Gwamnatin kawance zata yi karko

Cameron da Clegg
Bayanan hoto, Sabon Firaministan Birtaniya David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg.
An wallafa

Sabon Pira ministan Birtaniya, David Cameron, da mataimakinsa, Nick Clegg, sun dage kan cewa gwamnatin gambizar da suka kafa a jiya, wadda ita ce ta farko a kasar a cikin shekaru da dama da suka wuce, tana da karfi, kuma za ta dore.

A wani taron manema labarai da suka kira, inda a wasu lokuta suka rika raha, tsoffin abokan hamayyar biyu sun ce kan jam'iyyunsu a hade ya ke, kuma za su yi aiki tare a duk tsawon shekaru 5 na wa'adin mulkinsu, duk da cewa akwai bambancin manufa a tsakaninsu.

Mr Cameron ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta nuna shugabanci na gari, kuma ta sa ka'idoji uku a gaba: watau 'yanci, adalci da sanin ya kamata.