Wikileaks ya kara tonawa Amurka asiri

Wikileaks
Bayanan hoto, Duka wadannan shugabannin dai bayanan sun shafe su
An wallafa

Bayanai dai na ci gaba da bayyana daga dubban sakonnin sirrin Amurka, wanda shafin Wikileaks mai kwarmato bayanai ya wallafa.

Bayanan na Wikileaks sun muzanta, wasu shugabannin kasashen duniya kamar Fira ministan kasar Italiya Silvio Berlusconi da cewa mara kan gado, yayin da a bangare guda kuma Amurka ta nuna damuwarta game cin hanci da rashawa a Afghanistan.

Amurka dai ta yi Allah wadai da wadannan bayanai, ita kuwa kasar Iraqi ta bayyana cewa ne, babu wani taimako da bayanan za su yi.

Asiran da shafin Wikileaks ya wallafa dai sun kunshi bayanai kan wasu shuwagabannin kasashen duniya.

Cin mutuncin abokan hulda

A ciki, jami'an Amurka sun bayyana shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa, a matsayin mai mulkin kama-karya tare da rashin jurewa suka.

Shi kuwa Fira ministan Italiya, Silvio Berlusconi sun kira shi mara nutsuwa, mai jiji da kai, kuma dan amshin shatan Fira ministan Rasha a Turai.

Jaridu a Turai
Bayanan hoto, Jaridu da dama a duniya sun wallafa wadannan bayanai

Bayanan sirrin sun kuma bayyana shugaban Afghanistan Hamid Karzai da cewa ya fiye rauni, ga kuma saurin yadda da cewa ana kulla masa makirce-makirce.

Sannan kuma wani jami'in diplomasiyyar Amurka ya ce shugaba Muammar Gaddafi na Libya ba ya iya bulaguro sai da wata ma'aikaciyar jiyya 'yar kasar Ukraine mai cikakken diri.

Yayinda aka ambato sarki Abdallah na Saudiyya yana kira ga Amurka ta kai hari kan tashar makaman nukiliyar Iran.

Tasiri

Babbar tambaya dan gane da wannnan rahoto dai shi ne, wanne tunani Amurka ke da shi kan wadannan shugabannin da take hulda da su.

Wannan dai ba wani abu bane da zai shafi dangantakar Amurka da abokan huldarta na kasashen ke tare . Kasashe dai ba su fiye katse huldar jakadanci kan irin wannan al'amari ba.

Wani abu da ya fito fili shi ne yadda sarakunan kasashen gabas ta tsakiya ke kallon kasar Iran - duk da cewa dama matsayin na su a fili yake, amma bai taba bayyana kamar haka ba.

Rahotanni sun nuna cewa a kalla mutane miliyan biyu da rabi ne suka saamu bayanan ta hanyar e-mail.

To ko wanne tasiri fitar wadannan bayanai za su yi: Christopher Mayer, tsohon jakadan Burtaniya ne a Washington, ya kuma ce babbar illar abin shi ne na kasancewar bayanan a hannun mutane tuntuni.

"Babu shakka a duk lokacin da kake ganawa da Sarkin Saudi Arabiya, a matsayinka na jakadan Amurka ko Burtaniya a kasar, za ka so duk bayanan da za ka tattauna da shi su kasance cikin sirri".

Ministan harkokin wajen Italiya, Franco Frattini, ya bayyana su da cewa sun yi daidai da hare-haren 11 ga watan Satumba ta fuskar diplomasiyya.

Wakilin BBC ya ce ya fahimci cewa Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta tattauna da fadar gwamnatin shugaba Hamid karzai, inda ta nemi a kwantar da hankali kan bayanan da za a wallafa, kuma wani jami'i ya nuna cewa sun dauki fitar bayanan a matsayin mutuwar kaka.

Wallafa bayanan dai ya jawowa Amurka abin kunya saboda ya nuna yadda ta ke muzanta kawayenta, da kuma abokan ta na kut-da-kut.