Majalisar koli ta Nijar ta kama wasu sojoji

Majalisar koli ta mulkin sojan Jamhuriyar Nijar CSRD ta tabbatar da kama wadansu manyan hafsoshin soja hudu.
Majalisar kolin dai ta bayyana cewa manyan jami'an sojin da aka kama din a watan jiya na shirya makarkashiyar juyin mulki ne.
Kakakin majalisar ta CSRD kanal Goukoye Abdoulkarim ya shaidawa al'umar Nijar a wata sanarwar da ya bayar ta gidan talabijin din kasar cewa mutanen sun hada baki ne domin kashe shugaban gwamnatin soji, Janar Salou Djibo.
Sannan kuma an gano cewa suna da hannu dumu dumu a handamar kudin kasa da ake bincike a kai a halin yanzu.
Ya ce wadanda ake zargin za su gurfana a gaban kuliya a kotun soji ta kasar.
Wadanda aka kama din dai sun hada da mai mukamin lamba biyu a gwamnatin sojin, Kanal Abdullaye Badie tsohon na hannun daman shugaban kasar da aka tsige daga mukaminsa, da kuma tsohon ministan ayyukan gine gine Amadou Diallo, wadanda aka ce su na adawa da shirin gwamnatin na mai da mulki ga farar hula a badi.






















