An sake dage zaben kasar Guinea

An wallafa

An sake dage zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar Lahadi a kasar Guinea, wanda ya haifar da zaman dar-dar a kasar.

Shugaban hukumar zaben Siaka Toumani Sangare, ya shaidawa manema labarai cewa ba zai yiwu a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara ba.

Sai dai bai bayyana ranar da aka tsayar domin gudanar da zaben nan gaba ba.

Sanarwar ta zo ne a lokacin da ake fama da tashin hankali a kasar, sannan majalisar dinkin duniya ta zargi jami'an tsaron kasar da laifin cin zarafin bil'adama.