Masu askin birnin Freetown

An wallafa

Mai daukar hoto Olivia Acland, ya tara hotunan masu aski wadanda suke yi wa mazauna birnin Freetown aski a Saliyo.

Freetown barbers
Bayanan hoto, Mai daukar hoto Olivia Acland ya yi ta tara hotuna masu kala na shagunan aski da ke jere a duka titunan babban birnin Saliyo, Freetown wadanda ke cike da hada-hada. Shagon mai aski wani waje ne da mutane suke zama su huta cikin kwanciyar hankali. Yana da mahimmanci mutum ya ji shi a sake, yayinda wani ya dora masa zabira a kumatunsa ko kuma almakashi a kansa
Freetown barbers
Bayanan hoto, Mutumin dake mallakar wannan shagon askin, Ronald, ya yanke shawarar yiwa shagon irin wannan fentin, saboda yana son irin rayuwar mutanen Amurka da Burtaniya
Freetown barbers
Bayanan hoto, Mana ya kwashe shekaru 10 yana aski. Ya ce a kowacce rana yana yiwa mutane bakwai zuwa takwas aski, kuma yana samun akalla 10,000 na kudin kasar a rana daya. Cikin dariya ya fada min cewa ya san duka tsegumin da ake yi a birnin Freetown
Freetown barbers
Bayanan hoto, Arthur na da shagon aski da ya yi wa fenti kamar haka shekaru uku da suka gabata, yana son ya tabbatar da cewa shagon yana daukar hankali
Freetown barbers
Bayanan hoto, John na ziyartar shagon askin Arthur a duk mako domin ya yi aski
Freetown barbers
Bayanan hoto, Arthur ya kan yawaita sauraron rediyo idan yana aiki, ya ce hakan na taimaka masa wajen yiwa mutane aski mai kyau
Freetown barbers
Bayanan hoto, Lucy na zuwa wurin mai gyara mata gashi sau daya cikin makonni biyu, kuma tana biyan 20,000 na kudin Saliyo domin a yi mata saisayi.
Freetown barbers
Bayanan hoto, Kukklewar gashi ya zama kamar gizo abu ne da matasa suke matukar sha'awa kuma yana bukatar kulawa domin gashin ya ci gaba da yin kyau. Wannan shagon askin ne musamman ga masu irin wannan gashin.
Freetown barbers
Bayanan hoto, Mai aski Kolenzo da kuma 'yar uwarsa na hutawa a shago suna jiran kwastomomi
Freetown barbers
Bayanan hoto, Wannan mutumin na aiki ne a matsayin mai aski sannan a lokaci guda kuma soja ne a cikin rundunar sojojin fadar Shugaban Kasar. Yana yi wa wani abokin aikinsa aski a wajen fadar Shugaban Kasa.
Freetown barbers
Bayanan hoto, Wannan shagon mai askin dake gefen filin wasan Freetown na kasancewa a bude har zuwa karfe 11 na dare domin yiwa wadanda suke shiga ko kuma suke fitowa daga filin wasan