Mahajjata sun soma aikin hajjin 2015

An wallafa

Mutane fiye da miliyan biyu daga dukkan sassan duniya ne suka soma gudanar da ibada domin aikin Hajji na bana a kasar Saudiyya.

muna
Bayanan hoto, Yanzu haka dai bayanai sun ce mahajjata miliyan daya da dubu dari hudu sun riga sun isa Muna.Maniyata daga kasar Indonesia su ne suka fi na kowacce kasa yawa inda suka kai su 168,000.
Muna
Bayanan hoto, An tanadi rumfuna kimanin dubu 160 wadanda wuta ba za ta iya cin su ba a Muna a Saudiyya.
muna
Bayanan hoto, A bana, hukumomi a Saudiya sun yi gargadin za a iya samun yanayi mai zafi da kuma ruwan sama mai dauke da iska mai karfin gaske.
muna
Bayanan hoto, Aikin Hajji dai daya ne daga cikin shika-shikan musulunci, kuma bana ana sa ran mutane fiye da miliyan biyu ne za su yi wannan aikin na ibada.
muna
Bayanan hoto, Shirin aikin hajjin na bana dai ya fuskanci kalubale yayin da wani hatsari a Masallacin harami a Makka lamarin da janyo rasuwar mutane fiye da 100.