Zababbun hotuna daga nahiyar Afrika na wannan makon.
Bayanan hoto, Ana nan ana ta cece-ku-ce a hukumar kwallon kafa ta FIFA, amma kuma ga shi nan ana murza leda a wani filin wasanni da hukumar ta gina a Abuja, babban birnin Najeriya.
Bayanan hoto, An waye gari yara mata na karuwa da ilimin Ingilishi a Juba, babban birnin Sudan Ta Kudu.
Bayanan hoto, Ranar Asabar, yara kanana da basu kai shekarun yin zabe ba, sun zagaye wani mai yakin nema wa shugaban kasar Ivory Coast zabe, gabannin ranar gudanar da zaben a 25 ga watan Oktoba.
Bayanan hoto, A kasar Guinea kuma, raye-raye na murna da masu goyon bayan shugaban da ya lashe zabe.
Bayanan hoto, Mawakin nan Stromae na ci gaba da zagaye nahiyar Afrika, kuma wannan hoton ke nuna shi yana waka a ranar Asabar, a garin Kigali da ke kasar Rwanda, inda aka kashe mahaifinsa lokacin da aka yi kisan kare dangi.
Bayanan hoto, Ranar Litinin ne sojojin kasar Zimbabwe suka tabbatar da cewa sun dauki daidai lokacin da sojojin hadin gwiwa na kasashen Afrika watau 'Africa Standby Forces' ASF, suke aikin horo a Afrika Ta Kudu.
Bayanan hoto, Da maraice ne dubban masoya wakokin salon 'Afrobeat' suka hallara a birnin Legas da ke Najeriya, inda mawakin na kuma dan shahararren mawakin nan Fela da ya rasu, Femi Kuti ya gabatar da raye-raye da aka yi wa taken 'Felabration' domin tunawa da mahaifinsa.
Bayanan hoto, Kashe gari an samu wata mata da ta tarwatsa wasu jerin hotuna da masu zabe suka lika, domin ta cusa wa jama'a ra'ayin su zabi jamiyyar CCM, lokacin zaben kasar Tanzaniya da aka gudanar ranar 25 ga watan Oktoba.
Bayanan hoto, A birnin Dar es Salaam da ke kasar Tanzaniya, wani ya kafa tutoci uku domin nuna goyon bayan sa ga jam'iyyar adawa ta kasar, wanda suka gabatar da dan takara guda daya tal.
Bayanan hoto, Daga tsallake kuma a birnin Abidjan da ke Ivory Coast, masu takara da ke zaman kansu da kuma masu takarar da ke kan mulkin duk basu ja hankalin masu zabe ba.
Bayanan hoto, Hoto a garin Al-Damazin da ke Sudan da ke nuna dubban 'yan gudun hijira a wani sansani da ke Blue Nile.
Bayanan hoto, A wannan ranar an samu wasu masu rawa a jihar Cross Rivers da ke Najeriya, da suke raye-raye domin kadamar da sabon babban titi da aka yi a jihar.
Bayanan hoto, A nan kuma daliban makaranta ke nuna fushin su game da karin kudin makaranta a Afrika Ta Kudu, inda suka yi jerin gwano cikin jami'ar Wits da ke birnin Johannesburg.