Jonathan zai nada mai bada shawara kan ta'addanci

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
An wallafa

Shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan ya ce zai nada mai bada shawara na musamman kan ayyukan ta'addanci a makon gobe.

Mai baiwa shugaban shawara ta fannin yada labarai Ima Niboro ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, bayan shugaban ya gana da jami'an tsaron kasar.

Ya kara da cewa, shugaban zai hada gwiwa da majalisar dokokin kasar da zummar ganin ta zartar da kudurin doka kan ta'addanci a kasar.

Wannan kalami na shugaban kasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan harin bam din da aka kai a wata mashaya dake Abuja a jariberen Kirsimeti, inda kimanin mutane hudu suka rasa rayukansu.

Hare-haren bama-bamai dai sun yawaita a kasar a baya-bayan nan wadanda aka fi dangantawa da masu kishin addini da kuma masu son cimma wani buri na siyasa.