Kungiyar kwadago zata fara yajin aiki a Barno

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto, Kungiyar kwadago zata fara yajin aiki a jihar Barno
An wallafa

A yau ne kungiyar kwadago ta kasa a jihar Barnon Najeriya zata fara yajin aikin sakamakon abinda ta bayyana na rashin biyan hakkokin ma'aikata daga bangaren gwamnatin jihar.

Kungiyar Kwadagon dai ta bayyana cewa tun a shekarar 2008 ne ta cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar kan bukatu da dama amma har yanzu gwamnatin bata cika alkawuran da tayi musu ba.

Wannan yajin aikin ya zo ne a dai dai lokacin da Kungiyar Malaman Manyan Kwalejojin jihar guda bakwai, suke daf da shiga mako guda da fara yajin aikin.

A kwanaki biyun da suka gabata ne dai, ita gwamantin jihar Bornon ta fitar da wata sanarwar da ta nuna cewar duk wani ma'aikacin da ya kuskura ya tafi yajin aikin ba za'a biya shi albashi ba,batun da kungiyar kwadagon ke cewar ba zata sabu ba.