Littafin "A game da mata"

An wallafa

About Women ko a Game da mata, wani sabon littafi ne da wata fitacciyar mai daukar hoto ta fitar Dorothy Bohm, inda ta duba rawar da mata ke takawa a cikin al'ummar.

London a shekarun 1960. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Littafin A game da mata shi ne na farko da Dorothy Bohm ta rubuta wanda ya yi duba kocokan a kan al'amuran mata.
Garin Menton na kudancin Faransa 2008. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Bohm ta yi amfani da hotunan da aka dauka tun daga karshen shekarun 1940 har zuwa yau, kuma ta yi duba a kan mata daban-daban da suka hada da matan karkara wadanda suka mayar da hankali kan aiwatar da ayyukansu na yau da kullum, da kuma matan maraya wadanda suka samu wayewa ta rayuwa.
Birnin Paris 2005. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Wani bangare na aikin ya mayar da hankali kan yadda mata ke fito wa a tallace-tallace ko a fastoci ko yadda ake amfani da butum-butumi na mata a shagunan sayar da kayayyaki.
Birnin London shekarar 2003. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Sauran bangarorin littafin sun yi duba a kan hotunan mata irin wadanda ake sa wa a wuraren idon jama'a kamar dai wannan hoton da aka dauka wanda aka sanya shi a kan titin gabashin birnin London.
Birnin Stockholm 1971. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Da take magana a kan aikin nata, Bohm ta ce "Ina samun farin ciki na ga na sanya mutane suna kallon abubuwan da a da basu cika la'akari da su ba, kuma mutane su dinga sha'awar abubuwa da suke kallo a hotuna.
Hoton Dorothy Bohm kenan tana 'yar shekara 18.
Bayanan hoto, Dorothy Bohm ta je Biritaniya a shekarar 1939 tana 'yar shekara 14 a lokacin da ta gudu saboda rikicin kungiyar Nazi a Jamus. Daga nan sai ta ci gaba da kokarin gogewa a harkar daukar hoto, ta kuma yi fice sosai a wata kungiya ta masu daukar hoto a London.
Afrika ta kudu a shekarar 1974. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, wasu daga cikin hotunan da Bohm ta fi so dai an dauke su ne a Afrika. Ta ce "Akwai wadansu da na dauke su a Afrika. Wasu mutnae a birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu sun shaida min cewa, in ba don da dan'uwana na je ba, da bamu samu damar shiga wannan sako na duniya ba."
Birnin Venice a shekarar 1986. Dorothy Bohm
Bayanan hoto, Bohm ta shaida wa BBC cewa "A dan wani lokaci, na fi son wasu hotunan fiye da wasu, na shafe shekara 75 ina aikin daukar hoto."
Titin Chapel Market na birnin London a shekarun 1960.
Bayanan hoto, Dewi Lewis, shi ne ya yi dab'in littafin "About Women" na Dorothy Bohm.