Hotunan birnin Moscow da ba a saba gani ba, wadanda aka dauka da jirgi marar matuki.
Bayanan hoto, Mai daukan hoto Amos Chapple ya tattara hotunan Moscow da ya dauka daga sararin samaniya, wadanda ba a saba gani ba, inda ya yi amfani da abun daukan hoton da aka daura kan jirgi marar matuki.Hakan kuma ya sa mai daukan hoton wanda dan asalin kasar New Zealand ne, ya samu damar samun hotuna na gani na fada. Wannan hoton wani Otal ne mai suna Ukraina wanda aka dauka gabda faduwar rana.
Bayanan hoto, Hotunan sun fito da kasaitattun tsarin gine-gine, da butum-bumin 'Worker and Kolkhoz' da Vera Mukhina ya sassaka domin bikin baje koli na Paris a shekarar 1937.
Bayanan hoto, Wani tsarin gini mai daukan ido shi ma domin har kusan gajimari ya mike, wanda aka yi domin masu keta hazo tun shekarar 1964.
Bayanan hoto, Wani gini da ya ja hankalin Chapple shi ne ginin Kremlin, wanda ya dauki hoton sa daga saman dandalin 'Red Square'. Ya ce, "Na kosa in dauki hoton, saboda haka na yi kwana biyu ina neman wuri mai kyau, inda zan iya boye wa 'yan sanda'
Bayanan hoto, "Sai da na jira hayaniyar motoci domin su toshe karar jirgi marar matuki lokacin da ya ke tashi sama.
Bayanan hoto, Sauran gine-gine basu yi wuyan dauka ba, kamar jami'ar jihar Moscow wacce aka nuno a nan kusa da rafin Moskva.
Bayanan hoto, Majami'ar Cathedral of Christ wacce ita ma take gefen rafin Moskva, ya fito a hoton tare da hasken ranar hantsi.