Jami'an tsaro sun kama wani da ake zargi da kai hari a Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Bayanan hoto, Jami'an tsaro a Maiduguri
An wallafa

A Najeriya jami'an rundunar hadin gwiwa ta Operation Flush, sun cafke wani dan bindiga guda daga cikin wasu mutane ukku, wadanda ake zargi da kai hari a gidan daya daga cikin hakiman mai martaba Shehun Borno a Maiduguri.

Wannan hari shine karo na goma sha biyu a cikin jerin hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa jami'an tsaro, da masu unguwanni, da malamai da sauran jami'ai a jahar Borno. Mutane dayawa sun rasa rayukansu a irin wadannan hare-haren.

Jami'an tsaro suna cigaba da daukar kwararan matakan shawo kan lamarin da ake dangantakawa da 'yan kungiyar Boko Haram, ko da yake wasu na ganin cewa, a wasu lokutan 'yan fashi da makami ne ke kai hare-haren.