Korea ta Arewa ta gina sabuwar tashar nukiliya

Taswirar Korea ta Arewa
Bayanan hoto, Taswirar Korea ta Arewa
An wallafa

Wani masanin kimiyyar nukiliya dan kasar Amurka ya ce an nuna masa wata sabuwar tashar nukiliya lokacin da ya kai ziyara Korea ta Arewa a makon jiya.

Masanin, Siegfried Hecker, ya shaidawa jaridar New York Times cewa ya yi mamakin ganin tashar nukiliyar ta zamani.

Farfesa Hecker ya kuma ce abubuwan da ya gani daruruwan na'urorin da ke tace makamashin uranium ne wadanda za a iya amfani da su don sarrafa makamin nukiliya.

Jami'an Amurka sun ce lokacin da aka kori masu binciken makamai na kasa-da-kasa daga kasar ta Korea ta Arewa a watan Afrilun shekarar 2009 ba a kafa tashar nukiliyan ba.

Yadda kasar ta Korea ta Arewa ke bunkasa shirinta na nukiliya cikin hanzari zai jawo a yi zaton tana samun taimako daga ketare don yiwa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya karan tsaye.

Hakan kuma zai zamo wani sabon kalubale ga kashin bayan manufar Shugaba Obama na Amurka ta kawar da makaman nukiliya daga doron kasa.