Masu zanga zanaga a Thailand sun mika wuya

Masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a kasar Thailand wadanda suka hana al'amura tafiya har na tsawon makonni shida a Bangkok babban birnin kasar, sun mika wuya ga sojojin gwamnati.
A yanzu gwamnati ta sanya dokar tabaci a babban birnin, domin takaita tashin hankalin da ka iya sake barkewa.
Da yake jawabi ta gidan talabijin na kasar mai magana da yawun gwamnatin yace, a yanzu an kawo karshen akasarin tashin hankalin da ake fama da shi, kuma dokar tabacin za ta samar da tsaro ga jama'ar kasar, da ma 'yan kasashen waje.
A kalla mutane biyar aka kashe a rikici na baya-bayannan, amma yanzu shugabannin 'yan adawa da jami'an 'yan sanda sun ce ba sa so a ci gaba da asarar rayuka.
An ga hayaki yana ta tashi a birnin, bayan da aka kona gina-ginen gwamnati ciki harda kasuwar hada hadar hannayen jari ta kasar.
Harwayau masu zanga-zangar sun kai hari kan kafofin yada labarai, sannan kuma akwai rahotannin dake cewa ana ta sace sace.
Sai dai wani bangare na masu zanga-zangar sun nesanta kansu daga wannan tsagaita wuta, sannan suka yi alwashin ci gaba da fafutukar da suke yi.






















