamin kaninsu ya ce ga garinku.