Zanga-zanga kan cin hanci a Nigeria

An wallafa

A yau Litinin ne wasu tarin matasa maza da mata ke jerin gwano zuwa fadar shugaban Najeriya watau Aso Villa.

zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Tarin matasa rike da kwalaye da ke dauke da sakonni kan cin hanci a rashawa.Inda suka ce suna goyon bayan matakin Shugaba Buhari na yaki da cin hanci da masu karbar rashawa.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Matasa kan hanyar su zuwa fadar shugaban kasa, Aso Villa. Sun ce sun gaji da masu sama da fadi da dukiyar 'yan Nigeria.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun bi kan titin babban birnin Najeriya, Abuja inda suka ta wake-wake na neman kawar da rashawa.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Jerin gwanon ya biyo bayan wata ziyarar da wasu manyan shugabannin kasar suka kai wa Shugaba Buharin, inda suka bukace shi da ya mayar da hankali ga ayyukan ci gaban kasa.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Suna dauke da rubuce-rubuce da ke nuna kyamar cin hanci da almundahana da dukiyar kasa. Masu zanga-zangar ce sun gaji da wannan abu da ke mayar da Nigeria baya.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Kungiyar ta bukaci shugaba Buhari ya binciki zargin kwashe kudaden gwamnati da aka yi a shekarun baya da aka yi a karkashin gwamnatin da ta bar mulki ba.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Tun da safe masu zanga-zangar suka soma taruwa a Unity Fountain da ke Abuja domin yin maci zuwa fadar Aso Rock.
zanga-zangar Abuja
Bayanan hoto, Cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan da ke janyo wa Nigeria koma baya a fannonin daba-daban.