Gidan Bayi a Tsibirin Gorée na Senegal

An wallafa

Albarkacin Ranar Tunawa da Cinikin Bayi da Haramta shi ta Duniya, ga wasu hotuna nan na Gidan Bayi da ke Tsibirin Gorée a Senegal.

Tsibirin Gorée daga nesa
Bayanan hoto, Tsibirin Gorée, mai nisan kilomita biyu daga tashar jiragen ruwa ta Dakar, na cikin wuraren da hukumar ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya. Kuma daya ne daga cikin wurare na farko da Turawa suka zauna a nahiyar Afirka. Tsibirin ya samo sunansa ne daga tsibirin Goeree na kasar Holland; kasasncewar Turawan Holland din sun mamaye tsibirin a shekarar 1588. Kafin nan, Turawan kasar Portugal sun zauna a tsibirin a shekarar 1444. Wannan hoton na nuna yadda ake iya hango tsibi Gorée daga karamin jirgin ruwan da ke tasowa daga tashar jiragen ruwa ta Dakar.
Kofar shiga Gidan Bayi na Tsibirin Gorée
Bayanan hoto, "Gidan Bayi" na tsibirin Gorée, ko "Maison des Esclaves" a Faransanci, na cikin wuraren tarihi da suka sanya tsibirin Gorée ya shahara. 'Yan yawon bude ido da dama ne dai ke kai ziyara tsibirin, musamman ma gidan, don ganin abubuwan tarihi na bauta, ko da yake wadansu manazarta suna tababa a kan yawan bayin da aka dauka daga tsibirin zuwa nahiyoyin Turai da Amurka. Wannan hoto na nuna kofar shiga Gidan na Bayi, kuma a cewar shugabansa na farko tun bayan mayar da wurin gidan adana kayan tairihi, Boubacar Joseph Ndiaye, bayi fiye da miliyan daya sun wuce ta gidan.
Benen Turawa a Gidan Bayi na Tsibirin Gorée
Bayanan hoto, Mutum na shiga Gidan Bayi na Gorée zai fuskanci wadannan matattakala. A cewar masu kewayawa da 'yan yawon bude ido, a wannan bene Turawa masu kula da bayin suka zauna, yayin da ake ajiye bayin a kananan dakunan da ke kasan benen.
Dakin ramammun bayi
Bayanan hoto, Wannan daki daura yake da matattakalar benen Turawa a Gidan Bayi na Gorée daga gafen hagu. A nan ake ajiye bayin da ba su kai yadda ake so ba, ana ciyar da su har sai sun kara kiba.
Gida mai siffar jirgin ruwa don gwada juriyar bayi
Bayanan hoto, Idan bayi suka koshi suka kai ajin da ake bukata, sai a kawo wannan gida da ake iya gani su yi wata uku. An yi gidan ne da siffar jirgin ruwa don a gwada dauriyarsu idan aka shiga teku. Sai wanda ya kai labari a wannan gida ake dorawa a jirgin ruwa don tafiya da shi zuwa Turai ko Amurka.
Dakin mata da 'yan mata a Gidan Bayi na Gorée
Bayanan hoto, A wannan daki ake ajiye mata. A gaba-gaban dakin akwai wani dutse mai fadi wanda a kan shi matan suke wanka. Ba a barin mata da 'ya'yansu, kuma yara mata kanana suna da nasu dakin daban.
Babban dakin ajiye bayi
Bayanan hoto, Wannan ne babban dakin ajiye bayi na Gidan Bayi na Tsibirin Gorée.
Dakin yara a Gidan Bayi na Gorée
Bayanan hoto, A wannan dan tsukun dakin ne kuma ake ajiye kananan yara. A cewar masu kula da gidan tarihin, akalla yara 40 ake ajiyewa a nan.
Dakin horo a Gidan Bayi na na Gorée
Bayanan hoto, Duk bawan/baiwar da ya/ta yi taurin kai wannan daki ake kawo su. Shi ma dai daura yake da matattakalar benen Turawa, amma mutum komai kankantarsa ba zai iya mikewa tsaye ko kwanciya a ciki ba; sai dai ya zauna a takure ko ya tsugunna.
Gidan nas-nas masu karbar haihuwa da kula da jarirai a Tsibirin Gorée
Bayanan hoto, Idan wata baiwa mai juna-biyu za ta haihu, akwai nas-nas da ke kula da ita su karbi haihuwar. Bayan ta haihu sai a mayar da ita Gidan Bayi jaririn kuma su ci gaba da kula da shi har sai ya kai shekara uku. Wannan shi ne gidan da nas-nas din suka zauna.
Kofar Karshe, daga ke ba dawowa.
Bayanan hoto, Kofar Karshe: Daga wannan kofa da ake gani a wannan hoto, wacce ke kuryar Gidan Bayi, ba dawowa. Daga bakin ruwa ake diban bayin a kwale-kwale a kai su manyan jiragen ruwan da ke can cikin teku. Wanda ya kokarin gudu ta hanyar fadawa teku, mutuwa zai yi, wanda kuma ya ki shiga jirgi harbe shi ake yi. Sai dai kuma masana tarihi sun yi sabani a kan ko don cinikin bayi zalla Turawa suka yi amfani da Tsibirin Gorée, ko kuma cinikin bayin wani dan karamin bangare ne na kayan da aka yi safara zuwa Turai da Amurka.
Mutum-mutumin 'yanci daga bauta
Bayanan hoto, Mutum-mutumi na murnar samun 'yanci daga bauta a kusa da Gidan Bayi na Gorée. A shekara ta 2006 aka ba da shi ga Gidan Bayin.